Ramadan: Masu Kankara za Su Iya Kwantai, za a Yi Kwanaki ana Hazo da Ruwa

Ramadan: Masu Kankara za Su Iya Kwantai, za a Yi Kwanaki ana Hazo da Ruwa

  • Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta sanar da yadda yanayi zai kasance a kwanaki uku masu zuwa a jihohi daban-daban na kasar nan
  • Ta bayyana yadda za a shafe kwanakin ana hazo, wasu jihohi kuma za su samu ruwan sama a cikin kwanaki masu zuwa a fadin tarayyar Najeriya
  • Hakan na zuwa ne yayin da al'ummar Musulmi ke cigaba da azumin Ramadan, inda rashin rana ke hana masu sayar da kankara ciniki sosai a jihohi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta yi hasashen hazo da gajimare daga yau Litinin zuwa Laraba a faɗin ƙasar nan.

Hasashen yanayin da NiMet ta fitar a ranar Lahadi, 22 ga Janairun 2026 a Abuja ya nuna cewa za a samu hazo madaidaici a Arewa daga yau Litinin.

Kara karanta wannan

Yadda zabe ke gudana a Kano da wasu sassan Najeriya a yau Asabar

Yadda ake hazo a wani yankin Najeriya
Wajen da ake hazo a hagu, mai sayar da kankara a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Legit Hausa ta tattaro bayanan da NiMET ta yi game da hasashen yanayi ne a wani sako da hukumar ta wallafa a shafinta na X.

Jihohin da za a yi hazo da ruwa

A cewar hukumar NiMet, wasu jihohi kamar Borno da Yobe za su fuskanci matsakaicin hazo, inda hango wurare daga nesa zai yi wahala.

“A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran hazo matsakaici a duk faɗin yankin."
“A yankin Kudu, ana sa ran yanayi mai gajimare tare da hasken rana a wasu lokuta, tare da yiwuwar tsawa da safe a wasu sassan jihohin Cross River da Akwa Ibom."

NiMET ta ce ana sa ran tsawa tare da ruwan sama kaɗan a wasu sassan jihohin Ondo, Ogun, Lagos, Edo, Bayelsa, Cross River, Rivers, Delta da Akwa Ibom.

Kara karanta wannan

Ramadan 2026: Lokutan sahur da buda baki a Kano da wasu jihohin Najeriya

Hasashen ranar Talata a Najeriya

A ranar Talata, 24 ga watan Fabrairun 2026, hukumar hasashen yanayi ta NiMet yi hasashen hazo a yankin Arewa ta Tsakiya.

Ta bayyana cewa za a samu yanayi mai gajimare tare da hasken rana a wasu lokuta a yankin Kudu, tare da yiwuwar tsawa da safe a wasu sassan jihohin Akwa Ibom da Cross River.

Ta yi hasashen tsawa tare da ruwan sama kaɗan a wasu sassan jihohin Lagos, Oyo, Ondo, Ogun, Edo, Bayelsa, Cross River, Rivers, Delta da Akwa Ibom daga baya a ranar.

Babur na tafiya a cikin hazo
Mutane da abubuwan hawa na tafiya a cikin hazo. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Za a yi hazo a Arewa ranar Laraba

Rahoton jaridar Vanguard ya nuna cewa NiMET ta ce a Arewa, ana sa ran hazo mai yawa a duk faɗin yankin a ranar Laraba, 25 ga Janairun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun yi wa 'yan APC jina jina a wajen taro, wasu sun rasu

“A yankin Arewa ta Tsakiya, ana sa ran hazo mai yawa a duk faɗin yankin."

Da alama masu sayar da kankara a cikin azumi ba za su yi ciniki sosai ba a garuruwan Arewacin Najeriya idan hasashen hukumar NiMeT ya tabbata.

Adadin masu rajistar zabe a jihohi

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zabe ta fitar da adadin 'yan Najeriya da suka yi rajistar katin zabe a dukkan jihohin kasar nan.

Bayan samun mutane sama da miliyan daya da suka yi rajistar mallakar katin zabe, INEC ta bayyana cewa jihar Jigawa ce ta zo ta daya.

Jihohin Sokoto, Legas, Kano da Kaduna sun taka rawar gani, kuma INEC ta bayyana cewa 'yan Najeriya za su iya cigaba da rajistar har yanzu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng