El Rufai Ya Sake Kinkimo Rigima a cikin Watan Azumi, Ya Maka ICPC a gaban Kotu

El Rufai Ya Sake Kinkimo Rigima a cikin Watan Azumi, Ya Maka ICPC a gaban Kotu

  • Malam Nasir El-Rufai ya shigar kara gaban kotu kan samamen da hukumar ICPC ta kai gidansa na Abuja a ranar 4 ga watan Fabrairu, 2026
  • Tsohon gwamnan ya bukaci kotun ta ba da umarnin a biya shi diyyar Naira biliyan daya saboda bata masa suna da shiga gidansa ba bisa ka'ida ba
  • El-Rufai ya gabatar da hujjojinsa a gaban kotu a kokarin tabbatar da cewa samamen da aka kai gidansa ya sabawa kundin tsarin mulki

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Tsohon gwamnan jihar Kaduna kuma daya daga cikin jagororin jam'iyyar hadaka, ADC, Malam Nasir El-Rufai ya tattago rigimar shari'a da hukumar yaki da rashawa ta ICPC.

El-Rufai ya maka hukumar ICPC a gaban kotu kan samamen da ta kai gidansa da ke babban birnin tarayya Abuja, wanda ya bayyana a matsayin karya doka.

Kara karanta wannan

Tsare El Rufai: Jigo a ADC ya kausasa harshe kan hukumar ICPC, ya ba ta zabi 2

El Rufai.
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Facebook

El-Rufai ya nemi diyyar N1bn daga ICPC

Jaridar Vanguard ta ce El-Rufai, ya shigar da ƙarar hukumar ICPC tare da neman ta biya shi diyya ta Naira biliyan ɗaya bisa zargin mamaye gidansa da ta yi ba bisa ka’ida ba.

El-Rufai ya shigar da wannan kara a gaban babbar kotun tarayya ta Abuja ta hannun lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin Oluwole Iyamu, SAN.

Ya roƙi kotu ta ayyana sammacin bincike da Kotun Majistare ta bayar ranar 4 ga Fabrairu, 2026 wanda ya ba da izinin bincike da kwace kayayyaki a gidansa, a matsayin wanda ya saba doka.

Abubuwan da El-Rufai ya nema a kotu

Ya buƙaci kotu ta ayyana cewa sammacin binciken “ba shi da inganci saboda rashin fayyace bayanai, kurakuran rubutu, rashin bayyana yadda za a aiwatar da shi, wuce gona da iri, da kuma rashin dalili mai gamsarwa.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa tsohon gwamnan ya shigar da ƙarar ta hanyar takardar ƙorafi mai lamba FHC/ABJ/CS/345/2026, inda ya sanya ICPC a matsayin wanda ake ƙara na farko.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Jami'an ICPC sun kai samame gidan El Rufai, sun je neman wani abu

El-Rufai ya kuma sanya Alkalin Kotun Majistare ta Abuja; Sufeto Janar na ’Yan Sanda (I-G); da Antoni Janar (AGF) a matsayin waɗanda ake ƙara na biyu zuwa na huɗu.

A cikin ƙarar da aka shigar ranar 20 ga Fabrairu, tsohon gwamnan, wanda ake tsare da shi, ya nemi abubuwa bakwai daga kotu, kamar yadda Daily Post ta kawo.

ICPC.
Babban ofishin hukumar ICPC da ke birnin tarayya Abuja Hoto: @icpcnigeria
Source: Twitter

El-Rufai ya nemi a dawo da kayan gidansa

Ya roƙi kotu ta ayyana cewa samame tare binciken gidansa da ke House 12, Mambilla Street, Aso Drive, Abuja, ranar 19 ga Fabrairu da misalin ƙarfe 2:00 na rana, ya saba wa kundin tsarin mulki.

Haka kuma El-Rufai'i ya nemi kotu ta yi umarnin da zai tilasta wa ICPC da Sufetan Yan Sanda mayar masa da duk kayayyakin da aka kwace daga gidansa.

Bugu da ƙari, tsohon gwamnan ya nemi kotu ta umarci a biya shi Naira biliyan ɗaya a matsayin diyyar shiga gidansa ba bisa ka'ida ba, kwashe masa kaya, ɓacin rai, tozarci, damuwa, take sirri da ɓata masa suna.

Yadda ICPC ta kai samame gidan El-Rufai

A bayan, kun ji cewa jami'an hukumar ICPC sun kai samame gidan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai da ke Abuja domin gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

"Babu ruwan DSS," An ji wadanda suka cafke El Rufai bayan Ya bar hannun EFCC

Mai magana da yawun El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya bayyana cewa jami'an ICPC sun kai samame tare da gudanar da bincike a gidan tsohon gwamnan.

Lauyan Nasir El-Rufai ya bayyana cewa binciken da aka yi a gidan tsohon gwamnan ya saba wa doka da take hakkin dan adam.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262