An Rikita Malaman Musulunci da Miliyoyi a Kaduna, Sun Nuna Goyon Bayansu ga APC

An Rikita Malaman Musulunci da Miliyoyi a Kaduna, Sun Nuna Goyon Bayansu ga APC

  • Kwamishinan harkokin kananan hukumomi na Kaduna ya nemi alfarmar malaman Musulunci yayin raba masu kayan abinci da kudi
  • Hon. Sadiq Mamman Lagos ya ce tallafin cika alkawarin da aka yi ne lokacin yakin neman zaben Uba Sani a Kaduna tun a shekarar 2023
  • Malaman sun yi godiya na musamman kan abin alheri da aka yi masu, sun kuma sha alwashin ci gaba da mara wa APC baya a zaben 2027

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarauta na Kaduna, Hon. Sadiq Mamman Lagos, ya gana da wasu malaman Musulunci a Kaduna.

Kwamishinan ya ba malaman addinin Musulunci da malamai mata na Islamiyya tallafin kudi har ₦10m tare da buhunan shinkafa.

Kwamishina ya raba miliyoyi ga malamai a Kaduna
Taron raba wa wasu malaman Musulunci kudi da shinkafa daga gwamnatin Uba Sani a Kaduna. Hoto: Hon. Sadiq Mamman Lagos, Uba Sani.
Source: Facebook

An raba kudi, abinci ga malamai a Kaduna

Sadiq Mamman shi ya tabbatar da haka bayan wallafa wani faifan bidiyo a shafinsa na X wanda Legit Hausa ta gano yayin gudanar da taron.

Kara karanta wannan

Yadda Kashim Shettima ya je Kwara, ya ki ziyartar kauyukan da aka kashe mutane 200

An bayyana wannan tallafi ne a wani taron tuntubar jama'a da aka yi da malaman Islamiyya mata, mambobin Ihya’ussunnah da sauran malamai da suka taka rawa wajen tara kuri’u kafin zaben 2023.

Taron ya kuma tuna da wani zama da aka yi a Janairu 2023 a gidan kwamishinan da ke Marafa, inda malaman suka gana da Gwamna Uba Sani, wanda a wancan lokaci dan takarar sanata ne, suka kuma yi masa alkawarin goyon baya.

Da yake jawabi, Hon. Mamman Lagos ya yabawa malaman bisa cika alkawari, yana mai cewa kokarinsu ya taimaka matuka wajen samun nasarar zabe.

Ya ce wannan tallafi cika alkawarin da aka dauka ne a lokacin yakin neman zabe da ya gudana a baya.

Ya kara da cewa an bayar da ₦10m da kayan abinci ne a madadin Gwamna Uba Sani domin nuna godiya bisa jajircewarsu da biyayya ga gwamnati.

Kwamishina a Kaduna ya nemi goyon bayan malaman Musulunci
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna a Najeriya. Hoto: Uba Sani.
Source: Facebook

Rokon kwamishina ga malaman Musulunci a Kaduna

A cewarsa, wannan mataki ya dace da manufar gwamnati mai kula da jama’a da salon shugabanci na hadin kai, wanda ke gane muhimmancin shugabannin al’umma wajen karfafa dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Zaben cike gurbi: Abin da Gwamna Abba Kabir ya fada wa ƴan jam'iyyar APC

Kwamishinan ya roki malaman su ci gaba da yi wa Kaduna addu’ar zaman lafiya, kwanciyar hankali da ci gaba, yana mai jaddada kudirin gwamnati na kawo ribar dimokuradiyya ga kowane bangare.

A nasa bangaren, shugaban Ulama, Malam Muhammadu, ya nuna godiya ga kwamishinan da gwamnan, yana mai cewa wannan wata babbar alama ce ta karramawa.

Ya tabbatar da cewa malaman za su ci gaba da mara wa gwamnati baya tare da inganta hadin kai da shugabanci nagari a al’ummominsu.

Haka zalika, malaman sun sake jaddada biyayya ga jam’iyyar APC, tare da alkawarin tattara kuri’u domin zaben 2027 mai zuwa.

Ramadan: Fasto ya raba abinci ga malaman Musulunci

Tun a farko an ji cewa wani cocin Kirista ya yi abin alheri ga al'ummar Musulmi yayin da fara azumin watan Ramadan a jihar Kaduna.

Cocin ya rabawa Musulmai sama da 1,000 kayan abinci gabanin Ramadan 2026 domin tallafa wa marasa galihu.

Fasto Yohanna Buru ya ce shirin na daga cikin kokarin inganta zaman lafiya da hadin kai tsakanin addinai a Arewacin Najeriya da ke fama da matsaloli.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.