Ana cikin Azumi, Tinubu Ya Mika Bukata ga MTN, Airtel da Sauran Kamfanonin Sadarwa

Ana cikin Azumi, Tinubu Ya Mika Bukata ga MTN, Airtel da Sauran Kamfanonin Sadarwa

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya roki kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel da Glo da su samar da sabis mai karfi a cibiyoyin neman ilimi
  • Tinubu ya bayyana cewa duk da samun riba a irin wadannan wurare zai yi karanci, amma kamfanonin za su amfana da hakan a gaba
  • Shugaban kasar ya buƙaci kamfanonin su duba yiwuwar ba da damar amfani da wasu shafukan yanar gizo na ilimi kyauta da kuma tallafa wa fannin fasaha

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Yayin da azumin watan Ramadan ya kankama, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya waiwayi yanayin karfin intanet da ake samarwa a cibiyoyin ilimin Najeriya.

Shugaba Tinubu, ya roƙi kamfanonin sadarwa da su tabbatar da cewa cibiyoyin ilimi da sauran dandalin koyo sun samu damar amfani da intanet ba tare da tangarda ba.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ba Aminu Ado Bayero jagorancin ciyar da talakawa a Ramadan

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Shugaba Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya kai ziyarar aiki a jihar Katsina Hoto: Ibrahim Kaulaha Muhammed
Source: Facebook

Fannin da kamfanonin sadarwa suka ba fifiko

A cewar rahoton Vangaurd, shugaban ya ce ya lura cewa a harkokin kasuwancin kamfanonin sadarwa, sun fi daukar wuraren da suke samun riba da muhimmanci.

Tinubu ya ce hakan ya sa yawancin makarantu da wuraren ilimi, waɗanda ba su da fa’idar kasuwanci sosai, ba sa samun isasshen intanet.

Sai dai ya tunatar da su cewa ya kamata kamfanonin sadarwa su jawo kowane bangare a jiki domin amfanin al'umma.

Tinubu ya bayyana hakan ne a birnin Legas ta bakin Shugaban Majalisar Gudanarwa na Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, (NCC), Mista Idris Olorunnimbe.

Olorunnimbe ya karɓi baku cin tawagar kamfanonin sadarwa ƙarƙashin jagorancin Shugaban kungiyarsu, ALTON, Injiniya Gbenga Adebayo, jiya Alhamisinda ya ce roƙon saƙo ne kai tsaye daga shugaban kasa.

Tinubu ya mika bukata ga kamfanonin sadarwa

Ya ce Shugaba Tinubu ya buƙaci kamfanonin su duba yiwuwar ba da damar amfani da wasu shafukan yanar gizo na ilimi kyauta da kuma tallafa wa fannin fasaha da kirkire-kirkire saboda muhimmancinsu wajen gina matasa.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar Tinubu ta zo da alheri, kasafin gwamnatoci zai karu da tiriliyoyin Naira

"Kada ku ɗauki irin wannan zuba jari a fannin ilimi a matsayin asara, ku gan shi a matsayin ribar da za ta dawo nan gaba.
"Idan matasa sun samu damar koyo da gogewa ta intanet, ƙarfin samun kuɗinsu zai ƙaru, tattalin arziki zai amfana, kuma riba za ta dawo muku ta wata hanya daban,” in ji shi.
Sadarwa.
Wayoyin hannu da turken kamfanin sadarwa a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ƙara da cewa kamata ya yi kamfanonin sadarwa su dauki faɗaɗa sabis zuwa yankunan da ba su da sabis a matsayin wajibcin ƙasa, cewar rahoton Punch.

“Sadarwa ba aikin jin ƙai na kamfani ba ne, hakki ne na kowane ɗan Najeriya. Duk da cewa ribar kasuwanci tana da muhimmanci, bai kamata ta zama abu na farko da ake la’akari da shi ba,” in ji shi.

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar zabe

A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya kare matakinsa na sanya hannu a dokar gyaran zaɓe ta shekarar 2026 awanni kadan bayan Majalisa ta amince da ita.

Tinubu ya ce ingancin zaɓe ya dogara ne kan yadda ake tafiyar da shi da kuma sa idon ɗan adam, maimakon tura sakamako kai tsaye ta yanar gizo da ake ta surutu a kai.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ko ma wane irin tsarin fasaha aka yi amfani da shi, mutane ne ke gudanar da zaɓe kuma su ne ke kammala shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262