Tashin Hankali: 'Yan Boko Haram Sun Farmaki Karamar Hukumar Gwamna ana cikin Azumi

Tashin Hankali: 'Yan Boko Haram Sun Farmaki Karamar Hukumar Gwamna ana cikin Azumi

  • 'Yan ta'addan Boko Haram sun farmaki wasu kauyuka na jihar Adamawa inda suka hallaka mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
  • Tsagerun 'yan ta'addan sun mamaye kauyukan suna harbi kan mai uwa da wabi tare da kona gidajen mutane da dama
  • Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya yi Allah wadai da harin tare da jajantawa mutanen da lamarin ya shafa

​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Adamawa - 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin ta'addanci a jihar Adamawa, inda suka kashe mutame.

Aƙalla mutane bakwai ne aka tabbatar da mutuwarsu a wani sabon hari mayakan Boko Haram suka kai a karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa.

'Yan Boko Haram sun kashe mutane a Adamawa
Taswirar jihar Adamawa, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa 'yan ta'addan na Boko Haram sun kai harin ne a daren ranar Talata, 24 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki wurin ibada a watan azumi, sun bude wa mutane wuta

'Yan Boko Haram sun mamaye kauyuka

A cewar wata majiya, maharan sun mamaye kauyukan Sheweri da Kirchinga, inda suka ƙone gidaje da dama, yayin da mazauna garuruwan da dama suka tsere cikin daji domin tsira.

Majiyar ta kara da cewa adadin waɗanda suka rasu na iya ƙaruwa, amma ba ta iya bayar da takamaiman adadi ba a daidai lokacin da ake rubuta wannan rahoto.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Adamawa, Morris Dankwambo, ya riga ya isa yankin domin tantance irin ɓarnar da harin ya haifar.

An kashe mutane da dama

Wasu alkaluma da ba a tantance ba daga mazauna yankin sun nuna cewa mutane kusan 13 ne aka kashe sakamakon harin.

Jaridar Tribune ta ce maharan sun far wa kauyukan ne suna harbi kan mai uwa da wabi, lamarin da ya tilasta wa mazauna garin tserewa zuwa daji da kuma ƙauyukan da ke maƙwabtaka don tsira da rayukansu.

Kauyukan Sheweri da Kirchinga suna cikin ƙaramar hukumar Madagali ne, wani yanki da ya sha fuskantar hare-haren mayakan Boko Haram sakamakon kusancinsa da dajin Sambisa da kuma iyakar Najeriya da ƙasar Kamaru.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun farmaki babban Janar da tawagarsa, an yi gumurzu da sojoji

Gwamna Fintiri ya jajanta kan harin Boko Haram

Da yake martani kan hare-haren a shafinsa na X, Gwamna Fintiri ya jajanta wa iyalai da al’ummomin da abin ya shafa.

'Yan Boko Haram sun kai hari a Adamawa
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri na jihar Adamawa Hoto: @GovernorAUF
Source: Twitter
“Ina alhini ga mutanen jihar Adamawa kan hare-haren matsorata da aka kai a Madagali da Hong. Ina mika ta’aziyyata ga iyalan da suka rasa masoyansu da kuma kowace al’umma da wannan bala’i ya shafa."
“Ba za mu miƙa wani ɓangare na jihar mu ga tsoro ba. Tare da haɗin gwiwar hukumomin tsaro, za mu bi sahun waɗanda suka aikata wannan danyen aiki kuma mu tabbatar an yi adalci."
“Adamawa ta taɓa fuskantar munanan lokuta a baya kuma za mu sake yin nasara. Ku kasance masu juriya Muna tare da ku.”

- Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri

'Yan ta'adda sun kashe mutane

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa sun kai harin ta'addanci a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Boko Haram sun nuna tsaurin ido ga sojoji, an rasa rayuka bayan kazamin artabu

Tsagerun 'yan ta'addan Lakurawa sun kashe mutane da dama tare da lalata kauyuka bakwai a wasu hare-haren da suka kai.

Kakakin rundunar 'yan sandan Kebbi, Bashir Usman ya ce mambobin kungiyar Lakurawa sun kai harin ne a kauyukan gundumar Bui.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng