Abin da Tinubu Ya Gayawa Gwamna Abba kan Siyasar Kano bayan Kalaman Kwankwaso

Abin da Tinubu Ya Gayawa Gwamna Abba kan Siyasar Kano bayan Kalaman Kwankwaso

  • Mai girma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya tara gwamnoni domin yin buda baki na azumin watan Ramadan da Lent
  • Shugabann na Najeriya ya aika da sako ga Gwamna Abba Kabir Yusuf dangane da abubuwan da ke faruwa a siyasar jihar Kano
  • Hakazalika, Tinubu ya mika bukatarsa ga gwamnonin jam'iyyar APC yayin buda baki a daren ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairun 2026

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi buda baki tare da wasu gwamnonin jihohi a fadar Aso Rock Villa.

A yayin buda bakin, Shugaban kasar ya aika sako ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf wanda ya shigo APC kwanan nan.

Shugaba Tinubu ya aika sako ga Gwamna Abba
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa an gudanar da buda bakin ne a daren ranar Litinin, 23 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Babu wasa: Tinubu ya tara gwamnoni, ya gaya masu shirinsa don magance rashin tsaro

Bola Tinubu ya yi buda baki da gwamnoni

Taron ya haɗa da addu’o’in addinai daban-daban waɗanda babban limamin fadar shugaban kasa, Abdulwaheed (na ɓangaren Musulmi) da Gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas (na ɓangaren Kiristoci) suka jagoranta.

Jaridar Daily Trust ta ce Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila, da wasu mambobin majalisar ministoci ne suka halarci taron.

Gwamnonin sun haɗa da Alex Otti (Abia), Dapo Abiodun (Ogun), Babagana Zulum (Borno), Inuwa Yahaya (Gombe), Ahmed Aliyu (Sokoto), Sheriff Oborevwori (Delta), Abdullahi Sule (Nasarawa), Abba Kabir Yusuf (Kano), da Agbu Kefas (Taraba), da dai sauransu.

Me Tinubu ya gayawa Gwamna Abba?

Yayin da yake jawabi, Shugaba Tinubu ya yi kira ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya yi amfani da hikima da haƙuri game da takaddamar siyasa da ake yi a jihar.

Gwamnan dai kwanan nan ya koma jam’iyyar APC bayan ya yi watsi da uban gidansa na siyasa kuma tsohon gwamna, Dr. Rabiu Kwankwaso da kuma jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan

Buda baki: Shugaba Tinubu ya sha ruwa tare da wasu gwamnoni a watan Ramadan

Da yake magana a wurin buɗan bakin na ranar Litinin, Shugaba Tinubu ya ce:

“Na yi farin ciki da na ga Abba na Kano, koda yake hular ja ce, ba ta da bambanci da APC. Na ga rikicin a labaran TVC, don Allah a bi komai cikin sauki.”
Tinubu ya aika sako ga Gwamna Abba Kabir Yusuf
Shugaba Bola Tinubu a wajen buda baki da gwamnoni Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Sakon Tinubu ga gwamnonin APC

Haka zalika, Shugaba Tinubu ya yi kira da a rungumi kowa a cikin jam’iyya mai mulki ta APC, inda ya buƙaci gwamnoni da su ba matasan mambobin jam’iyyar dama.

“Zan ba wa waɗanda muke jam’iyya ɗaya shawara cewa don Allah ku sani cewa su ma waɗancan ƙanana (matasa) suna kuka. Ku haƙura da kowa. A ba matasanmu dama."

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya magantu kan rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwarsa kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Shugaba Tinubu ya sha alwashin samar da 'yan sandan jihohi domin kawo karshen matsalar rashin tsaron da ake fama da ita.

Hakazalika, ya ba 'yan Najeriya tabbacin cewa zai cika alkawuran da ya dauka kafin hawa karagar mulki a zaben shekarar 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng