'Yan Ta'addan Lakurawa Sun Yi Ta'addanci kan Musulman da Ke Azumi a Kebbi
- An shiga jimami a jihar Kebbi bayan da 'yan ta'addan kungiyar Lakurawa suka kai wani harin ta'addanci a wasu kauyuka
- Tsagerun 'yan ta'addan sun hallaka mutane sama da 30 bayan sun kai hare-hare a kauyukan da ke yankin Arewacin jihar
- Rundunar 'yan sandan jihar Kebbi ta hannun mai magana da yawun bakinta, ta yi karin bayani kan munanan hare-haren na 'yan ta'addan Lakurawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Mayakan kungiyar 'yan ta'addan Lakurawa sun kai hare-haren ta'addanci a jihar Kebbi.
'Yan ta'addan na Lakurawa sun kashe mutane da dama tare da lalata kauyuka bakwai a wasu hare-haren da suka kai.

Source: Twitter
Jaridar Vanguard ta ce rundunar 'yan sanda ta tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na AFP hakan a ranar Alhamis, 19 ga watan Fabrairun 2026.
'Yan sanda sun tabbatar da harin
Kakakin rundunar 'yan sandan Kebbi, Bashir Usman ya ce mambobin kungiyar Lakurawa sun kai harin ne a kauyukan gundumar Bui da ke yankin Areqacin jihar da misalin ƙarfe 1:15 na rana a ranar Laraba.
Wani rahoton tsaro ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun kashe “fiye da mutane 30”.
“An kashe mutane da dama yayin da mazauna kauyukan Mamunu, Awasaka, Tungan Tsoho, Makangara, Kanzo, Gorun Naidal, da Dan Mai Ago suka haɗa kai domin tunkarar maharan.”
- Bashir Usman
''Yan ta'addan Lakurawa sun yi barna
Wani mazaunin ɗaya daga cikin ƙauyukan ya bayyana cewa aƙalla mutane 35 ne 'yan ta'addan suka kashe.
“Muna cikin gida muka ji ƙarar harbe-harbe. Mutanen da ke waje suka fara guduwa zuwa mafaka, harsashi ya sami wasu mutanen.”
- Wata majiya
Kakakin rundunar 'yan sandan, Bashir Usman, ya ce maharan sun kuma kwashe shanu a yayin hare-haren.
Ya kara da cewa an tura 'yan sanda, sojoji, da 'yan sa-kai na sa-kai zuwa yankin cikin gaggawa, tashar BBC News ta kawo labarin.
Waɗannan hare-hare sun faru ne kwanaki kaɗan bayan da jihar ta gudanar da bikin kamun kifi na Argungu (wanda UNESCO ta amince da shi), wanda ke tazarar kilomita 60 (mil 38) daga yankin Arewa inda hare-haren suka faru.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: Wasu jagororin 'yan bindiga 17 sun shiga hannu, 'yan sanda sun jero sunayensu

Source: Original
'Yan Lakurawa na kai hare-hare
Ana zargin ƙungiyar Lakurawa da kai hare-hare da dama kan al'ummomi a yankin Arewacin jihar Kebbi da kuma maƙwabciyarta jihar Sokoto.
Mambobin kungiyar suna fitowa ne daga sansaninsu na daji don yin fashi, satar shanu, da kuma kakaba “haraji” ga mazauna yankin.
Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa hare-hare ta sama da dakarun Amurka suka kai a jihar Sokoto a lokacin Kirsimeti sun yi nufin mambobin wannan kungiya ne da kuma wasu gungun “yan bindiga”.
Sojoji sun kashe 'yan ta'addan ISWAP
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu nasara kan 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno.
Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'adda 16 a hanyar Gidan Kaji da ke kan titin Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno.
Hakazalika, dakarun sun kwace kekuna fiye da 20, da dumbin kayayyaki, makamai, da sauran kayan masarufi wadanda ake amfani da su.
Asali: Legit.ng
