Abin Ya Yi Muni: 'Yan Bindiga Sun Sake Tafka Ta'addanci Ana cikin Azumi a Zamfara
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani a jihar Zamfara cikin azumi
- Tsagerun 'yan bindiga sun hallaka bayin Allah bayan sun bude musu wuta a harin da suka kai a karamar hukumar Tsafe
- Hakazalika, 'yan bindiga sun kona wata motar yaki ta dakarun sojojin Najeriya bayan sun dasa mata nakiya a kan hanya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - 'Yan bindiga sun kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba yayin wani hari da suka kai a jihar Zamfara.
An tabbatar da mutuwar mutane 11 biyo bayan wani hari da 'yan bindiga suka kai a kauyen Ware da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Source: Facebook
Ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazaɓar Tsafe ta Yamma, Amiru Ahmad Keta, ne ya tabbatar da hakan ga tashar Channels tv a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026.
Yadda 'yan bindiga suka kai hari a Zamfara
Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka kutsa cikin ƙauyen tare da buɗe wa mazauna garin wuta.
'Dan majalisar ya bayyana cewa zuwa yanzu an gano gawarwaki 11 kuma an kwashe su zuwa ƙauyen Keta domin birne su.
Ba a san yawan mutanen da suka rasu ba
A cewarsa, mazauna garin da suka yi ƙoƙarin kwashe ragowar gawarwakin, maharan sun kore su, wanda hakan ya sanya ba a san takamaiman yawan mutanen da aka kashe.
Amiru Ahmad Keta ya ce an kwashe gawarwakin mutane 11 da aka gano a cikin baro zuwa Keta domin yi masu jana'iza.
Ya bayyana cewa maharan sun kori masu ƙoƙarin kwashe gawarwakin, kuma har zuwa lokacin hada wannan rahoton, babu jami'an tsaro ko ɗaya da suka sami damar shiga kauyen Ware tun ranar Alhamis.
'Yan bindiga sun kona motar sojoji
Ɗan majalisar ya kuma bayyana cewa wata motar yaƙi mai sulke ta sojojin Najeriya ta lalace bayan ta taka nakiya da aka dasa a kan hanyar Keta zuwa Danjibga a ƙaramar hukumar Tsafe.

Source: Original
Rahotanni sun nuna cewa dakarun sojojin suna rakiyar motocin fararen hula ne ta wannan hanya mai haɗari lokacin da fashewar ta faru.
Bayan fashewar, an ce sojojin sun janye daga wurin, inda maharan suka dawo tare da cinna wa motar da ta lalace wuta.
'Yan bindiga sun kashe mutane 50 a Zamfara
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kashe mutane da dama a wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Zamfara.
Tsagerun 'yan bindigan sun kashe aƙalla mutane 50 tare da sace mata da yara bayan sun farmaki ƙauyen Tungan Dutse a jihar Zamfara.
Ɗan majalisar dokokin jihar Zamfara mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta Kudu, Hamisi A. Faru, ya bayyana cewa maharan sun ƙona gidaje tare da harbe duk wani mazaunin ƙauyen da ya yi ƙoƙarin tsere musu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

