‘Ban Yafe ba’: Sakon Malamin Musulunci ga Tinubu da Ya Nemi Yafiya a Ramadan
- Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya soki rokon afuwar da Bola Ahmed Tinubu ya yi a Ramadan, yana mai ba shi shawara
- Malamin ya bukaci malamai su bayyana wa shugaban kasa sharudan tuba, yana nuna cewa kalaman neman gafara ba su isa ba
- Ya ce shi dai bai yafe ba, yana ganin idan shugaba ya amince da kuskure to ya kamata ya sauka domin a ba matasa dama
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kaduna - Babban malamin Musulunci a jihar Kaduna, Sheikh Ibrahm Aliyu Kaduna ya nuna damuwa game da halin da kasa ke ciki.
Malamin ya nuna takaicin yadda Bola Tinubu ya fito a watan Ramadan yana neman yan Najeriya su yafe masa idan ya masu laifi.

Source: Facebook
Malamin ya bayyana haka ne yayin hudubar sallar Juma'a da ya gudanar wanda ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook.
Malami ya soki Tinubu da ya nemi yafiya
A cikin bidiyon, malamin ya ce Tinubu ya fito yana neman yafiya inda ya caccake shi cewa sai dai idan har zai yi tuban gaskiya.
Sheikh Ibrahim Aliyu ya bukaci malaman Musulunci su karanta masa sharudan tuba domin tabbatar da tuba ta tsakani da Allah.
"Shugaban kasa ya fito ya ce idan ya yi muku laifi ku yafe masa, mutum yana neman yafiya ne idan ya tuba.
"Allah ya sa malamai za su karanta masa sharudan tuba, shugaban kasa a karanta maka sharudan tuba, ba ka fitowa ka ce mu yafe maka a lokacin da ka kara kudin mai.
"Ba ka fitowa ka ce mu yafe maka bayan kakaba mana haraji, ba ka fitowa ka ce mu yafe maka ana fama da rashin magani a asibiti."

Source: Facebook
Shawarar da malamin ya ba Tinubu
Malamin ya bukaci shugaban da ya sauka daga kan mulki idan har ya tabbatar da abin da yake yi ba daidai ba ne.
Ya bayyana cewa shi kam bai yafe masa ba saboda yana ci gaba da zaluntar shi har yanzu, ya ce wata kila sauran al'umma za su yafe masa.
"Mu abin da muke fada wa shugaban kasa idan ka gamsu ba daidai kake ba, ka sauka, kawai ka koma Lagos ka zauna a nemi matashi mai kwari.
"Don haka shugaban kasa ya ce a yafe masa, ni dai ban yafe masa ba, kila ku kun yafe amma ni ban yafe ba, tun da yana ji yana gani yana zalunta ta.
"Bai yiwuwa mutum ya matse ni ina ihu bai sake ni ba yana ka yafe min, a'a ban yafe ba, gaskiyar magana kenan, ahh ba mu yafe masa ba."
- Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna
Shehi ya yiwa Tinubu raddi kan neman yafiya
Mun ba ku labarin cewa malamin Musuluncin nan, Dr Bashir Aliyu Umar ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu martani game da rokon da ya yi a yafe masa.
Malamin ya bayyana cewa babban abin da ya kamata Shugaban kasa ya mayar da hankali a kansa shi ne sauke nauyin da ke kansa.
A wajen bude tafsirin Ramadan 2026 a fadar shugaban kasa ne Bola Ahmed Tinubu ya roki 'yan Najeriya su yafe masa idan ya masu laifi.
Asali: Legit.ng

