Gwamna Ya Tura wa Dan Tsohon Shugaban Ƴan Sanda N100m, an Fadi Yadda Aka Yi
- Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta yi karin haske game da tura miliyoyin kudi asusun bankin dan tsohon shugabanta
- Rahotanni sun ce an tura N100m zuwa asusun Victor Egbetokun, wanda ɗa ne ga tsohon Sufeto-janar, Kayode Egbetokun
- Bayani ya biyo bayan rahoton da ya zargi cewa an tura kuɗin daga asusun tsaron Anambra zuwa na Victor, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa an tura N100m zuwa asusun Victor Egbetokun, ɗan Kayode Egbetokun, tsohon Sufeto Janar na ‘yan sanda.
An taso rundunar gaba kan lamarin inda ta tabbatar da cewa an tura kudin ne bisa kuskure a wancan lokaci.

Source: Facebook
Da yake magana a shirin Politics Today na Channels TV, kakakin rundunar, Benjamin Hundeyin, ya ce Victor ya sanar da rundunar abin da ya faru.
Yadda aka tura wa dan Egbetokun N100m
Bayani ya biyo bayan wani rahoto da ya bazu a intanet, wanda ya yi zargin cewa Victor ya karɓi N100m daga asusun kuɗin tsaron gwamnatin Anambra.
Ya ce bayan ganin kuɗin a asusunsa, Victor ya umarci jami’in kula da asusunsa da ya mayar da kuɗin nan take.
Lamarin ya jawo maganganu da zargin cin hanci yayin da ake kalubalantar dalilin da ya sa gwamnatin Anambra za ta tura masa kudin.

Source: Twitter
Martanin rundunar yan sanda kan lamarin
Benjamin Hundeyin ya ce an fitar da takardar bayanin asusun, wadda ta nuna cewa an mayar da N100m zuwa asusun gwamnatin Anambra.
Ya kuma ce saboda ce-ce-ku-cen da suka biyo baya, matashin ya rufe asusun tare da rubuta koke ga EFCC domin a gudanar da bincike.
Ya ce:
“Za ku iya tunawa lokacin da shi (Omoyele Sowore) ya ce an tura Naira miliyan 100 zuwa asusun dan IGP. Nan take na kira dan IGP domin jin abin da ke faruwa, sai ya yi mani bayani.

Kara karanta wannan
Babbar magana: Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya ya yi murabus, an ji dalili
“Ya ce ya ga Naira miliyan 100 a cikin asusunsa, sai ya umarci jami’in kula da asusunsa da ya mayar da kudin nan take, kuma haka aka yi.
“Ya buga takardar bayanin asusunsa ya nuna mani. An tilasta wa matashin rufe wannan asusun. Har ma ya rubuta koke zuwa EFCC domin a binciki zargin.”
Kakakin rundunar ya bayyana lamarin a matsayin kuskure, yana mai cewa an gano matsalar da wuri kuma aka gyara ta.
Ya jaddada cewa kuɗin ba su zauna a asusun ba, domin an mayar da su cikin gaggawa bayan an gano abin da ya faru.
An gano dalilin murabus din shugaban yan sanda
Mun ba ku labarin cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta tabbatar da murabus ɗin Kayode Egbetokun daga matsayin Sufeto Janar na ‘Yan Sanda.
An ce ya ajiye aiki ne bisa dalilan kula da iyali, sai dai wasu majiyoyi sun ce an nemi ya sauka bayan ganawa da Bola Tinubu.
Murabus ɗin ya zo ne a daidai lokacin da ake sukar matsalar tsaro da ta ƙaru a sassa daban-daban na ƙasa baki daya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
