Babbar Magana: Shugaban Rundunar 'Yan Sandan Najeriya Ya Yi Murabus, An Ji Dalili
- Rahotanni daga fadar shugaban kasa sun tabbatar da cewa Bola Tinubu ya umarci Sufeto Janar na Yan Sandan Najeriya ya yi murabus
- Majiyoyi daga hedkwatar rundunar yan sanda sun tabbatar da lamarin, sun ce an fara shirin mika ragamar mulki ga wani daga cikin mataimakansa
- Har kawo yanzu dai babu wata sanarwa a hukumance amma majiyoyi sun ce Shugaba Tinubu ya gana da IGP Egbetokun a jiya Litinin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - An fara yada jita-jitar cewa Sufeto Janar na Rundunar 'Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya yi murabus daga mukaminsa.
Wasu majiyoyi daga rundunar ‘yan sandan sun tabbatar cewa an sanar da manyan jami’ai a ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairu, 2026 game da murabus ɗin Egbetokun.

Source: Facebook
Sufeton Yan Sanda ya yi murabus
Rahoton da jaridar Leadership Hausa ta wallafa da safiyar yau Talata, 24 ga Fabarairun 2026 ya nuna har yanzu ba a fito an bayyana dalilin ajiye aikin Sufeton Yan Sandan ba.
Rahotanni sun nuna cewa Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya (IGP) ya yi murabus daga mukaminsa ne bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu.
Wata majiya a fadar shugaban kasa ta ce an nemi IGP Egbetokun ya ajiye mukaminsa ne a wani taro da ya yi da Shugaban kasa a Aso Rock da ke Abuja a ranar Litinin.
Ana shirin maye gurbin Kayode Egbetokun
Ana sa ran maye gurbinsa da Tunji Disu, wanda ke rike da mukamin Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sanda (AIG).
Ko da yake har yanzu ba a sanar da hakan a hukumance ba, majiyoyi daga fadar shugaban kasa da hedkwatar ’yan sanda sun shaida wa Premium Times cewa ana shirin taron mika mulki daga Egbetokun zuwa Disu.
Shugaba Tinubu ne ya nada Mista Egbetokun a matsayin Sufeto Janar na 22 a ranar 19 ga Yuni, 2023. Hukumar Jin Dadin ’Yan Sandan Najeriya ta tabbatar da nadin nasa a ranar 31 ga Oktoban 2023.
Yadda aka kara wa sufetan yan sanda wa'adi
An nada shi yana da shekaru 58, kuma ya kamata ya yi ritaya a ranar 4 ga Satumba, 2024, bayan ya cika shekaru 60 da doka ta tanada.
Sai dai Majalisar Tarayya ta gyara dokar ’yan sanda, inda ta ba shi damar kammala cikakken wa’adinsa na shekaru hudu a matsayin Sufeto Janar, muddin shugaban kasa bai cire shi ba.
Saboda haka, ana sa ran zai kammala wa’adinsa har zuwa ranar 31 ga Oktoba, 2027 kafin wannan ci lamari.

Source: Twitter
Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, Fadar shugaban kasa ba ta fitar da sanarwar hukumance kan murabus din shugaban yan sandan ba.
Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga, da kakakin ’yan sanda na kasa, Ben Hundeyin, bai samu nasara ba.
Sai dai wata majiya ta ce ana sa ran za a fitar da sanarwa a hukumance nan gaba kadan a ranar Talata.

Kara karanta wannan
Babu wasa: Tinubu ya tara gwamnoni, ya gaya masu shirinsa don magance rashin tsaro
'Yan sanda 5,000 za su ajiye aiki a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa hukumar kula da fanshon ’yan sandan Najeriya ta bayyana cewa adadin jami'an da za su yi ritaya daga aiki a shekarar 2026 sun kai 5,000.
Mataimakin kwamishinan ’yan sanda (DCP) Sani Doki Yusuf, wanda shi ne Kwamishinan fanshon ’yan sanda a hedkwatar rundunar da ke Abuja, ne ya tabbatar da hakan.
Ya yi kira ga jami’an da ke aiki da waɗanda suka riga suka yi ritaya da su sabunta bayanansu, domin kauce wa jinkiri wajen karɓar hakkokin fansho.
Asali: Legit.ng

