'Yan Majalisa 9 Sun Rubuta Wasika ga Malaman Musulunci, An Ji Abin da Suka Nema a Ramadan

'Yan Majalisa 9 Sun Rubuta Wasika ga Malaman Musulunci, An Ji Abin da Suka Nema a Ramadan

  • Wasu 'yan Majalisar wakilan tarayya masu kishin kasa sun rubuta wasika zuwa ga malaman addinin musulunci a fadin Najeriya
  • Wasikar ta kunshi abubuwa da dama ciki har da rokon malamai su jagoranci addu'ar Al-Qunut domin neman Allah SAW ya kawo wa Najeriya sauki
  • 'Yan majalisar sun bayyana Ramadan a matsayin lokaci mai tsarki na ibada da nazari, wanda ke samar da natsuwa da damar kara kusanta ga Allah SWT

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Wasu mambobin Majalisar Wakilai da suka damu da halin da kasar nan take ciki, sun roki alfarma daga malaman Musulunci a cikin watan Ramadan.

Yan Majalisar sun bukaci malamai a fadin kasar nan da su yi addu’o’in Al-Qunut a wannan wata mai alfarma na Ramadan, domin rokon Allah ya yaye wa Najeriya abubuwan da suka dame ta.

Kara karanta wannan

Kisan masu sallar tarawihi a masallaci ya tayar da hankali, ana ta magana

Majalisar tarayya.
Zauren Majalisar wakilai ta kasa da ke birnin tarayya Abuja Hoto: HouseNGR
Source: Twitter

Daily Trust ta ce wannan kiran ya zo ne daidai lokacin da Musulmi a fadin Najeriya suke azumin watan Ramadan, wanda wata ne na ibada, addu’a, sadaka, da kuma taimako.

Wasu 'yan Majalisa sun tura sako ga malamai

‘Yan majalisar, wadanda suka fito daga jam’iyyu daban-daban, sun nemi a dukufa da addu’o’in neman daukin Ubangiji domin Najeriya ta samu abin da ya fi zama alheri ga makomarta.

Hakan na kunshe ne a cikin wasikun da aka aika wa Majalisar Koli ta Al’amuran Musulunci ta Najeriya (NSCIA), da shugabannin addini, da kuma limamai.

Sun bukaci dukkan limamai da shugabannin addini a fadin kasar nan da su jagoranci al'umma wajen yin addu’ar Al-Qunut akai-akai domin Najeriya a cikin wannan wata.

‘Yan majalisar sun bayyana Ramadan a matsayin lokaci mai tsarki na ibada da nazari, wanda ke samar da natsuwa da damar yin nazari kan makomar kasa.

Abin da 'yan majalisar suka nema daga malamai

Kara karanta wannan

Majalisar Dinkin Duniya ta ba gwamnati wa'adi a saki Nnamdi Kanu? Gaskiya ta fito

Sun jaddada cewa a matsayinsu na shugabanni, ya zama wajibi su yi ayyukan da za su tabbatar da dorewa da ci gaban Najeriya.

“Tarihi ya nuna cewa addu’a na taka rawa wajen jagorantar kasashe a lokutan rashin tabbas, da dawo da fata a lokacin yanke kauna, da kuma karfafa tarbiyyar al’umma,” in ji wasikar.

Wasikar ta kara da cewa ta hanyar addu’o’in hadin gwiwa da tuba na gaskiya, al’ummomi da dama sun samu waraka, sulhu, da sabuwar hanyar ci gaba, cewar Vanguard.

Har ila yau, ‘yan majalisar sun bukaci shugabannin addinin da su tunatar da mabiyansu muhimmancin hadin kai wajen neman daukin Ubangiji domin tabbatar da zaman lafiya, daidaito, da kuma ci gaban kasar nan.

Addu'a.
Musulmi a masallaci yana yin ibada a watan Ramadan Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Sunayen 'yan Majalisar da suka rubuta wasika

A karshe, ‘yan majalisar sun roki Allah da Ya shiryar da shugabanni, Ya warkar da kasar, sannan Ya bai wa Najeriya zaman lafiya da wadata mai dorewa.

'Yan majalisar sun fito ne daga jihohi ne irinsu Sokoto, Neja, Yobe, Osun, Oyo, Bauchi da sauransu.

Wadanda suka sanya wa wasikar hannu sun hada da: Hon. Aminu Sani Jaji, Hon. Abdussamad Dasuki, Hon Saidu Musa Abdullahi, da Hon. Adewale Morufu.

Kara karanta wannan

Zargin kashe Kiristoci: Matakai 6 da ake son Trump ya ɗauka a kan Najeriya

Sauran su ne Hon. Aliyu Aminu Garu, Hon. Abdulmaleek Abdulraheem Danga, Hon. MB Jajere, Hon. Ahmed Yusuf Doro, da kuma Hon. Adedeji Stanley Olajide.

Majalisar wakilai ta waiwayi yankin Akko a Gombe

A wani labarin, kun ji cewa Majalisar wakilai ta bukaci a yi amfani da jiragen yaki wajen fatattakar 'yan bindiga dake addabar kananan hukumomin Akko a jihar Gombe.

Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da wani kudurin gaggawa da babban mai tsawatarwa na majalisar, Hon. Usman Bello Kumo, ya gabatar.

Majalisar ta yi kira ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ba babban hafsan tsaron ƙasa umarnin fara kai farmakin gaggawa domin rusa dukkan sansanonin ƴan bindiga a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262