Iftar: Shugaba Tinubu Ya Yi Buda Baki tare da Wasu Gwamnoni a Watan Ramadan

Iftar: Shugaba Tinubu Ya Yi Buda Baki tare da Wasu Gwamnoni a Watan Ramadan

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi buda bakin azumi da gwamnoni da kusoshin gwamnati a fadar shugaban kasa da ke Abuja
  • Rahoto ya nuna cewa an shirya buda baki na Musulmi da Kiristoci saboda yadda azumin Ramadan ya hadu a ibadar azumin Lent
  • Gwamnonin da aka hanga a wurin buda bakin sun hada da Gwamna Ahmed Aliyu, Uba Sani, Hope Uzodinma, Alex Otti da sauransu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya shirya buda bakin azumi watau Iftaar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya gayyaci gwamnoni da manyan jiga-jigan gwamnati, inda suka yi buda baki bayan kai azumin yau Litinin, 6 ga watan Ramadan, 1447AH daidai da 23 ga Fabrairu, 2026.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na magana a wurin buda baki Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Tinubu ya yi buda baki da wasu gwamnoni

Kara karanta wannan

Kano: Sauya shekar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jawo tarnaki a jam'iyyar APC

The Nation ta ruwaito cewa taron buda bakin ya fara ne jim kaɗan bayan ƙarfe 6:30 na yamma, daidai lokacin da rana ke faduwa.

Legit Hausa ta fahimci ce wannan shi ne karo na uku a jere da shugaban ƙasar ke gayyatar gwamnoni domin yin Iftaar tare a fadar shugaban kasa tun bayan hawansa mulki a 2023.

Gwamnonin da suka halarci wannan buda baki sun kunshi musulmai, wadanda suke azumin Ramadan, da kiristoci da suka ibadarsu ta azumi watau Lent.

Gwamnonin da suka halarci taron buda baki

Daga cikin gwamnonin da aka gani suna isa fadar shugaban kasa tun daga ƙarfe 6:15 na yammacin yau Litinin akwai:

1. Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo

2. Gwamna Dapo Abiodun na jihar Ogun

3. Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo

4. Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi

5. Gwamna Babagana Umarq Zulum na jihar Borno

6. Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe

7. Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sakkwato

8. Gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta

9. Gwamna Mohammed Umaru Bago na jihar Neja

Kara karanta wannan

Tinubu ya fusata kan kashe kashe a taron APC, ya dauki kwakkwaran mataki

10. Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa

11. Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa

12. Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano

13. Gwamna Agbu Kefas na jihar Taraba

14. Gwamna Alex Otti na jihar Abia

15. Gwamna Uba Sani na Kaduna

16. Gwamna Francis Nwifuru na Ebonyi

Haka kuma mataimakin gwamnan Jihar Bauchi ya halarci taron.

Tinubu.
Shugaba Tinubu na gaisawa da gwamnoni a taron buda baki a fadar shugaban kasa Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shettima ya halarci buda baki da Tinubu

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, tare da wasu mambobin majalisar ministoci sun halarci buda bakin.

Iftar ɗin na daga cikin shirye-shiryen Ramadan na shekara-shekara da shugaban ƙasa ke yi, inda yake karɓar masu riƙe da muƙaman siyasa, manyan jami’an gwamnati, sarakunan gargajiya da kuma jakadun ƙasashen waje.

A lokutan da suka gabata, shugaban ƙasar kan yi amfani da wannan dama wajen kira ga haɗin kai da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyu daban-daban.

A baya, kun ji cewa Shigaba Bola Tinubu ya halarci bude tafsirin Alkur'ani a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa da ke birnin tarayya Abuja

Ya bukaci 'yan Nijeriya na kowane addini da su yi addu'ar neman zaman lafiya tare da ba da goyon baya ga ƙoƙarin da ake yi na yaƙi da ta'addanci, 'yan bindiga da zauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262