Tsare El Rufai: Jigo a ADC Ya Kausasa Harshe kan Hukumar ICPC, Ya Ba Ta Zabi 2

Tsare El Rufai: Jigo a ADC Ya Kausasa Harshe kan Hukumar ICPC, Ya Ba Ta Zabi 2

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai na tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC har yanzu
  • Wani kusa a jam'iyyar ADC, Usman Austin, ya fito ya yi magana kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan da ICPC ta ke yi
  • Ya bukaci ICPC ta yi koyi da hukumar DSS wadda ta kai karar El-Rufai gaban kotu kan wasu zarge-zarge da take yi masa

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar ADC, Usman Austin, ya mika bukatarsa ga hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC kan Nasir El-Rufai.

Usman Austin ya bukaci ICPC da ta gaggauta gurfanar da tsohon gwamnan na Kaduna, a gaban kotu ko kuma ta sake shi ya kama hanyar gaban shi.

Kara karanta wannan

Bayan kanannaɗe El Rufai, ana zargin gwamnatin Tinubu ta shirya cafke tsohon gwamna

Jigo a ADC ya bukaci ICPC ta saki El-Rufai
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da ya raba ba ta a ranar Asabar, 21 ga watan Fabrairun 2026.

Jigon ADC ya damu kan tsare Nasir El-Rufai

Usman Austin ya nuna damuwarsa kan ci gaba da tsare El-Rufai da ake yi, inda ya yi kira ga hukumar da ta bi tsarin doka da ya dace.

Ya kafa hujja da salon da hukumar DSS ta bi kwanan nan, inda ya ce su sun zaɓi bin hanyar kotu wajen tafiyar da makamancin wannan lamari.

“Matakin da DSS ta ɗauka na tunkarar kotu maimakon yin amfani da damar tsare mutum yadda suka ga dama, abu ne na wayewa da kuma bin tsarin dimokuradiyya.”
“DSS ta nuna cewa hanya mafi dace wajen tafiyar da irin waɗannan al’amura ita ce barin kotu ta yanke hukunci ta hanyar sauraron hujjoji daga masu ƙara da kuma wanda ake ƙara."

Kara karanta wannan

Tsugunne ba ta kare ba; El Rufai na tsare hannun ICPC, wata hukuma ta sa lokacin kai shi kotu

- Usman Austin

Ya bukaci a kai El-Rufai kotu

Usman Austin ya jaddada cewa idan har akwai zarge-zarge a kan El-Rufai, to kamata ya yi a kai su gaban kotu, yana mai nuna mahimmancin bin tabbatattun matakai na shari’a.

Usman Austin ya kuma lura cewa El-Rufai ya riga ya amsa gayyatar hukumar EFCC, inda ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin wanda yake ba da haɗin kai ga hukumomin bincike.

“Har yanzu EFCC ba ta yi bayanin yadda aka yi ya tsinci kansa a wannan tsarewar ba, ko an miƙa Malam El-Rufai ne ga ICPC a hukumance, ko kuma an sake kama shi ne bayan an ba shi beli. Wannan rashin tabbas yana raunana tsarin bin doka da oda."

- Usman Austin

Jigo a ADC na son ICPC ta saki El-Rufai
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai a dakin karatunsa Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

An bar mutane a duhu kan dalilin tsare El-Rufai

Usman Austin ya yi kira da a fito fili a bayyana dalilan da suka sa ake tsare da shi, tare da jaddada buƙatar gaskiya a cikin irin waɗannan al’amura.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Ya nanata cewa babban muradin ƙasashen duniya da suka ci gaba shi ne kare haƙƙin wanda ba a tabbatar da laifinsa ba.

“Kama mutum kafin a fara bincike babban keta haƙƙin sa ne na samun adalci. Ka da hukumomin yaƙi da cin hanci su yarda su zama makamin danniya idan har suna son ƙarfafa dimokuradiyyar Najeriya."
“Dole ne ICPC ta kiyaye ka'idoji. Idan akwai ƙara a kan El-Rufai, a je kotu a gabatar da hujjoji. Idan kuma babu, to dole ne a sake shi cikin gaggawa."

- Usman Austin

DSS za ta gurfanar da El-Rufai gaban kotu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar DSS ta shirya gufanar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmad El-Rufai a gaban kotu.

Hukumar DSS za ta gurfanar da El-Rufai ne kan wasu tuhume-tuhume guda uku da suka shafi mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro.

Daga cikin tuhumar da DSS ke yi wa babban 'dan hamayyar har da zargin yin kutse tare da sauraron wayar Malam Nuhu Ribadu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng