Gobara: Matakan da Gwamnatin Kano Za Ta Bi Wajen Raba N8bn ga Ƴan Kasuwar Singer
- Gwamnatin Kano ta kafa kwamitin mutane 23 domin raba tallafin naira biliyan takwas ga yan kasuwar Singer da gobara ta shafa
- Kwamitin zai tantance ainihin yan kasuwar da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an raba kudaden cikin gaskiya da adalci
- Tallafin ya kunshi kudaden da Shugaba Bola Tinubu da kungiyar gwamnonin APC suka bayar don farfado da tattalin arzikin yan kasuwar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kano - Gwamnatin Kano ta kafa wani babban kwamiti mai mutum 23 domin sa ido kan rabon N8bn a matsayin tallafi ga ’yan kasuwar Singer da gobara ta shafa.
Jaridar Legit Hausa ta rahoto cewa gobarar, wadda ta auku sau biyu a sassa daban-daban na kasuwar, ta haddasa asarar dukiya mai dumbin yawa.

Source: Facebook
An kafa kwamitin raba wa 'yan kasuwa N8bn a Kano
Yayin kaddamar da kwamitin a ranar Talata a Kano, Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Umar Faruq, ya ce an ɗora wa kwamitin alhakin tabbatar da rabon tallafin cikin gaskiya da adalci, in ji rahoton Premium Times.
Umar Faruq, wanda Babban Lauyan Jiha kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Maude, ya wakilta, ya ce an zaɓi mambobin kwamitin daga sassa daban-daban na masu ruwa da tsaki.
A cewarsa, kwamitin wanda SSG zai jagoranta, zai tabbatar da gaskiya da rikon amana tare da bai wa sahihan waɗanda gobarar ta shafa tallafin da ya dace.
Wakilai daga hukumomi da ƙungiyoyi
Sauran mambobin kwamitin sun haɗa da kwamishinoni, wakilan hukumar bada agajin gaggawa ta jiha, rundunar ’yan sanda, hukumar tsaro ta DSS, majalisar masarautar Kano, shugabannin addini da wakilan ’yan kasuwar da gobarar ta shafa.
An ce kwamitin zai tantance girman ɓarnar da aka yi, ya auna asarar kayayyaki da jarin da ’yan kasuwa suka yi, sannan ya tsara ingantaccen tsarin rabon tallafin.
Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rahoto cewa kwamitin zai duba matsalolin da kasuwar ke fuskanta tare da bayar da shawarwari kan yadda za a hana sake aukuwar gobara a nan gaba.

Kara karanta wannan
Babu wasa: Tinubu ya tara gwamnoni, ya gaya masu shirinsa don magance rashin tsaro

Source: Facebook
An yaba da matakin Gwamnatin Kano
Shugaban kungiyar ’yan kasuwar Kano, Sabi’u Bako, ya yabawa gwamnan jihar bisa saurin ɗaukar mataki da kuma kafa kwamitin da zai tabbatar da rabon tallafin cikin tsari.
Ya kuma gode wa gwamnatin tarayya bisa aike da tawaga domin jajanta wa waɗanda lamarin ya shafa, yana mai cewa kwamitin zai gudanar da aikinsa cikin gaskiya da adalci.
Ya ce duk da cewa har yanzu ba a tantance ainihin adadin ’yan kasuwar da abin ya shafa da jimillar asarar da aka yi ba, kwamitin zai tabbatar da cewa waɗanda suka yi asara ne kawai za su amfana da tallafin.
Yadda Kano ta samu tallafin N8bn
Tun da fari, rahoton Legit Hausa ya nuna cewa gobarar ta ja hankalin shugaban kasa, Bola Tinubu, wanda ya amince a bada Naira biliyan biyar a matsayin tallafin jin ƙai ga ’yan kasuwar Singer da abin ya shafa.
Haka kuma, ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar APC (PGF) ta bayar da Naira biliyan uku domin tallafa wa gwamnatin Kano wajen kokarin farfaɗo da kasuwar.
Tun da farko, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin, sun bayar da tallafin Naira miliyan 200 ga waɗanda gobarar ta shafa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

