Daga Fara Azumi, Malaman Musulunci 40 Sun Samu Kyautar Sababbin Motoci a Najeriya
- Gwamna Dauda Lawal ya raba wa limaman masallatan Juma'a 40 kyautar sababbin motoci domin taimaka masu wajen ayyukan addini
- Dauda Lawal ya ce ya zabi rabawa limaman motoci ne domin sauƙaƙa musu wajen tafiye-tafiyen wa'azi zuwa garuruwa daban-daban
- Gwamnan ya kuma roƙi limaman da su ci gaba da yi wa Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya addu’ar samun zaman lafiya da kwanciyar hankali
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya raba wa limaman masallatan Juma’a 40 sababbin motoci a matsayin tallafi daga gwamnatin jiha.
Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa ya ba limaman kyautar motocin ne domin tallafa masu wajen gudanar da harkokin koyar da addinin musulunci a Zamfara.

Source: Facebook
An ba malamai kyautar motoci a Zamfara
Jaridar Vanguard ta tattaro cewa an yi bikin mikawa limaman motocin a yau Juma'a, 20 ga watan Fabrairu, 2026 a fadar gwamnatin Zamfara da ke Gusau.

Kara karanta wannan
Ramadan: Gwamna ya amince da ciyar da talakawa, ya yi wa malaman addini tagomashi
Yayin da yake jawabi, Gwamna Lawal ya bayyana cewa ya yi haka ne domin inganta zirga-zirgar limaman da kuma sauƙaƙa musu zuwa garuruwa daban-daban wajen wa’azi da ayyukan wayar da kai.
Ya ce Zamfara jiha ce da aka gina bisa kyawawan ƙa’idojin Musulunci, inda limamai da dama ke hidimtawa al’umma a ƙananan hukumomi 14 na jihar.
Dalilin Gwamna Lawal na tallafa wa malamai
A cewarsa, kula da jin daɗin shugabannin addini na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa ta fi ba muhimmanci.
“Muna gina masallatai da gidaje ga limamai, kuma muna ganin yana da muhimmanci mu taimaka masu wajen tafiye-tafiye.
"Zirga-zirgar malamai tana da muhimmanci musamman wajen wa’azi da hulɗa da al’umma. Saboda haka muka zaɓi limamai 40 a wannan mataki na farko domin su samu motocin da za su taimaka musu,” in ji Dauda Lawal.
Ya ƙara da cewa shirin ba zai tsaya a nan ba, domin wannan rabon motoci shi ne mataki na farko, kuma za a ci gaba da aiwatar da shi a gaba, cewar Guardian.
Dauda Lawal ya roki limamai a Zamfara
Gwamna Lawal ya kuma roƙi limaman da su ci gaba da yi wa jihar Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya addu’ar samun zaman lafiya mai ɗorewa.
Tun da farko, Mai Bai wa Gwamna Shawara kan Harkokin Addini, Sheikh Bello Almufty, ya yaba da jagorancin Dauda Lawal, yana mai cewa gwamnan shugaba ne mai gaskiya, adalci da ci gaban bai ɗaya.
Ya ce gwamnatin Lawal ta kawo sauye-sauye masu ma’ana ga rayuwar malamai, ciki har da inganta alawus-alawus da sauran tallafi.

Source: Facebook
A nasa jawabin, Sheikh Atiku Zawiyya, wanda ya yi magana a madadin limaman, ya gode wa gwamnan kan wannan tallafi, yana mai cewa motocin za su taimaka wajen ƙarfafa ayyukan su na hidima ga al’umma.
Gwamnan Zamfara ya sayo kayan yaki
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya saya kayan yaki da suka hada da jirage marasa matuka domin tallafa wa dakarun Najeriya.
Gwamnan ya miƙa motoci masu sulke da sauran kayan aiki ga dakarun tsaro a wani biki da aka gudanar a fadar gwamnati da ke Gusau.
Ministan tsaro, Janar Christopher Musa (Mai ritaya) ya halarci taron kaddamar da kayan yakin, inda ya yaba wa Gwamna Dauda Lawal.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
