Abin da Tinubu Ya Fada wa Abba da Sauran Gwamnoni a Wurin Buda Baki a Abuja

Abin da Tinubu Ya Fada wa Abba da Sauran Gwamnoni a Wurin Buda Baki a Abuja

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci masu mulki da shugabannin musulmi da kiristoci su tausayawa talakawa musamman a wannan lokaci na azumi
  • Tinubu wanda ya shiga Aso Rock a 2023 ya ce haɗuwar azumin Ramadan da na Kiristoci (Lent) na nuna cewa dukkan addinai suna da manufa ɗaya
  • A wurin taron shan ruwa da ya shirya a fadar shugaban kasa, Tinubu ya yabi gwamnan Borno bisa tallafin da ya raba wa musulmi da kiristoci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaba Bola Tinubu ya bukaci shugabanni Musulmi da Kiristoci da su nuna ƙarin tausayi ga talakawa da marasa galihu ta hanyar tsara manufofi da shirye-shiryen da za su amfanar da mafi yawan jama’a.

Shugaban ya yi wannan kira ne a ranar Litinin yayin da ya karɓi bakuncin gwamnonin jihohi domin buda baki na haɗin kan addinai a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Abin da Tinubu ya gayawa Gwamna Abba kan siyasar Kano bayan kalaman Kwankwaso

Shugaba Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a taron buda baki da gwamnoni Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da shugaban kasar ya wallafa a shafinsa na X a daren jiya Litinin, 23 ga watan Janairu, 2026.

Bola Tinubu ya ja hankalin musulmai da kiristoci

A sanarwar, Shugaba Tinubu ya ce haɗuwar azumin Ramadan da na Kiristoci (Lent) na nuna cewa dukkan addinai suna da manufa ɗaya ta ɗabi’a, ladabi, sadaukarwa da ƙaunar juna.

“Abin farin ciki ne da girma mu sake kasancewa tare domin gode wa Allah da Ya raya mu mu ga wani Ramadan, wanda ya zo daidai da lokacin Lent na Kiristoci,” in ji shugaban.

Ya ce wannan lokaci na azumi da tuba ya kamata ya zama damar da shugabanni za su zurfafa tunani kan halin da talakawa ke ciki tare da tsara shirye-shiryen da za su shafi rayuwar jama’a kai tsaye.

Nasihar Bola Tinubu ga gwamnonin jihohi

Tinubu ya jaddada cewa ana iya ƙara yin abin da ya fi wanda aka yi a baya a wannan lokaci, musamman wajen rage talauci da bai wa matasa damar da za su farfado da tattalin arzikinsu.

Kara karanta wannan

Babu wasa: Tinubu ya tara gwamnoni, ya gaya masu shirinsa don magance rashin tsaro

“Ku jawo kowa, ku gina tsari a wannan lokaci na kara imani, haɗin kai da sadaukarwa. Ku bai wa matasa dama,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, bisa rabon tallafin Ramadan ga Musulmi da Kiristoci, yana mai cewa hakan na nuna kyakkyawan ruhin haɗin kai.

Wurin buda baki.
Shugaba Bola Tinubu, Kashim Shettima da wasu gwamnoni a taron buda baki a fadar shugaban kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Haka zalika, ya yi maraba da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, tare da yin tsokaci kan wasu rahotanni da ya gani game da Jihar Ebonyi.

"Ina farin ciki da ganin Abba daga Kano. Duk da cewa hular ja ce, amma ba ta bambanta da ta gwamnan jihar Ebonyi ba. Gwamnan Ebonyi, na ga rikicin da ke faruwa a labarai, don Allah nuna adalci da tausayi," in ji shi.

Tinubu ya nemi yafiyar 'yan Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya roki yan Najeriya su yafe masa idan ya aikata wani kuskure a karkashin mulkinsa.

Tinubu ya yi wannan roƙon ne ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026 yayin da ya halarci buɗe Tafsirin Alkur'ani mai girma na Ramadan a masallacin fadar shugaban ƙasa da ke Abuja .

Ya bukaci 'yan Nijeriya na kowane addini da su yi addu'ar neman zaman lafiya tare da ba da goyon baya ga ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ta'addanci, 'yan bindiga, da sauran matsalolin tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262