MURIC: Kungiyar Musulunci Ta Kausasa Harshe ga ICPC kan Ci Gaba da Tsare El Rufai

MURIC: Kungiyar Musulunci Ta Kausasa Harshe ga ICPC kan Ci Gaba da Tsare El Rufai

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai na ci gaba da zama a tsare a hannun hukumar ICPC
  • Kungiyar MURIC ta fito ta soki matakin da hukumar ta dauka na ci gaba da tsare tsohon gwamnan a hannunta
  • MURIC ta kuma yi kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya kan mutunta dokokin da kundin tsarin mulki ya tanada

​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Ƙungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC) ta yi magana kan ci gaba da tsare Nasir El-Rufai da hukumar ICPC ke yi.

Kungiyar MURIC ta yi Allah-wadai da ci gaba da tsare tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai da hukumar ICPC ke yi.

Kungiyar MURIC ta bukaci a saki Nasir El-Rufai
Shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola da Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ce shugaban kungiyar MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai a ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Zance ya fito: ICPC ta yi magana kan batun El Rufai ya shiga mummunan hali a hannunta

ICPC na ci gaba da tsare El-Rufai

El-Rufai dai ya kasance a tsare tun bayan da ya amsa gayyatar hukumar EFCC a ranar 16 ga watan Fabrairu, 2026.

Kwanaki biyu da suka gabata, Muyiwa Adekeye, mai taimakawa El-Rufai kan kafafen yaɗa labarai, ya zargi hukumar ICPC da kin ba da belin tsohon gwamnan na Kaduna.

A cewar Adekeye, tsohon gwamnan ya fuskanci matsalar zubar jini ta hanci a inda ake tsare da shi, kuma an hana matarsa ganinsa kai-tsaye lokacin da ta kai masa abinci.

Me MURIC ta ce kan tsare El-Rufai

Sai dai yayin da yake jawabi a wajen taron, Farfesa Ishaq Akintola, ya buƙaci a saki El-Rufai cikin gaggawa ko kuma a gurfanar da shi a gaban kotu.

“Mallam Nasir El-Rufai yana tsare tun bayan da ya kai kansa ofishin EFCC da ke Abuja ranar Litinin, 16 ga Fabrairu, 2026. Ko da yake EFCC ta sake shi ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, hukumar ICPC ta sake kama shi a ranar.”

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sanya har yanzu hukumar EFCC ba ta gurfanar da Nasir El Rufai ba

"Rahotannin da ke fitowa daga kafafen yaɗa labarai sun nuna cewa rashin zuwansa kotu a yau Laraba, 25 ga Fabrairu, 2026, shi ne dalilin rashin gurfanar da shi."
”Akwai alamu na kokarin ganin an ci gaba da tsare El-Rufai. Mutumin da yake tsare ba za a iya ɗora masa laifin ‘rashin halartar kotu’ ba, domin ba shi da ikon sarrafa zirga-zirgarsa.‎"
“MURIC tana buƙatar a gurfanar da Mallam Nasir El-Rufai cikin gaggawa a gaban kotu mai iko. Doka ta tanadi sa’o’i 48 ne kawai a matsayin iyakar lokacin da za a iya tsare wanda ake zargi, wanda kuma a cikin wannan lokacin dole ne a gabatar da shi a gaban kotu."

- Farfesa Ishaq Akintola

MURIC ta bukaci a saki Nasir El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

MURIC ta aika sako ga gwamnatin tarayya

Farfesa Ishaq Akintola ya bukaci gwamnatin tarayya da ta mutunta dokoki wanda suka hada har da 'yancin fadar albarkacin baki, rahoton Daily Post ya tabbatar da hakan.

‎”Muna kuma kira ga gwamnatin tarayya da ta bi dokokin dimokuraɗiyya waɗanda suka haɗa da mutunta tsarin doka, ’yancin zirga-zirga, da ’yancin faɗar albarkacin baki, waɗanda duka suke cikin kundin tsarin mulkin Najeriya (sashe na 41 da na 39)."

Kara karanta wannan

Bayan ICPC, El Rufai ya maka hukumar DSS a kotu, ya gabatar da manyan bukatu 3

”Najeriya ba za ta iya jure nuna wa duniya munanan abubuwan siyasa a daidai lokacin da idon duniya yake kanta ba. Tsohon gwamnan Sokoto, Waziri Tambuwal, tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN, sannan yanzu El-Rufai, duka mambobin jam’iyyun adawa ne."

"Muna fatan sakonmu yana isa. Lokaci ya yi da za a gurfanar da El-Rufai ko a sake shi.”

ICPC ta magantu kan rashin lafiyar El-Rufai

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar ICPC ta yi magana kan batun tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya kamu da rashin lafiya yayin da yake tsare a hannunta.

Hukumar ICPC ta musanta zargin cewa tsohon gwamnan ya fuskanci matsalar zubar da jini ta hancinsa.

Mai magana da yawun hukumar ICPC ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin ikirarin cewa El-Rufai ya samu matsala ta rashin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng