Tinubu Ya Fusata kan Kashe Kashe a Taron APC, Ya Dauki Kwakkwaran Mataki

Tinubu Ya Fusata kan Kashe Kashe a Taron APC, Ya Dauki Kwakkwaran Mataki

  • An samu hargitsi wanda ya jawo asarar rayuka yayin gudanar da zaben shugabannin APC a matakin mazabu a jihar Ondo
  • Rikicin dai ya jawo an raunata mutane da dama yayin da wasu ke kwance a asibiti suna jinya saboda girman raunukan da suka samu
  • Rikicin ya harzuka shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, inda ya dauki matakin kiran gwamnan jihar domin ya ba shi bayani kan abin da ya faru

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Alamu sun bayyana a daren jiya cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa, a Abuja.

An yi ganawar ne sakamakon kashe-kashen da suka biyo bayan gudanar da zaɓen jam’iyyar APC a matakin mazabu da aka yi ranar Laraba.

Shugaba Tinubu ya kira gwamnan jihar Ondo zuwa Villa
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu da gwamnan jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Hon. Lucky Aiyedatiwa
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce wata majiya daga gidan gwamnati da ke Akure, babban birnin jihar, ta ce an gayyaci gwamnan ne cikin gaggawa a daren ranar Alhamis biyo bayan wasu rahotannin tsaro da Shugaba Tinubu ya samu.

Kara karanta wannan

Sabon rikici: Gwamna Alia da sakataren gwamnatin Tinubu sun raba APC gida 2

Tinubu ya kira gwamna kan rikicin APC

Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya gana da shugaban ƙasar a daren ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairun 2026 a fadar shugaban kasa ta Aso Rock Villa.

Jaridar Leadership ta kawo cewa wata majiya ta kusa da jam’iyyar APC a jihar ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya yi matuƙar fusata da rahotannin kashe-kashen.

“Muna tsaka da shirin taron cikar gwamna shekara guda a kan mulki, sai muka samu labarin cewa gwamnan ba zai samu damar kasancewa ba a ranar Alhamis.".
"Mun fahimci cewa shugaban ƙasa ya yi fushi sosai kan kashe-kashen kuma yana son jin ba’asi daga bakin gwamnan kan abin da ya faru, ganin cewa ma jihar ba ta da wata jam'iyyar adawa mai ƙarfi da za ta tayar da irin wannan tarzoma.”

- Wata majiya

An yi rikici a taron APC a Ondo

Rikicin dai ya faru ne yayin zaɓe a matakin mazaɓu na APC a ranar Laraba, inda aka kashe mutane biyu tare da raunata wasu da dama a ƙaramar hukumar Idanre.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba Aminu Ado Bayero jagorancin ciyar da talakawa a Ramadan

Wannan tashin hankali ya faru ne sa'o'i 24 kacal bayan da wasu 'yan daba suka kai hari sakatariyar APC da ke Akure, inda suka tarwatsa taron masu ruwa da tsaki wanda shugaban jam'iyyar na jiha, Ade Adetimehin, ke jagoranta.

Gwamna Aiyedatiwa ya gana da Shugaba Tinubu
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa Hoto: Hon Lucky Aiyedatiwa
Source: Facebook

An ci zarafin Adetimehin, yayin da aƙalla mutane 15 suka samu munanan raunuka.

Tsohon ɗan majalisar dokokin jihar, Success Torukerijoh da tsohon shugaban karamar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo/Odigbo, Dayp Akinsuroju, na can ana jinyarsu a wani asibiti da ba a bayyana ba.

Dayo Akinsuroju: Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ile-Oluji/Okeigbo/Odigbo. Waɗannan jiga-jigai suna can ana jinyarsu a wasu asibitoci da ba a bayyana sunayensu ba a babban birnin jihar sakamakon harin da aka kai musu.

Gwamna Aiyedatiwa ya fusata kan kashe kashe

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ondo, Lucky Orimisan Aiyedatiwa, ya hrzuka kan rigingimun da aka yi a tarurrukan jam'iyyar APC.

Gwamna Aiyedatiwa ya ba hukumomin tsaro umarnin su gano tare da gurfanar da wadanda ke da alhakin rikicin da ya tarwatsa taron mazabu na jam’iyyar.

Hakazalika, ya umurci jami’an tsaro da su dawo da zaman lafiya tare da gudanar da bincike mai zurfi domin hukunta masu hannu a rikicin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng