Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutane 50, Sun Sace Mata da Yara a Zamfara
- Yan bindiga sun kashe mutum 50, sun sace mata da yara a kauyen Tungan Dutse dake Zamfara bayan sun kwashe sa'o'i suna barna
- Mazauna garin sun bayyana cewa jami'an tsaro sun yi watsi da gargadin da suka bayar bayan sun ga mahara sama da 150 kafin harin
- Harin ya faru ne kwana daya bayan ministan tsaro ya kaddamar da motocin yaki da jirage mara matuka domin yaki da ta'addanci a jihar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Zamfara - Wasu miyagun 'yan ta'adda sun kashe aƙalla mutane 50 tare da sace mata da yara bayan sun farmaki ƙauyen Tungan Dutse a jihar Zamfara.
Wani ɗan majalisar jiha, Hamisu A. Faru, ya tabbatar da cewa maharan sun shafe sa'o'i kusan 11 suna cin karensu babu babbaka a kauyen.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun kashe mutane a Zamfara
Hamisu Faru, ya shaidawa kamfanin labarai na Reuters cewa maharan sun afka garin ne da misalin ƙarfe 5:00 na yammacin Alhamis, inda suka ci gaba da yin barna har zuwa ranar Juma'a.
Ɗan majalisar, mai wakiltar mazabar Bukkuyum ta Kudu ya bayyana cewa maharan sun ƙona gidaje tare da harbe duk wani mazaunin ƙauyen da ya yi ƙoƙarin tsere masu.
"Sun rika shiga daga wannan kauye zuwa wancen, suna tafka ta'asa. Akalla mutane 50 ne suka mutu," Hamisu Faru.
Ya ce har yanzu ba a iya tantance adadin mutanen da aka sace ba. Kawo yanzu, shugabannin al'umma da jami'an gwamnati na kan tattara bayanan wadanda aka tafi da su.
"Ba a saurari gargadinmu ba," Mazaunin Zamfara
Wani mazaunin Tungan Dutse, Abdullahi Sani, ya bayyana cewa sun ga 'yan bindiga sama da 150 a kan babura tun kafin su kawo wannan harin.
Abdullahi Sani ya koka da cewa sun sanar da jami'an tsaro da hukumomi, amma aka yi banza da gargaɗinsu, wanda hakan ya kai ga rasa rayuka masu yawa.
Ya bayyana cewa:
"Babu wanda ya yi barci a jiya, dukanmu muna cikin tsananin tashin hankali, ni kai na an kashe mini ƴan uwa guda uku a wannan harin."
Harin ya auku ne kwana ɗaya bayan ministan tsaro, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabbin motocin yaƙi da jiragen marasa matuƙa a cikin Jihar Zamfara.
Legit Hausa ta rahoto cewa Gwamna Dauda Lawal ne ya siyo waɗannan kayan aiki domin ƙarfafa tsaro, amma hakan bai hana ƴan bindiga keta alfarma tare da kashe talakawa ba.

Source: Original
Halin da al'umma ke ciki a Ramadan
Wannan mummunan hari ya jefa fargaba a zukatan mazauna maƙwabtan ƙauyuka, musamman ganin cewa ya faru ne a cikin wannan wata mai alfarma na Ramadan.
Mutane da yawa suna cikin damuwa yayin da suke gudanar da ibadunsu, domin ba su san lokacin da maharan za su sake dawowa ba.
Jaridar Vanguard ta rahoto wani Malam Yakubu Dan Ajiya, wanda ya tsallake wannan harin, ya shaidawa manema labarai cewa:
"Bayan sun gama kewaye mu, sai suka bude wuta kan mai uwa da wabi, suna bi gida gida suna kashe mutane, fiye da mutane 30 suka kashe, sun kuma tafi da wasu daji."
Kawo lokacin haɗa wannan rahoto, kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Zamfara, DSP Tasiu Abubakar, bai amsa kiran waya ba domin jin ta bakinsa.
'Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara
A wani labari, mun ruwaito cewa, 'yan bindiga sun sace mutanen da ba su san hawa ba, ba su sauka ba a jihar Zamfara bayan sun kai wasu hare-hare.
Miyagun 'yan bindigan sun sace mutanen ne a wasu kauyuka guda biyu na karamar hukumar Bukkuyum bayan sun farmake su a cikin dare.
Jami'an tsaro sun bayyana shirinsu na kubutar da kusan mutane 100 da aka yi garkuwa da su zuwa cikin daji domin ganin an sada su da iyalinsu.
Asali: Legit.ng


