Amnesty Ta Hurawa Abba Kabir Wuta a Kano, Ta Zarge Shi da Cin Zarafin 'Yan Adawa

Amnesty Ta Hurawa Abba Kabir Wuta a Kano, Ta Zarge Shi da Cin Zarafin 'Yan Adawa

  • Kungiyar Amnesty International ta zargi Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da kuntatawa 'yan jam'iyyun adawa a kwanan nan
  • Amnesty ta lissafa wasu masu adawa da Gwamnatin Kano da ta ce an kama, wasu kuma an gurfanar da su a gaban kotu a jihar
  • Bugu da kari, kungiyar ta bukaci shugabanni su tabbatar sun ba al'umma damar fadin albarkacin bakinsu kamar yadda doka ta tanada

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Ƙungiyar Amnesty International ta yi zargin cewa ana ƙara kamawa tare da tsare mutane saboda sukar gwamnati ko bayyana ra’ayin da ya sabawa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kungiyar Amnesty ta yi korafi ne kasa da wata daya da gwamna Abba Kabir Yusuf ya sauya sheka daga jam'iyyar NNPP zuwa APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sanya har yanzu hukumar EFCC ba ta gurfanar da Nasir El Rufai ba

Abba Kabir Yusuf a wajen taro
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yana jawabi. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Legit Hausa ta rahoto cewa Amnesty ta yi kira na musamman ga Abba Kabir Yusuf a wani sakon da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Maganar kama 'yan adawa a jihar Kano

Amnesty ta ce a kusan dukkan lokuta, ana kamawa ko gayyatar masu sukar gwamnatin Kano, musamman ta hannun hukumar tsaron farin kaya (DSS).

Kungiyar ta ce matakin na ƙara haifar da yanayin tsoro mai muni tare da jefa ’yancin faɗin albarkacin baki cikin haɗari a jihar Kano.

Ta ce sababbin shari’o’in da suka tattara sun nuna karara yadda ake cin zarafi da kuma amfani da hukumomin tsaro ta hanyar da ke tauye hakkin jama’a a Kano.

Wasu da aka ce an kama a Kano

Ta ce saboda sukar Gwamnan jihar Kano, jami’an DSS masu ɗauke da makamai sun yi awon gaba da Abba Ibrahim a gidansa da ke Kano.

Amnesty ta bayyana cewa har yanzu yana tsare, kuma yana cikin haɗarin rasa jarabawar da ake yi a Jami’ar Northwest inda yake karanta Shari’a.

Kara karanta wannan

Ana shirin buda baki, 'yan bindiga sun tare bayin Allah, sun yi masu kisan gilla

Ta ce an kama fitaccen mai tasiri a kafafen sada zumunta kuma mai sukar gwamnan, Aminu Warkal. Amnesty ta ce DSS ta tsare shi na tsawon sa’o’i biyar a ƙarshen mako bisa zargin cin zarafin gwamna ta yanar gizo.

Kugiyar ta ce Samir Hanga ya fuskanci gayyata daga DSS saboda sukar gwamnan. Sai dai an sake shi bayan tambayoyi da ta ce manufarsu ita ce a rufe masa baki.

Ta kara da cewa an kama Abdulmajid Danbilki Kwamanda mako biyu da suka gabata, tare da tilasta masa janye sukar da yake yi wa gwamna Abba Kabir Yusuf.

Dan Bilki Kwamanda da Abba Kabir Yusuf
Abba Kabir Yusuf a hagu, Dan Bilki Kwamanda a dama. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa|Imran Muhammad
Source: Facebook

Bugu da kari, ta ce an kama Saifullahi Abubakar ba bisa ka’ida ba tare da tsare shi saboda yin wani bidiyon barkwanci a TikTok kan gwamna Abba Kabir Yusuf.

Kungiyar ta ce:

"Haƙƙinsu ne su soki shugaban ƙasa ko gwamna. Babu wanda ya fi ƙarfin a soke shi komai matsayinsa."

An yi magana kan tsare Walida

A wani labarin, kun ji cewa masana da kungiyoyi sun kara kira ga hukumomi su dauki mataki game da wata 'yar jihar Jigawa da aka ce an mayar Kirista.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Malamin jami'ar ABU, Dr Kabiru Danladi Lawanti ya yi kira ga gwamnan Jigawa ya sa baki hukumar DSS ta saki Walida Abdulhadi.

Kungiyoyin addinin Musulunci da suka hada da MURIC sun buƙaci sake bincike, suna ƙalubalantar rahoton da DSS ta fitar game da lamarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng