Tinubu Ya Bukaci Majalisa Ta Gaggauta Sauya Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

Tinubu Ya Bukaci Majalisa Ta Gaggauta Sauya Kundin Tsarin Mulkin Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi buda baki tare da Sanatoci a fadar shugaban kasa a daren Laraba, 25 ga Fabrairun 2026
  • A yayin zaman da suka yi, rahoto ya nuna cewa Bola Tinubu ya bukaci majalisar dattawa da ta sauya kundin tsarin mulkin Najeriya
  • Shugaban kasar ya yi maganar ne a shirin bayar da kofar kafa 'yan sandan jihohi domin yaki da rashin tsaro da ya yi katutu a kasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya bukaci majalisar kasa da ta fara shirin gyara kundin tsarin mulki domin samar da ’yan sandan jihohi a matsayin wani mataki na magance matsalolin tsaro a ƙasar.

Tinubu ya ce gyaran kundin tsarin mulki ya zama dole domin a kare dazuzzuka daga hannun masu laifi tare da amintar da 'yan kasa daga tsoro.

Kara karanta wannan

2027: Tinubu ya tura jakadu lungu da sako, za su isar da sako ga 'yan Najeriya

Sanata Godswill Akpabio tare da Bola Tinubu
Sanata Godswill Akpabio a hagu, Shugaba Bola Tinubu a dama. Hoto: Bayo Onanuga|Nigerian Senate
Source: Twitter

Tinubu: Batun sauya tsarin mulki

Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa shugaban ya yi kira a sauya kundin tsarin mulki ne yayin buda-baki da ya yi da sanatoci a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

“Abin da na ke roƙo a yau shi ne ku fara tunanin yadda za a gyara kundin tsarin mulki domin kafa ’yan sandan jihohi, don mu kare ƙasarmu, mu karɓi dazuzzukanmu daga masu barna, mu kuma amintar da yaranmu daga tsoro,”

- Inji shugaba Tinubu

Ya yabawa sanatocin kan goyon bayan da suke ba shi wajen tinkarar matsalolin tsaro, yana mai alƙawarin cewa ba zai ɗauki haɗin gwiwarsu da wasa ba.

Punch ta rahoto ya ce:

“Ba ku taɓa kasa a gwiwa game da irin waɗannan kiraye-kiraye ba. Ina tabbatar muku zan ci gaba da amfani da goyon bayan da kuke ba ni, kuma zan girmama hakan,”
Bola Tinubu da Sanatocin Najeriya
Shugaba Bola Tinubu yayin buda baki da sanatoci a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Alkawarin Tinubu ga gwamnonin jihohi

Kara karanta wannan

Babu wasa: Tinubu ya tara gwamnoni, ya gaya masu shirinsa don magance rashin tsaro

Kiran Tinubu ga majalisa ya zo ne kwana uku bayan ya yi irin wannan alƙawari ga gwamnonin jihohi yayin buda-baki, inda ya sha alwashin cewa ba za a jinkirta kafa ’yan sandan jihohi ba.

A lokacin, Tinubu ya ce:

“Ba za mu jinkirta abin da na yi muku alƙawari ba. Za mu kafa ’yan sandan jihohi domin yaƙi da matsalar tsaro.”

Bukatar kafa ’yan sandan jihohi na samun ƙarfi a faɗin ƙasar, inda gwamnonin jihohi, sarakunan gargajiya da masana harkokin tsaro ke ganin hakan a matsayin mafita ga matsalar tsaro.

A halin yanzu, aikin ’yan sanda a Najeriya yana ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya ne kaɗai, yayin da jihohi ke dogaro da rundunar ’yan sanda wajen gudanar da ayyukan tsaron cikin gida.

Sai dai wasu masu sharhi na sukar wannan tsarin da cewa bai isa ya magance barazanar tsaro daban-daban da ke wanzuwa a jihohi 36 ba.

Jakadun Tinubu za su fara aiki

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin jam'iyyar APC sun yi taro na musamman da shugabannin kungiyar jakadun Bola Tinubu a Abuja.

APC ta ce dole sai an fita a nemi jama'a kafin a ci zabe, saboda haka aka ce dole jakadun shugaban kasar su shiga gari wayar da kan jama'a.

An yi kira ga jakadun Tinubu su shirya zuwa kasuwanni da sauran wuraren da jama'a ke taruwa domin wayar da kan 'yan kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng