Dokar Zabe: Jam'iyyar ADC Ta Taso Tinubu a Gaba, Ta Fadi Shirin da Take Yi don Hana Magudi

Dokar Zabe: Jam'iyyar ADC Ta Taso Tinubu a Gaba, Ta Fadi Shirin da Take Yi don Hana Magudi

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu a dokar zabe ta shekarar 2026 wadda majalisa ta amince da ita
  • Jam'iyyar ADC mai adawa a Najeriya ta soki shugaban kasar kan matakin da ya dauka na sanyawa dokar hannu
  • ADC ta bayyana cewa gaggawar sanya hannu kan dokar ya nuna cewa akwai abin da jam'iyya mai mulki ke tsoro dangane da zaben 2027

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam’iyyar ADC ta soki shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan sanya hannu a dokar zabe ta shekarar 2026.

Jam'iyyar ADC ta ce wannan mataki ya yi daidai da sanya hannu kan kawo karshen gaskiya da adalci a zaɓen Najeriya.

ADC ta caccaki shugaban kasa Bola Tinubu
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu da mai magana da yawun ADC na kasa, Bola Abdullahi Hoto: @aonanuga1956, @BolajiADC
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya fitar ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairun 2026, wadda ya sanya a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

ADC, kungiyoyi sun nuna damuwa kan gaggawar Tinubu na amincewa da dokar zabe

Me ADC ta ce kan Shugaba Tinubu?

ADC ta nuna mamakin yadda shugaban kasa ya gaggauta amincewa da kudurin duk da irin korafin da ’yan kasa suka yi.

Jam’iyyar ta bayyana hakan a matsayin wani ɓangare na shirin tafka maguɗi a zaɓen 2027.

Wane shiri ADC ke yi?

ADC ta ce wannan ci gaba ya zana layin yaki tsakanin jam’iyya mai mulki da al’ummar Najeriya, inda ta kara da cewa za ta tattara ’yan kasa domin bijire wa duk wani maguɗin zaɓe ta hanyoyin da doka ta amince da su.

“Gaggawar da aka yi wajen sanya wa dokar zaɓe hannu na nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu don kashe sahihin zaɓe, kuma ta hakan ya mayar da dimokuradiyyar Najeriya baya da shekaru da dama."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta ce a lokacin da ’yan Najeriya ke kiran a samar da tsarin zaɓe na zamani mai cike da gaskiya, abin bakin ciki ne ganin shugaban da ke alfahari da kishin dimokuradiyya ya amince da gyare-gyaren da za su rage wa jama’a kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

Jigo a APC ya ankarar da Tinubu kan masu sauya sheka, ya fadi masu yanke makomarsa a 2027

“Ta hanyar kin yin jinkiri, da kin saurarar ƙorafe-ƙorafe, da kuma kin tuntuɓar ’yan Najeriya yadda ya kamata, Shugaba Tinubu da majalisar tarayya karkashin jagorancin APC sun nuna cewa tsoro suke ji na abin da al’ummar Najeriya za su yi musu a zaɓe na gaskiya da adalci."

- Bolaji Abdullahi

ADC ta soki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Mai magana da yawun jam'iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi Hoto: @BolajiADC
Source: Twitter

ADC 'yan Najeriya na iya kare kuri'unsu

Jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa rashin ba da tabbaci kan tura sakamakon zabe ta yanar gizo na iya sa ’yan kasa su ji cewa dole ne su kare ƙuri’unsu da kansu ta hanyar da ta dace.

“ADC tana sanar da ’yan Najeriya da abokan Najeriya na duniya cewa a matsayinmu na jam’iyyar siyasa, muna shirye kuma muna mika wuya wajen kare martabar dimokuradiyyar Najeriya ta kowace hanya ta shari’a da kundin tsarin mulki ya ba mu dama."

- Bolaji Abdullahi

Kwankwasiyya ta soki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa kungiyar Kwankwasiyya ta yi martani kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka na sanya hannu a dokar zabe.

Kwankwasiyya ta nuna damuwa kan abin da ta kira “sahalewar gaggawa” da Bola Ahmed Tinubu ya yi wa dokar mai cike da ce-ce-ku-ce.

Ta bayyana cewa duk da korafe-korafen jama’a da kiraye-kirayen kungiyoyin fararen hula, sahalewar shugaban kasa ta janyo tambayoyi kan makomar dimokuradiyya. R

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng