Bayan Abin da EFCC, DSS Suka Yi Wa El Rufai, Na Kusa da Peter Obi Ya Fadi Fargabar Ubangidansa

Bayan Abin da EFCC, DSS Suka Yi Wa El Rufai, Na Kusa da Peter Obi Ya Fadi Fargabar Ubangidansa

  • Ana yada jita-jitar cewa hukumomin tsaro da na yaki da cin hanci na iya farautar tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi
  • Hadimin Peter Obi, ya fito ya yi magana kan jitar-jitar wadda ke cewa hukumomin na iya kirkirar tuhume-tuhume kan tsohon gwamnan na Anambra
  • Yunusa Tanko wanda babba ne a kungiyar Obidient ya bayyana cewa a shirye suke da duk wani irin shiri da gwamnati mai mulki za ta yi a kansu

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hadimin tsohon ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi magana kan yiwuwar fadawa komar hukumomin DSS da EFCC.

Yunusa Tanko ya yi watsi da jita-jitar da ake yi na cewa jami’an tsaro da na yaƙi da cin hanci da rashawa na iya kirkirar masa tuhume-tuhume kafin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Tsare El Rufai: Jigo a ADC ya kausasa harshe kan hukumar ICPC, ya ba ta zabi 2

Ana jita-jitar hukumomin tsaro na farautar Peter Obi
Tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

Tsohon Kakakin yaƙin neman zaɓen Obi, kuma shugaban kungiyar "Obidient Movement", Dr. Yunusa Tanko, ne ya yi watsi da wannan jita-jita a wata hira da ya yi da jaridar The Punch.

Peter Obi bai wata fargaba

Yunusa Tanko ya ce babu dalilin da zai sanya fargaba tsohon na jihar Anambra yin fargaba.

Ya jaddada cewa tsohon gwamnan na jihar Anambra ba shi da wani tarihin aikata laifi, kuma hukumar EFCC ko DSS ba su taɓa tuhumarsa da cin hanci da rashawa ba.

Ana zargin gwamnati na farautar 'yan adawa

Yunusa Tanko ya yi wannan ƙarin haske ne biyo bayan rahotanni da ke nuna cewa ana iya saka Obi da sauran manyan ’yan adawa na jam’iyyar ADC a cikin jerin waɗanda za a kama, duba da zarge-zargen tsanantawa da matsalolin da Nasir El-Rufai ke fuskanta.

Sauran manyan mutane da aka ambata cewa suna karkashin sa ido sun haɗa da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, da kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi.

Kara karanta wannan

Ramadan: Gwamna ya amince da ciyar da talakawa, ya yi wa malaman addini tagomashi

Peter Obi ya shirya in ji Tanko

Sai dai Yunusa Tanko ya dage kan cewa ba za a iya tsoratar da Obi da magoya bayansa ba.

"An daɗe da tabbatarwa ba tare da wata shakka ba cewa Peter Obi bai da kashi a gindinsa, kuma ’yan Najeriya har ma da hukumomin tsaro sun riga sun san hakan."
"Don haka, muna shirya kanmu ga matakan wuce-gona-da-iri da wannan gwamnati za ta ɗauka, domin mun san cewa wannan gwamnati ba za ta raga wa komai ba wajen yin maguɗi, tsoratarwa, da cin zarafin duk wani ɗan adawa don su tabbatar da ikonsu a kan Najeriya. Wannan mun riga mun sani."
"Saboda haka muna shirye, kuma muna jiran su, domin idan suka zaɓi bin wannan hanyar, to lallai za su amsa tambayoyin al’ummar Najeriya tambayoyi. Wannan shi ne abin da zan iya faɗa."

- Yunusa Tanko

Peter Obi ya shirya fuskantar gwamnati
Peter Gregory Obi wanda ya yi takarar shugaban kasa a 2023 Hoto: @PeterObi
Source: Twitter

Yayin da aka tambaye shi ko ya yi amanna cewa zarge-zargen cin hanci da ake yi wa ’yan adawa na da alaƙa da zaɓen 2027, Yunusa Tanko ya ce hakan a bayyane yake.

Kara karanta wannan

Akwai matsala: Tsohon kwamishinan INEC ya ba Tinubu shawara kan dokar zabe

"Haka ne mana. Batun zaɓen 2027 ne kawai, ba wani abu ba. Don haka, kamar yadda na faɗa a baya, muna jiran su kan duk wani mataki da suke son ɗauka."

- Yunusa Tanko

Gobarar Kano ta sa Obi ya je jaje

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, ya je ziyarar jaje a jihar Kano.

Peter Obi ya kai ziyarar ne zuwa jihar Kano domin jajantawa 'yan kasuwar da gobara ta ritsa da su a kasuwar Singer.

​A yayin ziyarar jaje da ya kai kasuwar, Peter Obi ya zagaya sassa daban-daban tare da abokan tafiyarsa, inda ya gana kai tsaye da ’yan kasuwar da abin ya shafa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng