Ana tsaka da Hada Hada, Gobara Ta Kama a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed
- Hukumar FAAN ta tabbatar da tashin gobara a wani sashen filin jirgin sama na Muratala Muhammed da ke jihar Legas
- Rahotanni sun nuna cewa gobarar ta kama a wani bangaren da ake yi wa gyara domin sabunta shi da nufin inganta walwalar fasinjoji
- FAAN ta kwantar da hankulan fasinjoji da ke kai komo a filin jirgin, inda ta ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon gobarar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos, Nigeria - Rahotannin da muka samu daga jihar Legas sun nuna cewa gobara ta tashi a wani bangaren filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammed.
Bayanai sun nuna cewa ibtila'in gobarar ya faru ne tsohon bangaren tashar jirgin saman da yammacin yau Litinin, 23 ga watan Fabrairu, 2026.

Source: UGC
Gobara ta tashi a filin jirgin sama a Legas

Kara karanta wannan
Juma'a: Isra'ila ta jibge dakaru, ta kakaba wa Musulmi takunkumin shiga masallacin Kudus
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a halin yanzu ana kan aikin gyara bangaren da gobarar ta kama domin sabunta shi tare da inganta jin dadi da walwalar fasinjoji.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu wasu cikakkun bayanai kan musabbabin gobarar da ta afku a filin jirgin saman.
Sai dai an bayyana cewa gobarar ta takaita ne a wani ɓangare na tsohuwar tashar jiragen sama wanda ake gyarawa domin daidaita shi da sababbin ka’idoji.
FAAN ta tabbatar da faruwar lamarin
Daraktan Hulɗa da Jama’a da Kare Haƙƙin Fasinjoji na Hukumar Kula da Filayen Jiragen Sama ta Kasa (FAAN), Henry Agbebire, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Ya ce jami’an hukumomin da abin ya shafa sun isa wurin domin shawo kan lamarin cikin gaggawa.
A wata sanarwar da FAAN ta wallafa a shafin X, Henry Agbebire ya ce:
“Mun samu labarin tashin gobarar, kuma muna wurin a yanzu haka. Za mu fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba,” in ji shi.
Wane mataki hukumar FAAN ta dauka?
Ya ƙara da cewa sashen ba da agajin gaggawa na hukumar FAAN ya fara aiki domin hana gobarar yaɗuwa zuwa sauran sassa a filin jirgin.
“Jami'anmu na sashen kashe gobara sun dukufa aiki a halin yanzu domin shawo kan lamarin,” in ji Agbebire.
Agbebire ya bai wa jama’a tabbacin cewa babu wanda ya rasa rayuwarsa sakamakon wannan gobarar da ta auku.
“Ba a samu asarar rai ba. Za mu ci gaba da ba da ƙarin bayani,” in ji shi.

Source: Original
Ya kuma shawarci fasinjoji da masu amfani da tashar jirgin su kwantar da hankalinsu yayin da jami’ai ke ƙoƙarin kashe gobarar gaba ɗaya tare da tantance irin ɓarnar da ta faru.
Ana sa ran hukumar FAAN za ta fitar da cikakkiyar sanarwa nan gaba domin ƙarin haske kan lamarin.
Gobara ta tashi a wata kasuwa a Kano
A wani rahoton, kun ji cewa wata mummunar gobara ta tashi a kasuwar Fatima Simra Multi-Purpose da ke yankin Dakata a cikin birnin jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa gobara ta babbake shaguna akalla 50, lamarin da ya yi sandin asarar makudan kudi a wurin kasuwancin.
Shugaban kwamitin gobara na kasuwar, Dauda Haruna Chula, ya bayyana cewa shagunan da abin ya shafa galibinsu na kananan 'yan kasuwa ne masu harkar samar da mai, da kuma masu sake sarrafa robobi da leda.
Asali: Legit.ng
