EFCC Ta Saki Hotunan Wasu Manyan Ma'aikatan Gwamnati da Ake Zargi da Zambar N2bn
- Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu manyan daraktoci uku na hukumar sufurin jiragen kasa (NRC) kan zargin zambar N2.04bn
- A shari'a daban daban, EFCC ta zargi manyan jami'an da karbar kudaden haram daga 'yan kwangila, wanda ya saba dokar kasa
- Dukkan wadanda ake zargi sun musanta aikata laifuffukan, yayin da kotu ta bada umarnin tsare daya daga ciki, aka bada belin sauran
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Hukumar EFCC ta gurfanar da wasu manyan jami’an hukumar sufurin jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC) guda uku a gaban babbar kotun jihar Legas da ke Ikeja.
Ana tuhumar jami'an ne da zargin zamba, rashawa, da kuma halatta kuɗaɗen haram waɗanda jimillar su ta haura naira N2.04bn.

Source: Facebook
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar 25 ga Fabrairu, 2026.
Tuhume tuhumen da ake yi wa jami'an NRC
Waɗanda ake tuhumar sun haɗa da Felix Njoku, tsohon daraktan kuɗi; Benjamin Chinwuba Iloanusi, daraktan sayayya; da kuma Oche Jerry Ogbole-Inalegwu, darakta a bangaren makanikanci.
1. Njoku: Zargin zambar N736m
An gurfanar da Felix Njoku a gaban Mai shari'a Olubunmi Abike-Fadipe kan tuhume-tuhume 17, kamar yadda sanarwar hukumar ta nuna.
Hukumar EFCC ta yi zargin cewa Njoku ya karɓi Naira miliyan 240 daga hannun ƴan kwangilar NRC ta asusun bankin kamfaninsa bayan ya bar ofis, kuɗaɗen da ke da alaƙa da kwangilolin da aka bayar lokacin yana kan mulki.
Lauyan EFCC, Abba Muhammad (SAN) ya gabatar da bukata ga kotu, cewa:
"Muna neman kotu ta sanya ranar shari'a sannan ta tsare wanda ake tuhuma a gidan gyaran hali har zuwa lokacin kammala shari'ar."
Sai dai, alkaliyar ta ba da shi belin wucin gadi saboda dalilai na rashin lafiya, amma ta umarce shi da ya ajiye fasfo ɗinsa na fita ƙasashen waje a kotu.
2. Iloanusi: Zambar N915m
Shi kuwa Benjamin Iloanusi, an gurfanar da shi ne kan tuhume-tuhume 10 na zambar kudi da suka kai naira miliyan 915.
Ana zarginsa da karɓar naira miliyan 160 daga ƴan kwangila tsakanin watan Janairu zuwa Disambar shekarar 2022.
Mai shari'a Ismail Ijelu ya ba da umarnin a tsare shi a gidan yari har sai ranar 3 ga watan Maris domin sauraron buƙatar belinsa.
3. Ogbole-Inalegwu: Zambar N395m
Shi kuma Oche Jerry Ogbole-Inalegwu, ana tuhumarsa ne da zambar Naira miliyan 395, a cewar sanarwar hukumar EFCC.

Source: UGC
EFCC ta ce ya karɓi kuɗaɗe daga kamfanin CCECC ta asusun kamfaninsa na Altech Engineering lokacin yana manajan gunduma.
Mai shari'a Mojisola Dada ta ba Oche Jerry Ogbole-Inalegwu damar ci gaba da amfani da belin da EFCC ta ba shi tun farko, an dage shari'arsa zuwa 23 ga Afrilu, 2026.
Dukkan jami'an guda uku sun musanta aikata laifuffukan da ake tuhumar su da su a gaban alkalai daban-daban.
Hukumar EFCC ta bayyana cewa waɗannan laifuffuka sun saɓa wa sassan dokokin manyan laifuffuka na Jihar Legas na shekarar 2011.
Duba hotunan wadanda ake zargi a nan kasa:
NRC ta dakatar da zirga-zirgar jirage
A wani labari, mun ruwaito cewa, hankulan jama'a sun yi matukar tashi yayin da jirgin kasa da ke zirga zirga a hanyar Abuja zuwa Kaduna ya yi hatsari a 2025.
Hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta dauki matakin dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa a hanyar Abuja-Kaduna har zuwa wani lokaci.
NRC a lokacin ta ya bayyana cewa ma’aikatanta tare da hukumar NSIB da wasu hukumomi suna gudanar da bincike a wurin hatsarin domin gano matsalar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


