Dalilai 3 da Suka Jawo Tinubu Ya Umarci Sufeton Yan Sanda Ya Yi Murabus

Dalilai 3 da Suka Jawo Tinubu Ya Umarci Sufeton Yan Sanda Ya Yi Murabus

  • An kara samun bayanai a kan muhimman dalilan da suka jawo Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci tsohon IGP Kayode Egbetokun da ya yi murabus
  • Daga cikin dalilan, ana ganin Egbetokun ya nuna rashin goyon baya ga tsarin ‘yan sanda na jihohi, wanda ya saba wa manufar gwamnatin tarayya
  • Sannan sunan tsohon Sufeton yan sandan ya shiga wani mummunan kundi wanda ake zarginsa da take hakkin wasu 'yan jarida da ke Najeriya

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Wasu majiyoyi daga fadar shugaban ƙasa sun bayyana cewa an umarce Kayode Egbetokun ya sauka daga mukaminsa ne saboda manyan dalilai guda uku.

Na farko, Egbetokun ba ya goyon bayan tsarin ‘yan sanda na jihohi wanda Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ke muradin a tabbatar.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya tura jakadu lungu da sako, za su isar da sako ga 'yan Najeriya

Rahoto ya ce Tinubu ne ya umarci Egbetokun ya sauka
Kayode Egbetokun, tsohon Sufeton yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

A labarin da ya kebanta ga jaridar Premium Times, gwamnati ta yi imanin cewa kirkirar ‘yan sanda na jihohi zai inganta tsaro a ƙasa.

Dalilan umartar Sufetan 'yan sanda ya bar kujerarsa

Rahoton ya ce tsohon IGP ya bayyana cewa Najeriya ba ta kai matakin da za a samar da yan sandan jihohi ba tare da an siyasantar da su ba.

Wannan ra’ayi ya saba wa manufar shugaban ƙasa wanda ya dage wajen ganin an kafa ‘yan sanda na jihohi a matsayin wani mataki na inganta aikin ‘yan sanda da tsaro.

An yi zargin ra'ayin Egbetokun ya ci karo da na Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: UGC

Dalili na biyu da ake ganin shi ya sa aka tilasa wa Egbetokun ya yi ritaya shi ne bai cika bin umarnin shugaban ƙasa na janye ‘yan sanda daga gadin manyan mutane ba.

An bayar da wannan umarni a taron tsaro a watan Nuwamba 2025, amma matakin da aka ɗauka don cika wannan umarnin bai kai yadda aka so ba.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Gwamnatin Tinubu ta fadi dalilin murabus din Sufetan 'yan sanda

Ana zargin Egbetokun da cin zarafi

Na uku kuma, akwai damuwa game da halayen Egbetokun na tauye ‘yancin ‘yan jarida a lokacin da yake IGP.

Hukumar IPI Nigeria ta saka sunansa a cikin “Book of Infamy” bayan samun rahotanni na harin ‘yan jarida har guda 24 a karkashin kulawarsa.

Duk da sauye-sauyen doka, an ci gaba da amfani da dokar laifuffukan yanar gizo wajen takurawa da kuma tsoratar da ‘yan jarida da masu magana.

Rashin daukar matakin gyara a wannan lamari shi ne babban dalilin da ya sa IPI ta yi wannan hukunci.

Bayan ficewar Egbetokun, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya nada Olatunji Disu a matsayin IGP na rikon kwarya, domin ci gaba da aiwatar da manufofin gwamnati a fannin tsaro.

Fadar Shugaban kasa ta magantu kan Egbetokun

A baya mun wallafa cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da murabus ɗin Kayode Egbetokun daga matsayin Sufeto Janar na ‘yan sandan Najeriya.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya ya yi murabus, an ji dalili

Rahotanni sun bayyana cewa Kayode Egbetokun ya ajiye aiki ne bisa dalilan kula da iyali, sai dai wasu majiyoyi sun ce an nemi ya sauka bayan ganawa da Bola Tinubu.

Murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake sukar matsalar tsaro da ta ƙaru a sassa daban-daban na ƙasa duk da haka Tinubu ya amince da murabus dinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng