Dalilin da Ya Sanya har Yanzu Hukumar EFCC ba Ta Gurfanar da Nasir El Rufai ba

Dalilin da Ya Sanya har Yanzu Hukumar EFCC ba Ta Gurfanar da Nasir El Rufai ba

  • Hukumar EFCC ta yi karin haske game da dalilin da ya sanya har zuwa wannan lokaci ba ta gurfanar da Malam Nasir El-Rufai ba
  • Wata majiya daga EFCC ta bayyana cewa hukumar son gudanar da cikakken bincike kafin ta gurfanar da tsohon gwamnan a kotu
  • Ofishin yada labaran El-Rufai ya koka kan yadda tsohon gwamnan ya shafe kwanaki tara a tsare ba tare da ICPC ta ba shi beli ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta bayyana dalilin da ya sanya har yanzu ba ta gurfanar da Nasir El-Rufai a kotu ba.

EFCC ta yi bayani cewa ba za ta yi gaggawar kai tsohon gwamnan na Kaduna kotu ba har sai ta kammala dukkan binciken da take yi kansa.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Halin da El Rufai ya shiga yayin da yake tsare a hannun ICPC

Hukumar EFCC ta yi bayani game da gurfanar da El-Rufai a gaban kotu.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a wajen wani taron ADC. Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

EFCC na son tattara hujjoji kan Nasir El-Rufai

Wata majiya mai tushe daga hukumar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) cewa EFCC na son gudanar da aiki na ƙwararru domin tabbatar da gaskiyar zarge-zargen da ake masa.

Tsohon gwamnan ya shafe kwanaki a hannun EFCC, daga ranar 16 ga Fabrairu zuwa 18 ga Fabrairu, 2026, kafin daga baya ya koma wajen hukumar ICPC.

Majiyar ta bayyana cewa laifuffukan da ake zargin El-Rufai da su suna da matuƙar nauyi, saboda haka hukumar ke son tattara dukkan hujjoji kafin shigar da ƙara.

Lokacin da EFCC za ta gurfanar da El-Rufai

Ko da yake EFCC ta bayar da belin tsohon gwamnan a ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, hukumar ICPC ce ta sake kama shi nan take domin nata binciken.

Majiyar EFCC ta bayyana cewa:

"Har yanzu muna binciken tsohon gwamnan; ba mu kammala ba muka ba da shi beli a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

El Rufai ya sake kinkimo rigima a cikin watan azumi, ya maka ICPC a gaban kotu

"Za mu ci gaba da namu binciken, kasancewar ya shiga hannun hukumar ICPC a ranar da muka ba da shi beli, za mu jira ya gama da su tukunna.
"Za mu gurfanar da shi gaban kotu da zarar mun kammala binciken zarge-zargen da ake yi masa."
Hukumar EFCC ta ce za ta gurfanar da El-Rufai da zarar ta kammala bincike.
Allon shiga hedikwatar hukumar EFCC da ke birnin tarayya Abuja. Hoto: @officialEFCC
Source: Facebook

Halin da El-Rufai ke ciki a hannun ICPC

Mai tamakawa El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa ya zuwa yau Talata, tsohon gwamnan ya shafe kwanaki tara a tsare a hannun hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa guda biyu.

Adekeye ya koka da cewa har yanzu lauyoyin El-Rufai ba su sami martani daga ICPC ba game da buƙatar belin da suka shigar, in ji rahoton Vanguard.

Haka kuma, Adekeye ya bayyana cewa hukumar ICPC ba ta nuna musu wata takardar kotu da ke ba su damar ci gaba da tsare shi ba, bayan da wa'adin sa'o'i 48 da kundin tsarin mulki ya ba da na tsare mutum ba tare da tuhuma ba ya cika.

El-Rufai ya maka DSS a kotu

A wani labari, mun ruwaito cewa, Malam Nasir El-Rufai ya nemi kotu ta soke tuhumar da hukumar DSS ke masa tare da biyan sa diyyar N2bn.

Kara karanta wannan

Tsare El Rufai: Jigo a ADC ya kausasa harshe kan hukumar ICPC, ya ba ta zabi 2

Lauyoyin Nasir El-Rufai sun gabatar da hujjoji guda 17 inda suka ce tuhumar ta saba wa hakkin dan adam da kundin tsarin mulki.

Mai Shari'a Joyce Abdulmalik ce za ta saurari wannan bukata a ranar 25 ga watan Fabrairu, 2026 a babbar kotun tarayya da ke Abuja.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com