Sheikh Murtala Asada Ya Yi Fatali da Neman Yafiyar Tinubu, Ya Jero Dalilansa

Sheikh Murtala Asada Ya Yi Fatali da Neman Yafiyar Tinubu, Ya Jero Dalilansa

  • Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Murtala Asada, ya yi kakkausar suka ga Shugaban kasa Bola Tinubu da ye nemi jama'a su yafe masa
  • Malanin ya nuna takaici kan yadda Tinubu da manyan Najeriya suka halarci bikin kamun kifin Argungu duk da kashe-kashen da ake yi a Arewa
  • Ya bukaci talakawa su gyara halayensu domin samun sauki daga Allah SWT, sannan a daina nema wa 'azzalumai' neman kariyar Ubangiji

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Sokoto – Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Murtala Asada, ya yi kakkausar suka ga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Malamin ya bayyana haka ne bayan Tinubu ya nemi afuwar talakawan Najeriya, lamarin da Sheikh Murtala Asada ya ce ba za ta sabu ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta gyara halin tubabbun 'yan ta'adda sama da 100, za su dawo cikin mutane

Sheikh Asada ya fusata da neman afuwar Tinubu
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Sheikh Murtala Asada Hoto: Asiwaju Bola Tinubu, Malam Murtala Bello Asada.
Source: Facebook

A wani bidiyo da Duke of Nigeria ya wallafa a shafin X, malamin ya zargi Gwamnatin Tarayya da jefa Najeriya cikin matsaloli da masifu iri-iri.

Sheikh Asada ya dura kan Bola Tinubu

Ya ce akwai takaici yadda Shugaban kasa da gwamnoni suka hallara a Argungu da ke jihar Kebbi, duk da cewa ana zargin kashe mutane da dama a sassan Arewacin Najeriya a lokacin.

Sheikh Murtala Asada ya bayyana cewa ba zai taba yafe wa Shugaban kasa ba saboda irin wahalhalun da talakawa suke ciki a karkashin wannan gwamnati.

Sheikh Murtala Asada ya zargi gwamnatin Tinubu da sa mutane a wahala
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

A cewarsa, an kakaba wa jama’a haraji, an janye tallafin mai, kuma rayuwa ta kara tsananta a sassa daban-daban na Najeriya.

A cikin kalamansa, ya ce:

“Ba za mu yafe ba. Ga bala’i nan an kakaba wa mutane, ga haraji an kakaba wa mutane, an janye tallafin mai. Amma duk da haka wasu suna jiran lokacin kamfen su zo su yaudare mu."

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba Aminu Ado Bayero jagorancin ciyar da talakawa a Ramadan

"Don Allah, yanzu sai an fada maka ne? Ba sai mu Murtala Asada mun ce a ba ka kashi ba, mutane da kansu za su ba ka kashi.”

Malamin ya kara da cewa yayin da ake zargin an kashe sama da mutum 100 a wasu sassan Arewa cikin mako guda, shugabanni sun tafi Argungu ana shagulgula, ana kide-kide tare da taron mata da maza, lamarin da ya ce bai dace ba.

Shawarar Sheikh Asada ga talakawa

Duk da sukar da ya yi wa gwamnati, Sheikh Asada ya kuma ja kunnen talakawan Najeriya da su gyara halayensu.

A cewarsa:

“Allah Yana kawo mana sauki idan mun gyara. Wallahi talakawa sai mun gyara. Idan kana tare da azzalumi kana cewa Allah Ya taimake ka, wannan izgili ne. Azzalumai karya hannayensu ake yi, ba a yi musu irin wannan addu’a ba.”

Matawalle: Malami ya shirya bayyana a kotu

A baya, mun wallafa cewa Malamin addini, Sheikh Murtala Asada, ya ce sakonsa game da zarge-zargen da ya yi wa Bello Matawalle, ya kai ga Fadar Shugaban Ƙasa.

Kara karanta wannan

Sheikh Bashir Aliyu ya yi wa Tinubu raddi kan rokon 'yan Najeriya su yafe masa

Sheikh Asada ya jaddada cewa a shirye ya ke ya gurfana a gaban kotu, yana mai cewa yana da hujjoji kan zarge-zargen da yake yi wa tsohon gwamnan.

Ya bayyana takaici game da yadda duk da irin waɗannan munanan zarge-zarge, Matawalle ya ci gaba da zama a kujerarsa ta Minista ba tare da bincike ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng