2027: Lagos Ta Sha Gaban Kano, Jigawa Ta zo Ta 1 a Fafatawar Yin Katin Zabe

2027: Lagos Ta Sha Gaban Kano, Jigawa Ta zo Ta 1 a Fafatawar Yin Katin Zabe

  • Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta fitar da adadin wadanda suka kammala rajistar katin zabe a shirin tunkarar siyasar 2027
  • Jihohin Jigawa, Lagos, Sokoto, Katsina, Zamfara, Kaduna da Delta na cikin wadanda suka samu mafi yawan jama'an da suka yi rajista
  • INEC ta sanar da cewa sama da mutum miliyan daya ne suka kammala rajista a fadin Najeriya daga ranar 13 ga watan Fabrairu, 2026

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta fitar da adadin wadanda suka yi rajistar katin zabe da ta fara tun a farkon shekarar 2025.

Daga 2025 zuwa 13 ga Fabarairun shekarar 2026, sama da mutum miliyan 1.2 ne suka kammala rajista da hukumar INEC domin mallakar katin zabe.

Kara karanta wannan

DSS na shirin gayyatar yaran El Rufa'i, matar Dadiyata ta yi magana kan dauke mijinta

Katin zabe da ake aiki da shi a Najeriya
Katin zabe da ake ba 'yan Najeriya bayan rajista. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayani da hukumar INEC ta yi ne a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X a ranar Alhamis, 19 ga Fabrairun 2026.

Wadanda suka kammala rajista a jihohi

Wani rahoto da The Cable ta wallafa ya nuna cewa jihar Jigawa ce ta farko da ta fi yawan masu rajista yayin da Anambra ta zo kurar baya.

Ga jerin jihohi da adadin da suka kammala rajista a cikinsu:

1. Jigawa: 99,698

2. Lagos: 86,307

3. Sokoto: 77,004

4. Kano: 71,990

5. Katsina: 60,730

6. Zamfara: 52,210

7. Kebbi: 42,295

8. Kaduna: 41,667

9. Delta: 39,529

10. Niger: 38,403

11. Benue: 36,799

12. Kogi: 34,928

13. Rivers: 34,811

14. Ogun: 33,163

15. Borno: 33,023

16. Oyo: 32,545

17. Bauchi: 32,483

18. Akwa Ibom: 31,695

19. Yobe: 31,393

20. Osun: 29,883

21. Adamawa: 27,728

22. Nasarawa: 26,990

23. Taraba: 25,488

Kara karanta wannan

Ana batun dokar zabe, kotu ta ba hukumar INEC sabon umarni

24. Kwara: 23,302

25. Gombe: 22,929

26. Ebonyi: 22,274

27. Cross River: 21,111

28. Imo: 17,593

29. Abia: 16,720

30. Bayelsa: 16,252

31. Plateau: 15,416

32. Ondo: 12,246

33. Enugu: 11,698

34. Edo: 11,516

35. Ekiti: 10,654

36. Anambra: 7,175

Jimilla: miliyan 1.23

Karin bayani kan rajistar katin zabe

A lokacin da aka fahimci Jigawa kurum ta samu fiye da 8% na sababbin wadanda suka yi rajista, an tsaida wannan shiri a wasu wurare.

An dakatar da rajista a Babban Birnin Tarayya (Abuja) har sai bayan zaɓen ƙananan hukumomi da za a yi ranar 21 ga Fabrairu, 2026.

A yanzu haka 'yan Najeriya:

  • 673,124 sun yi rajistar farko ta yanar gizo
  • 555,524 sun kammala rajista ta zahiri

Adadin masu rajista bisa jinsi:

  • Mata – 696,891 (57%)
  • Maza – 531,757 (43%)
Masu zabe a jihar Anambra
Masu zabe yayin zaben gwamna a Anambra a 2025. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

An yi shirin zabe a jihar Kano

A wani rahoton, kun ji cewa Rundunar 'yan sanda ta sanar da cewa an kammala shirye-shiryen gudanar da zabe cike gibi a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Izala ta dakatar da tafsiri, ta kira taron gaggawa a Kaduna

Bayan zaman kwamitin tsaro da ya shafe zabe, kwamishinan 'yan sanda ya sanar da cewa an takaita zirga-zirga a wasu yankuna.

INEC ta ce za a yi zabe a kananan hukumomin Birni da Ungogo domin cike gibin 'yan majalisar jihar da suka rasu a kwanakin baya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng