Yadda Peter Obi da Jiga Jigan ADC Suka Tsallake Rijiya da Baya a Harin 'Yan Bindiga a Edo
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya fuskanci harin 'yan bindiga a birnin Benin na jihar Edo
- Harin dai an kai shi a wurin taron jam'iyyar ADC inda aka raunata mutane tare da lalata wasu motoci sakamakon hargitsin da aka samu
- Wani jigo a jam'iyyar ADC, John Odigie-Oyegun, ya bayyana yadda suka tsira daga harin na 'yan bindiga a birnin Benin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Edo - Tashin hankali ya mamaye birnin Benin na Jihar Edo a jiya, yayin da 'yan bindiga suka farmaki ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi.
Peter Obi, tsohon gwamnan jihar Edo, John Odigie-Oyegun, da sauran shugabannin jam’iyyar ADC sun tsallake rijiya da baya daga harin na wasu ’yan bindiga.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta kawo rahoton cewa John Odigie Oyegun ya yi magana kan harin na 'yan bindiga a ranar Talata, 24 ga watan Fabrairun 2027.
Yayin da yake tattaunawa da manema labarai, Odigie-Oyegun ya yi gargaɗin cewa wannan lamari na iya haifar da hargitsi idan ba a shawo kansa ba.
“Ina tsoron cewa shugabanninmu, na tarayya da na wannan jiha, suna wasa da wuta. Sakamakon hakan na iya zama mai ban tsoro, fiye da yadda kowa ke tsammani."
- John Odigie-Oyegun
Yadda Obi da 'yan ADC suka tsira
A cewarsa, taron da suka yi a sakatariyar an tsara shi ne bisa ƙa'ida, amma sai suka samu gargaɗi na tsaro, jaridar The Sun ta kawo labarin.
"Muna tsaka da gudanar da taron, sai muka samu rahoton sirri daga ɗaya daga cikin hukumomin tsaro cewa suna da labarin za a kawo hari wurin, don haka mu yi ƙoƙarin kammalawa."
“Ba za ka iya yin watsi da bayani ba. Don haka muka gajarta taronmu, kuma ina jin mun yi sa’a sosai da muka bar wurin a kan lokaci, domin bayan tafiyarmu komai ya lalace. Mutane sun iso a cikin motoci kusan 10 suna ta harbe-harbe a ko’ina... An raunata mutane.”
- John Odigie- Oyegun

Kara karanta wannan
An fara nuna yatsa ga Tinubu da 'yan bindiga suka farmaki Peter Obi, tsohon shugaban APC
An nuna yatsa ga gwamnatin Edo
Game da harin da aka kai gidansa, ya ƙara da cewa:
“Muna da baƙo, tsohon gwamnan Anambra kuma ɗaya daga cikin manyan shugabannin ADC. Kamar yadda alamu suka nuna, mai neman takara ne."
“Gwamnatin nan ta yi barazanar cewa idan ya zo jihar Edo ba tare da izini ba, ba za a tabbatar da tsaron sa ba. Yana kawo mini ziyarar ban-girma ne sai harsashi ya fara kwarara a ko’ina. Yaushe muka koma irin wannan matsayin?”

Source: Twitter
ADC ta nuna yatsa ga APC
Shugaban jam’iyyar ADC na jihar Edo, Kennedy Odion, ya zargi jam’iyyar APC da hannu wajen shirya harin.
“Mun ji labarin cewa APC na tafe don kawo mana hari. Cikin sauri muka gajarta taron muka kawo ƙarshensa."
"’Yan mintoci kaɗan bayan mun gama, muka ji cewa ’yan daba sun mamaye wurin. Sun raunata mutane uku... Bayan sun tarwatsa wurin, sai suka zo gidan Oyegun inda muke wani taron. Dukkan motocin da aka yi fakin a waje an lalata su.”

Kara karanta wannan
Tashin hankali: 'Yan bindiga sun farmaki Peter Obi, an yi yunkurin kashe shi a Benin
“Ni karan kaina Peter Obi, da Sanata Owie, da kuma Oyegun mun riga mun bar wurin taron lokacin da muka ji labarin harin ’yan daban. Sun raunata mutane uku.”
- Kennedy Odion
Peter Obi ya je ziyarar jaje a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Petee Obi, ya kai ziyarar jaje sakamakon gobarar da ta auku a Kano.
Peter Obi, ya bayyana alhininsa ga ’yan kasuwar Singer da ke Kano sakamakon gobarar da ta tashi wadda ta jawo asarar dukiya mai yawa.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya jaddada cewa gobarar ba ta tsaya ga lalata gine-gine da kayayyaki kaɗai ba, ya ce ta shafi tattalin arziki da rayuwar jama’a da dama.
Asali: Legit.ng
