Akwai Kura: Wasu Manyan Alkalai a Najeriya Na Iya Shiga Matsala da NJC Ta Fara Bincikensu

Akwai Kura: Wasu Manyan Alkalai a Najeriya Na Iya Shiga Matsala da NJC Ta Fara Bincikensu

  • An samu korafe-korafe masu girma kan wasu manyan alkalan Najeriya masu aikin tabbatar da adalci a wajen shari'a
  • Hukumar shari'a ta kasa (NJC) a Najeriya ta yi azama wajen fara bincike domin zakulo gaskiyar abin da ke faruwa
  • Binciken dai kamar yadda majiyoyi suka bayyana ya shafi manyan alkalai wadanda suka har da shugabannin kotu

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar shari’a ta kasa (NJC) ta ƙaddamar da wani bincike na sirri amma mai faɗin gaske kan wasu manyan alkalai a kasar nan.

Binciken dai da hukumar NJC ta fara ya shafi har da shugabannin kotuna, bayan samun korafe-korafe.

NJC ta fara bincike kan wasu manyan alkalai
Alkalin alkalai ta Najeriya, Mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun Hoto: @SupremeCourtNg
Source: Twitter

Jaridar Premium Times ta kawo rahoton cewa majiyoyi daga cikin hukumar ne suka shaida mata hakan.

NJC na da iko kan alkalan Najeriya

Hukumar NJC ita ce hukumar da kundin tsarin mulki ya ba wa alhakin naɗawa, ƙarin girma, da kuma ladabtar da jami’an shari’a a Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamna ya sanya doka: Ƴan takara za su biya N150m don yakin neman zabe a jiharsa

Hukumar mai mambobi 24, wacce babbar alkalin alkalan Najeriya (CJN), Kudirat Kekere-Ekun ke jagoranta, tana samun ikonta ne daga sashe na 20 na sashe na ɗaya sakin layi na uku na kundin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999 (wanda aka yi wa gyara).

Wane bincike ake yi kan alkalai?

Majiyoyin sun bayyana cewa, wannan “bincike na musamman” ya biyo bayan ɗimbin “korafe-korafe masu tada hankali” da aka shigar kan wasu “manyan jami’an shari’a” waɗanda ba a ambaci sunayensu ba.

Wani jami’i da ke da masaniya kan lamarin ya bayyana cewa:

“Zargin da ake yi wa ɗaya daga cikin manyan alkalan yana da girma sosai, har ta kai ga CJN ta ba da umarnin gudanar da bincike na gaggawa domin gano waɗanda ke da laifi da kuma tsabtace aikin shari’a."

Ya ƙara da cewa ana gudanar da binciken ne cikin sirri kuma mutane kalilan ne kawai suka sani.

An samu korafe-korafe kan alkalai

Majiyar ta ci gaba da cewa:

“Zan iya shaida muku cewa NJC ta karɓi takardun korafe-korafe da dama a kwanan nan, waɗanda ke zargin manyan laifuffuka na rashin ɗa’a, yin jabun takardu, sauya shekarun haihuwa, da kuma bayyana karya game da kadarori.”

Kara karanta wannan

Babban jami'in gwamnatin Amurka zai dura a Najeriya kan batun ta'addanci

"Damuwa da girman waɗannan zarge-zarge, CJN tana tattara mambobin NJC domin ɗaukar matakin gaggawa na gudanarwa. Ba ta son waɗannan zarge-zargen su ƙara rage amincewar da jama'a ke da shi ga ɓangaren shari'a."

Majiyoyin jaridar sun ki bayyana sunayen alkalan da ake bincika ko kuma mutanen da suka shigar da korafe-korafen, suna masu cewa ba su da ikon tattauna batun a fili.

Alkalin alkalai ta umarci fara bincike kan wasu alkalai
Shugaba Bola Tinubu da mai shari'a Kudirat Kekere-Ekun lokacin rantsar da ita Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Ba a ji ta bakin CJN da NJC ba

Yayin da aka tuntuɓi Tobi Soniyi, mataimaki na musamman ga CJN kan kafafen yaɗa labarai, ya tura dukkan tambayoyin zuwa ga hukumar NJC, inda ya ce ba a ba shi bayani kan batun ba.

Haka ita ma mataimakiyar daraktan yaɗa labarai na NJC, Kemi Babalola-Ogedengbe, ta bayyana cewa ba ta da masaniya kan wani bincike makamancin wannan.

Tsohon alkalin alkalai ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi rashi na daya daga cikin tsofaffin alkalin alkalai na Najeriya, wanda ya riga mu gidan gaskiya.

Tsohon alkalin alkalan Najeriya, Mohammed Lawal Uwais, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 88 a duniya.

Mohammed Uwais ya hau kujerar alkalin alkalan Najeriya a shekarar 1995, inda ya yi aiki har zuwa shekarar 2006 kafin ya yi ritaya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng