Kai Ruwa Rana da Ake Yi Tsakanin El-Rufai da Gwamnatin APC, abin da Muka Sani
Abuja - Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, Malam Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan Kaduna (2015-2023) yana tsare a hannun hukumar yaki da rashawa ta ICPC.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
A cikin wata sanarwa da ICPC ta fitar a ranar 19 ga Fabrairu, 2026, hukumar ta ce El-Rufai na tsare a hannunta ne daga ranar 18 ga Fabrairu, 2026.

Source: Twitter
Takun sakar El-Rufai da gwamnatin APC
A sanarwar da ICPC ta wallafa a shafinta na X, dauke da sa hannun shugaban sashen hulda da jama'a da watsa labarai, John Okor, Odey, hukumar ta ce:
"Malam Nasiru El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna yana tsare a hannunmu ya zuwa lokacin tashi aiki a yau, Laraba 18 ga Fabrairu, 2026... bisa wani bincike da ake yi."
A cikin wannan rahoto, Legit Hausa ta yi nazari kan kai ruwa rana da ake yi tsakanin El-Rufai da gwamnatin APC, karkashin Shugaba Bola Tinubu.
1. Alakar El-Rufai da APC da zaben 2023

Source: Facebook
Malam Nasir El-Rufai ya kasance daya daga cikin mambobin da suka kafa jam’iyyar APC kuma babban jigo ne a cikinta.
Lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023, ya taka rawar gani sosai wajen tattara goyon baya ga dan takarar lokacin, Bola Tinubu, musamman a yankin Arewa.
A wata hira da BBC Hausa ta wallafa a shafinta na intanet a ranar 13 ga watan Fabrairu, 2026, El-Rufai ya fito fili ya bayyana cewa ba shi da wata alaka ta kashin kansa da Shugaba Tinubu.
Kuma ya ce ya goyi bayan takarar Tinubu ne kawai saboda haduwarsu karkashin jam’iyyar APC, inda ya bambanta hakan da kusancin da ke tsakaninsa da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari.
Ya bayyana cewa:
“Ni Tinubu ba mu taba wani sha'ani da shi ba, ni Tinubu ba mutumina ba ne, ba abokina ba ne, ba mu yi siyasa tare ba, a APC muka hadu."
'Yar alakar da ke tsakaninsu ta fara tabarbarewa ne bayan zaben 2023. Shugaba Tinubu ya nada El-Rufai a matsayin minista, sai dai majalisar dattawa ta ki tabbatar da shi a watan Oktoban 2023.
Daga nan ne El-Rufai ya rikide zuwa mai sukar manufofin gwamnatin Tinubu, inda ya fara sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP kafin ya koma jam’iyyar ADC ta hadakar 'yan adawa.
Wannan sauyin sheka ya sanya shi a sahun gaba wajen adawa, wanda hakan ya kara fadada barakar siyasa dake tsakaninsa da jam’iyyar APC mai mulki.
2. Yunkurin kama El-Rufai a filin jirgi

Source: Facebook
Takun saka ya fara karfi ne a ranar 12 ga watan Fabrairu, 2026, inda jami’an tsaro sun yi yunkurin cafke El-Rufai bayan saukarsa a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe dake Abuja, daga birnin Cairo.
Kamar yadda hadimin sa kan yada labarai, Muyiwa Adekeye, da lauyansa, Ubong Akpan suka bayyana, jami’an sun tunkari tsohon gwamnan ne ba tare da nuna masa takardar sammaci ko gayyata ta hukuma ba.
El-Rufai ya ki amincewa da bukatar jami’an, lamarin da ya janyo hatsaniya, inda Legit Hausa ta rahoto cewa fasinjoji da sauran jama’ar da ke kusa suka taru suka hana a tafi da shi.
A yayin wannan dambarwar, jami’an sun kwace fasfo din tsohon gwamnan na fita kasashen waje daga hannun daya daga cikin hadimansa.
3. Batun nadar kiran wayar Ribadu

Source: Twitter
Bayan abin da ya faru a filin jirgin sama, El-Rufai ya bayyana a shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV a ranar 13 ga watan Fabrairu, 2026.
A cikin wannan hira da aka yi kai-tsaye, ya sanar da aniyarsa ta mika kansa ga EFCC da kansa a ranar Litinin, 16 ga watan Fabrairu, domin amsa tuhume-tuhumen da ake masa na cin hanci da rashawa.
Haka kuma, ya fadi wasu zarge-zarge masu tada hankali game da Mai Ba Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu.
Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ya samu damar sauraron (ko kuma an sanar da shi) wata tattaunawar waya da aka nada, inda aka ji Ribadu yana bai wa jami'an tsaro umarnin su kama shi.
Ya danganta wannan umarni kai-tsaye da yunkurin da aka yi na kama shi a filin jirgin sama ranar 12 ga watan Fabrairu, inda ya ce:
"Nuhu Ribadu ne ya yi kiran sannan ya ba da umarnin lallai sai an tsare ni... Wani ne ya nada muryarsa a waya sannan ya gaya mini."
Ya bayyana cewa gwamnati na tunanin ita kadai ce ke da ikon saurare ko nada kiran waya, amma ya jaddada cewa su ma 'yan adawa suna da irin wannan fasahar.
4. Zargin shigo da Thallium da martanin Ribadu
A ranar 30 ga Fabrairu, 2026, Malam Nasir El-Rufai ya aika wa Nuhu Ribadu wasikar neman bahasi a hukumance game da rahoton cewa ofishinsa ya sayo kimanin kilogiram 10 na sinadarin thallium sulphate.
El-Rufai ya wallafa wasikar a shafinsa na X, inda ya bayyana binciken nasa a matsayin wani abu da ya shafi "tsaron jama’a, bin ka’idojin dimokuradiyya... da kuma tabbatar da amana."
A wasikar, ya yi tambaya game da manufar sayo sinadarin, inda za a adana shi, da kuma ko an sanar da hukumomi irin su NAFDAC da NCDC.
Ofishin Ribadu ya mayar da martani ta wata wasika mai kwanan wata 13 ga watan Fabrairu, 2026 wadda Birgediya Janar O.M. Adesuyi ya sanya wa hannu, in ji rahoton Premium Times.
NSA ya ya musanta sayo ko shigo da wannan sinadari yayin da ya mika maganar ga hukumar DSS domin ci gaba da bincike, tare da fadawa El-Rufai ya shirya gabatar da hujjojinsa ga hukumar.
5. El-Rufai ya kai kansa EFCC

Source: Twitter
A ranar 16 ga watan Fabrairu, 2026, wadda ta yi daidai da ranar cikarsa shekaru 66 da haihuwa, Malam Nasir El-Rufai ya mika kansa ga hukumar EFCC a hedikwatarta dake Abuja.
An tsare shi tare da yi masa tambayoyi kan zargin bacewar kimanin N423bn na jihar Kaduna a lokacin da yake gwamna, kamar yadda yake kunshe cikin rahoton kwamitin bincike na musamman na majalisar dokokin jihar Kaduna na shekarar 2024.
Jaridar Guardian, ta rahoto cewa tsohon gwamnan na Kaduna ya shafe kwanaki a tsare a hannun EFCC (daga Litinin zuwa yammacin Laraba).
6. DSS ta yi karar El-Rufai
Ana cikin hakan, sai hukumar DSS ta shigar da kara kan tuhume tuhume uku a kan El-Rufai a gaban Babbar Kotun Tarayya dake Abuja, bisa zargin tafka laifukan yanar gizo da kuma barazana ga tsaron kasa.
Tuhume tuhumen, karkashin lambar shigar da kara ta FHC/ABJ/CR/99/2026, sun zargi El-Rufai da yin kutse ta haramtacciyar hanya a tattaunawar wayar Ribadu, da kuma sanin mutumin da ya yi wannan kutse tare da yin harka da shi ba tare da ya kai rahoto ga hukumomi ba.
Wadannan laifuka sun saba wa dokar hana aikata laifuka ta yanar gizo, 2024, da kuma dokar sadarwa ta Najeriya, 2003.
An tsara cewa za a gurfanar da shi a gaban kotun ranar 25 ga watan Fabrairu, 2026, kamar yadda jaridar The Cable ta rahoto.
7. Belin EFCC da shiga hannun ICPC
A ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairu, 2026, da misalin karfe 8 na dare, hukumar EFCC ta amince ta ba Malam Nasir El-Rufai beli bayan kwanaki uku ana yi masa tambayoyi.
Sai dai, yayin da yake shirin barin harabar ofishin EFCC, wasu dakaru dauke da makamai suka sake cafke shi nan take, in ji rahoton Legit Hausa.
Rahotannin farko da shaidun gani da ido sun yi nuni da cewa jami'an DSS ne suka kama shi, amma daga baya hukumar ICPC ta bayyana cewa jami’anta ne suka kama shi.
8. Tsare shi da samamen gidansa na Abuja

Source: Twitter
Hukumar ICPC ta tabbatar da cewa El-Rufai yana hannunsu a ranar 19 ga watan Fabrairu, inda ta bayyana cewa zai ci gaba da zama a can domin "bincike dake gudana" dangane da lokacin mulkinsa na gwamna.
Kwanaki biyu da suka gabata ne Legit Hausa ta rahoto cewa, jami’an hukumar ta ICPC sun kai samame gidan El-Rufai dake unguwar Aso Drive a Abuja.
Hadiminsa kan yada labarai, Muyiwa Adekeye, ne ya sanar da gudanar da binciken a shafinsa na X, inda ya tabbatar da cewa jami’an sun kai samame don nema wasu abubuwa a gidan.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an kai samamen ne a daidai lokacin da El-Rufai yake riga yana tsare a hannun hukumar ta ICPC.
9. Martanin lauyoyin El-Rufai
Babban lauyan El-Rufai, Ubong Akpan, ya yi Allah-wadai da samamen da ICPC ta kai gidansa, inda ya bayyana shi a matsayin "haramtaccen mataki kuma take dokokin shari'a da hakkokin bil'adama."

Kara karanta wannan
Babbar magana: Ganduje ya yi magana kan batan Dadiyata, ya maida martani ga El Rufai
Shi da tawagar sa ta lauyoyi sun lashi takobin kalubalantar tsare shi da kuma binciken da aka yi ta hanyar amfani da hanyoyin da suka dace a kotu.
Jaridar Vanguard ta nakalto kalaman Akpan, inda ya bayyana cewa tawagar lauyoyin tana kokarin shigar da bukatar neman beli da kuma karar neman kariya ga hakkokin dan adam.
Jiga-jigan jam’iyyar ADC sun goyi bayan kiran da ake yi na cewa lallai a gurfanar da El-Rufai a gaban kotu ko kuma a sake shi nan take, inda suka bayyana jerin kame-kamen da ake yi masa a matsayin "farautar siyasa."
10. Abubuwan da ka iya faruwa nan gaba
A mako mai zuwa, hukumar DSS za ta gurfanar da Malam Nasir El-Rufai, kan tuhume-tuhumen laifukan yanar gizo.
Sannan, a makonni masu zuwa, hukumomin EFCC da ICPC na iya gurfanar da tsohon gwamnan bayan kammala bincike kan kudaden jihar Kaduna.
Ya zuwa yau 22 ga watan Fabrairu, 2026, El-Rufai yana ci gaba da zama a hannun hukumar ICPC ba tare da tabbas kan ranar da za a sake shi ba.
Jigon ADC ya kausasa harshe kan El-Rufai
A wani labari, mun ruwaito cewa, jigo a jam’iyyar ADC, Usman Austin, ya mika bukatarsa ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC kan Nasir El-Rufai.
Usman Austin ya bukaci ICPC da ta gaggauta gurfanar da tsohon gwamnan na Kaduna, a gaban kotu ko kuma ta sake shi ya kama hanyar gaban shi.
Ya jaddada cewa idan har akwai zarge-zarge a kan El-Rufai, to kamata ya yi a kai su gaban kotu, yana mai nuna mahimmancin bin tabbatattun matakai na shari’a.
Asali: Legit.ng







