NiMet Ta Gargadi Kamfanonin Jiragen Sama, Ta Hango Matsala a Kano da Wasu Jihohi

NiMet Ta Gargadi Kamfanonin Jiragen Sama, Ta Hango Matsala a Kano da Wasu Jihohi

  • Hukumar NiMet ta yi gargadin cewa hazo da kura mai kauri za ta mamaye jihohin Arewa yayin da za a samu tsawa da ruwa a jihohin Kudu
  • Saboda haka NiMet ta shawarci masu fama da ciwon numfashi da su dauki matakan kariya yayin da ta gargadi kamfanonin jiragen sama
  • Daga cikin jihohin Arewa da za su fuskanci hazo akwai Kano, yayin da ake ganin ruwan sama zai sauka a Legas, Bayelsa, Rivers da sauransu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet), ta fitar da hasashen yanayi na ranar Laraba, 25 ga watan Fabrairu, 2026.

NiMet ta kuma yi gargaɗin cewa ƙura da hazo za su mamaye yawancin jihohin Arewa, yayin da ake za a samu tsawa da ruwan sama a Kudancin ƙasar.

Kara karanta wannan

Ramadan: Masu kankara za su ya kwantai, za a yi kwanaki ana hazo da ruwa

NiMet ta yi hasashen hazo a jihohin Arewa da kuma ruwan sama a Kudu
An samu hazo mai kauri a Dakar, Senegal, a ranar 16 ga Fabrairu, 2026. Hoto: Cem Ozdel/Anadolu via Getty Images
Source: Getty Images

A cikin rahoton da hukumar ta wallafa a shafinta na X, NiMet ta bayyana cewa hasashen zai fara aiki daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa 11:59 na daren Laraba.

Yadda yanayi zai kasance a Arewa

NiMet ta ce a safiyar Laraba, ana hasashen hazo da ƙura mai kauri a yankin Arewa maso Gabas da kuma wasu sassan jihohin Kano, Katsina da Jigawa.

Hakazalika, jihohin Arewa maso Yamma za su fuskanci matsakaicin hazo, inda za a iya hango nesa da tazarar kilomita biyu zuwa biyar kawai.

A yammacin ranar kuma, ana sa ran yanayin hazo zai ci gaba da mamaye yankin, inda hazon zai ci gaba a Arewa maso Gabas da wasu sassan Kano, Katsina da Jigawa.

Hasashen da masanan hukumar suka yi, ya bayyana cewa sauran jihohin Arewa maso Yamma za su ci gaba da fuskantar matsakaicin hazo.

Karin hasashe a wasu jihohin Arewa

Kara karanta wannan

Babban jami'in gwamnatin Amurka zai dura a Najeriya kan batun ta'addanci

A yankin Arewa ta Tsakiya, NiMet ta bayyana cewa za a samu ƙura da safiya, tare raguwar hangen nesa tsakanin kilomita 2 zuwa 5 saboda hazo.

Hukumar ta kuma bayyana cewa yanayin zai ci gaba a haka har zuwa yammacin raar ba tare da wani babban sauyi ba.

Hadari da yiwuwar ruwa a jihohin Kudu

A jihohin Kudancin Najeriya, ana hasashen za a samu haduwar hadari tare da hasken rana a wasu a safiyar ranar Laraba.

Hukumar hasashen yanayin ta kuma ce akwai yiwuwar samun tsawa hade da ruwan sama a wasu sassan Jihar Legas.

Daga baya, ana sa ran tsawa tare da ruwan sama mai sauƙi a wasu sassan jihohin Ogun, Ondo, Legas, Bayelsa, Delta, Rivers, Cross River da Akwa Ibom.

NiMet ta ce kura za ta yi yawa a ranar Laraba a Kano da wasu jihohin Arewa
Kura ta baibaye wani yanki na birnin Niamey, kasar Nijar. Hoto: Ute Grabowsky/Photothek via Getty Images
Source: Getty Images

Gargaɗin da hukumar NiMet ta yi

NiMet ta yi gargaɗin cewa ƙura na iya rage hangen nesa, don haka ta shawarci masu fama da cututtukan numfashi su ɗauki matakan kariya.

Haka kuma, ta ja hankalin jama’a cewa tsawa na iya zuwa tare da iska mai ƙarfi, don haka ya dace a kasance cikin shiri.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya za ta soke amfani da Naira daga shekarar 2027? Gaskiya ta fito

Bugu da ƙari, hukumar ta buƙaci kamfanonin jiragen sama da su nemi cikakken bayanin yanayi na filayen jiragen sama daga NiMet domin tsara zirga-zirgar su yadda ya kamata.

Karanta rahoton a kasa:

Za a yi kwanaki ana hazo da ruwa

A wani labari, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta sanar da yadda yanayi zai kasance a kwanaki uku masu zuwa a jihohi daban-daban na kasar nan.

Ta bayyana yadda za a shafe kwanakin ana hazo, wasu jihohi kuma za su samu ruwan sama a cikin kwanaki masu zuwa a fadin tarayyar Najeriya.

Hakan na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmi ke cigaba da azumin Ramadan, inda rashin rana ke hana masu sayar da kankara ciniki sosai a jihohi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com