Mun Kirga Gawawwaki 208 da 'Yan Ta'adda Suka Kashe a Harin Kwara In ji Mazaunin Woro
- A harin da wasu ‘yan ta’adda suka kai a kauyukan Woro da Nuku a karamar hukumar Kaiama, an rasa mutane masu yawan gaske
- Legit Hausa ta yi kokarin jin ta bakin mutanen Kwara da aka yi wa wannan barna, kuma sun iya bada labarin abin da ya faru a ranar
- Ganin irin ta’adin da aka yi masu a ranar 3 ga watan Fubrairu 2026, sun kawo shawarwarin yadda za a tabbatar da tsaro a kauyukan
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
M. Malumfashi ya shafe shekaru kimanin 10 ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kwara – A farkon watan Fubrairu 2026, aka samu wasu miyagun ‘yan ta’adda da suka auka wa garuruwan Woro da Nuku a garin Kaima, jihar Kwara.
Wasu rahotanni sun bayyana cewa adadin mutanen da aka hallaka a garuruwan na Arewacin Kwara sun haura 200 ba tare da agajin jami’an tsaro ba.

Source: Getty Images
Jaridar Legit Hausa ta yi hira ta musamman da wasu daga cikin mutanen garin Kaiama a jihar Kwara, inda ‘yan ta’adda suka kai wa mummunan hari.
Yadda ‘yan ta’adda suka rutsa kauyukan Kaiama
Kwamred Muhammad Bashir mazaunin garin Woro ne, ya shaida mana cewa tun kusan karfe 5:00 na yamma aka kawo hari har zuwa cikin tsakar dare.
“Ya fara ne kusan 5:00, an kammala sallar la’asar sai daidai karfe 4:50 haka suka shigo, suna shigo wa sai suka fara rarraba juna ta ko ina a kauyen…
“Bayan karfe 5:00 na yamma ta wuce kenan, sai wasu suka wuce gidan Sarkin (Woro), suka fara harbe mutanen da ke kan titi.
“Shi Sarkin ba ya gida, amma yana kusa da kauyen, ya samu ya tsere sai ya sanar da jami’an tsaro cewa ‘yan ta’adda sun shigo garin shi suna kashe-kashe.
"Haka suka yi ta yi har zuwa 2:00 na dare kuma babu wani jami’in tsaro da ya zo”
- Kwamred Muhammad Bashir

Source: Getty Images
Mutane nawa aka kashe a harin Kaiama
Da Legit Hausa ta tambayi Muhammad Bashir ko mutane nawa aka hallaka, ya ce sun haura 200.
"Hakika wadanda aka yi jana’izarsu a asalin Woro domin akwai wadanda ba su cikin kauyen, wasu kuma ba a iya dauko gawarsu ba, an yi jana’izarsu a can. Cikin garin da aka yi jana’iza, mutane 208 muka kirga da aka birne.
“Kuma sun sa bam sun yi barna, sun kona shaguna, sun kona a gidan sarki – sun kashe yaransa biyu kuma sun wuce da matarsa ta biyu da wata yarinya da kuma jaririya da ake shayarwa."
- Kwamred Muhammad Bashir
Adadin bayin Allah da aka dauke daga kauyukan
Majiyarmu ta tabbatar mana da abin da aka rahoto na cewa mutane 175 na hannun 'yan ta'adda a yanzu.
"Sannan sun kwashe mata da yara sun tafi da su, mu a lissafinmu (domin ranar ana biki don haka mutane sun zo daga Kainji, Vera da Nuku), mun kirga mutane 154, ashe sun fi haka
"Ranar da suka fitar da bidiyo sun ce 176, idan sun ce haka ne ba karya ba ne domin akwai baki da ba mu lissafa ba."
- Kwamred Bashir Muhammad
Wannan mutumi ‘dan asalin garin Woro ya shaida mana cewa yanzu dai an baza sojoji a garin Maje kafin a iya shiga kauyukan da aka yi ta’adi.
Sai dai duk da haka ya shaida mana cewa an yi yunkurin kai wani harin a Kudancin jihar Kwara sannan ana yi wa mutanen yankin Baruren barazana.

Source: Getty Images
Martanin 'yan sanda kan abin da ya faru
Da ake tattaunawa da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar Kwara, Adetoun Ejire-Adeyemi, ya bayyana fargabar yiwuwar lamarin ya fi karfin jami'an da ke yankin.
A kalamanta yayin amsa tambayoyi daga dan jaridar Channels Tv:
“To, a lokacin dai, abin da zan iya cewa shi ne wataƙila abin ya fi ƙarfinsu ne.
"Muna kuma da alakar aiki da ’yan sa-kai na yankin, sannan kuma abin da ya fi muhimmanci, jami’an da ke gadin daji na ƙasa ma suna cikin wannan al’umma.
"Don haka muna ganin abin ya fi ƙarfinsu ne a wancan lokacin, kuma kafin su samu damar dawowa, saboda nisan da ke tsakanin garin da Hedikwatar ’Yan Sanda ta Sashe wadda take a Kaiama — ban san tsawon lokacin da hakan ya ɗauka ba — amma dai tazara ce mai nisa. Duk da haka, tabbas sun samu ƙarin jami’ai a matsayin tallafi.”
Miyagun ƴan bindiga sun ƙone fadar Sarkin Woro
Tun a farkon watan nan aka zo da labari cewa ana fargabar 'yan bindiga sun hallaka fiye da mutane barkatai a jihar Kwara a wani mugun hari da aka kai.
A sabon harin da suka kai garin Woro, 'yan ta'adda sun cinnawa fadar sarki da gidajen mutane wuta kamar yadda wani dan majalisar yankin Kaiama ya sanar.
'Yan majalisar yankin sun bukaci gwamnatin tarayya ta tura dakarun soji na musamman domin kakkabe yan bindiga dake addabar Kaiama a Arewacin Kwara.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng
Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng



