Rokon Majalisar Jihar Kano ga Abba Kabir game da Zargin Amurka kan Kwankwaso

Rokon Majalisar Jihar Kano ga Abba Kabir game da Zargin Amurka kan Kwankwaso

  • Majalisar Dokokin Kano ta bukaci gwamnatin jihar ta yi martani kan zargin da Amurka ke yi kan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
  • Wani dan majalisar ya ce Kwankwaso jagora ne da ke hada kan kasa kuma ya tsaya tsayin daka kan yaki da ta’addanci
  • Majalisar ta kuma amince da kudurorin gina hanyoyi a Tarauni, Madobi da Kura/Garun Malam kafin dage zaman zuwa watan Maris din 2026

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Majalisar Dokokin Kano ta tura roko na musamman ga gwamnatin Kano kan zargin da Amurka ke yi wa Sanata Rabiu Kwankwaso.

Majalisar ta bukaci Abba Kabir da ya dauki matakin mayar da martani kan wasu zarge-zarge da Amurka ke yi kan tsohon gwamnan jihar.

An bukaci Abba Kabir ya kare Kwankwaso bayan zargin Amurka
Gwamna Abba Kabir da jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: Abba Kabir Yusuf, Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

Amurka: Majalisar Kano ta magantu kan zargin Kwankwaso

Kara karanta wannan

Duniya labari: Sanata a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, ana ta rasa 'yan majalisa

Rahoton Leadership ya nuna cewa ana danganta tsohon gwamnan da zargin alaka da ta’addanci tare da kokarin kwace kadarorinsa.

An gabatar da kudurin ne a zaman majalisa ta hannun dan majalisa mai wakiltar Kiru, Usman Tasiu, yayin da Kakakin Majalisa, Jibril Ismail Falgore, ya jagoranci zaman.

Da yake gabatar da bayanin, Tasiu ya bayyana Kwankwaso a matsayin jajirtaccen bawan jama’a wanda ya kawo gagarumin ci gaba a Kano lokacin mulkinsa.

Ya ce tsohon gwamnan ya bayar da muhimmiyar gudunmawa a bangaren ilimi, gine-ginen more rayuwa da kuma tabbatar da zaman lafiya tsakanin mabambantan addinai da kabilu.

Kwankwaso na ci gaba da samun goyon baya kan zargin Amurka
Tsohon gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Kwankwaso. Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso.
Source: Twitter

An fadi gudunmawar Kwankwaso a kasa

A cewarsa, jagoran Kwankwasiyya ya kasance mai hada kan kasa, inda ya rika sasanta rikice-rikice tsakanin Arewa da Kudu tare da rike matsaya mai karfi kan yaki da ta’addanci.

Ya kara da cewa Kwankwaso ya kasance uba kuma mai ba da shawara ga matasa da dama ba tare da la’akari da bambancin addini ba, cewar The Guardian.

Tasiu ya bukaci gwamnatin Kano da ta tuntubi Gwamnatin Tarayya domin tattaunawa da hukumomin Amurka kan lamarin ta hanyar diflomasiyya.

Kara karanta wannan

Masu daukar nauyin ta'addanci sun bani, Majalisar Dinkin Duniya ta yi maganar kashe Musulmi

Ya nemi a dauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa ba a ware shi bisa rashin adalci ba a kowace doka da za a gabatar a majalisar dokokin Amurka.

Bayan muhawara, majalisar ta amince da kudurin baki daya tare da bukatar gwamnatin Kano ta dauki matakin da ya dace kan batun.

A gefe guda kuma, majalisar ta amince da wasu kudurori na bukatar a gina hanyoyi a wasu sassan Tarauni, Madobi da Kura/Garun Malam.

Daga bisani, majalisar ta dage zamanta zuwa ranar Litinin, 2 ga Maris, 2026 bayan kudurin dage zaman da Shugaban Masu Rinaye, Lawan Hussaini, ya gabatar.

Zargin Amurka: Majalisar shari'a ta kare Kwankwaso

An ji cewa Majalisar Kolin Shari'a ta Najeriya ta ba Sanata Rabiu Musa Kwankwaso kariya kan zargin da wani dan majalisar Amurka ya masa.

Majalisar ta ce babu gaskiya a zargin da wasu 'yan majalisar Amurka ke yi wa Kwankwaso, tana cewa akwai alamar an dagora da bayanai marasa inganci.

Wani dan majalisar Amurka ya nemi a hana Rabiu Kwankwaso biza da nufin hana shi shiga kasar kan zargin tauye hakkin addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.