Babbar Magana: Jami'an ICPC Sun Kai Samame Gidan El Rufai, Sun Je Neman Wani Abu

Babbar Magana: Jami'an ICPC Sun Kai Samame Gidan El Rufai, Sun Je Neman Wani Abu

  • Jami'an hukumar ICPC sun kai samame gidan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai dake Abuja domin gudanar da bincike
  • Lauyan Nasir El-Rufai ya bayyana cewa binciken da aka yi a gidan tsohon gwamnan ya saba wa doka da take hakkin dan adam
  • Majalisar dokokin Kaduna ta bukaci a binciki El-Rufai kan zargin bacewar kudi har Naira biliyan 432 a lokacin da yake kan mulki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Jami’an hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (ICPC) sun gudanar da samame a gidan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, da ke Aso Drive a Abuja.

Wannan mataki ya biyo bayan kama El-Rufai da hukumar ta yi jim kaɗan bayan ya bar ofishin EFCC da ke a babban birnin tarayya Abuja.

Jami'an ICPC sun kai samame tare da yin bincike a gidan Malam Nasir El-Rufai na Kaduna.
Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai a dakin karatu. Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

ICPC ta kama El-Rufai

Kara karanta wannan

Halin da ake ciki yayin da El Rufai ke ci gaba da zama tsare a hannun EFCC

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda jami'an ICPC suka cafke El-Rufai a harabar hedikwatar EFCC, bayan bada belinsa daren ranar Laraba, 18 ga Fabrairu, 2026.

Tsohon gwamnan ya girmama gayyatar da hukumar EFCC ta yi masa tun a ranar Litinin, inda ya shafe kwanaki kafin a ba da belin sa daren jiya.

A cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ranar Laraba, shugaban yaɗa labarai na ICPC, Mista J. Okor Odey, ya tabbatar da cewa tsohon gwamnan yana tsare a wajensu.

Yayin da ICPC ba ta bayyana takamaiman dalilin kama El-Rufai da binciken da ake yi kansa ba, ta ce dai za ta sanar da jama'a halin da ake ciki nan gaba.

ICPC ta kai samame gidan El-Rufai

Sai dai a daren ranar Alhamis, mai magana da yawun El-Rufai, Muyiwa Adekeye, ya wallafa a shafinsa na X cewa jami'an ICPC sun gudanar da bincike a gidan tsohon gwamnan.

Muyiwa Adekeye ya ce:

"Hukumar ICPC ta gudanar da bincike a gidan Malam Nasir El-Rufai.
"Ubong Akpan, lauyan El- Rufai, ya yi Allah wadai da matakin, tare da bayya cewa matakin ya saɓa wa doka, kuma keta alfarma ce ga hanyoyin shari'a da kuma haƙƙoƙin ɗan Adam."

Kara karanta wannan

"Babu ruwan DSS," An ji wadanda suka cafke El Rufai bayan Ya bar hannun EFCC

Ma'abota kafofin sada zumunta sun bukaci ICPC ta rika gudanar da bincikenta cikin gaskiya game da El-Rufai
Malam Nasir El-Rufai a cikin mota jim kadan bayan ya isa ofishin EFCC a Abuja. Hoto: @MuyiwaAdekeye
Source: Twitter

Martanin mutane kan matakin ICPC

Wani mai amfani da kafar X, Imran U. Wakili (PULLO), shi ma ya tabbatar da cewa an kai samame gidan tsohon gwamnan a Abuja.

A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Imran ya bayyana cewa ba a samu wani tabbaci kan ko an ba da takardar izinin binciken ba, kuma mahukunta ba su fitar da wata sanarwa ba tukunna.

Ya ƙara da cewa waɗanda ke binciken su tabbatar suna bin doka, domin babu abin da za su samu na rashin gaskiya a gidan El-Rufai.

Majalisar dokokin Jihar Kaduna ta taɓa ba da shawarar cewa a binciki El-Rufai kan zargin ɓatar da naira biliyan 432 lokacin da yake kan mulki.

Halin da E-Rufai yake ciki

Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Jami'an DSS sun cafke El Rufai a harabar ofishin EFCC

Hukumar ICPC ta cafke tsohon gwamnan na Kaduna ne tare da tsare shi domin gudanar da bincike kan wasu zarge-zarge da ake yi masa.

Ci gaba da tsare El-Rufai na zuwa ne bayan ya samu beli daga wajen hukumar EFCC bayan ya kwashe kwana biyu a hannunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com