Jigo a APC Ya Ankarar da Tinubu kan Masu Sauya Sheka, Ya Fadi Masu Yanke Makomarsa a 2027
- Wani babba a jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, Alhaji Sani Shinkafi, ya yi tsokaci kan zaben shekarar 2027 da ake tunkara
- Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya ja kunnen shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan karfafa sauya shekar da 'yan siyasa suke yi
- Jagoran na APC ya bayyana cewa zaben 2027 zai kasance ne tsakanin talakawa da jam'iyyun siyasar da ake da su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Wani jigo a jam’iyyar APC, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi, ya gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan ƙarfafa sauya sheƙar ƴan siyasa.
Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya jaddada cewa nasarar zaɓe ta dogara ne kan muradin talakawa maimakon tsarin jam’iyya.

Source: Facebook
Shinkafi ya bayyana hakan ne yayi wani shiri na SYNFONI News wanda Dr. Kenon ya wallafa a shafinsa na X.
Me jigon APC ya ce kan zaben 2027?
Jigon na APC ya bayyana cewa idan har talakawa ba su gamsu da salon mulki ba, zai yi wuya kowace jam’iyya ta yi nasara, yana mai jaddada cewa zaɓen 2027 zai kasance ne tsakanin talakawa da jam’iyyun siyasa.
Ya kafa hujja da cewa abubuwan da suka faru a zaɓukan 2015 da 2023 sun nuna cewa tsarin jam’iyya kaɗai ba ya ba da tabbacin nasara.
Ya kawo misalin Peter Obi da Buhari
Ya buga misali da tarihin siyasar Peter Obi, inda ya tuna cewa ya tsaya takarar gwamnan jihar Anambra a 2003 a karkashin jam’iyyar APGA, wadda a lokacin ba ta da wani tsari mai karfi, amma duk da haka ya lashe kananan hukumomi 17 cikin 21 bisa sakamakon da aka gabatar a kotu.
Haka kuma, ya yi nuni da zaɓen shugaban ƙasa na 2023, inda ya bayyana cewa Obi, wanda ya koma LP, ya doke Tinubu a jihar Legas da kuma babban birnin tarayya Abuja, duk da cewa jam’iyyar ba ta da gwamna ko ɗan majalisa ko ɗaya kafin zaɓen.

Kara karanta wannan
Kurunkus: Gwamna Abba ya bayyana ainihin dalilinsa na komawa APC a gaban Shettima
“Bisa zaɓukan 2015 da 2023, za ku yarda da ni cewa babu amfanin yawan sauya shekar siyasa maras dalili. Talakawa ne a ko da yaushe suke yanke wanda zai yi nasara.”
- Sani Abdullahi Shinkafi
Ya kuma tunatar da yadda a shekarar 2015, tsohon Shugaba Muhammadu Buhari ya doke Shugaba Goodluck Jonathan duk da cewa jam’iyyar PDP ce ke iko da mafi yawan jihohi da mambobin majalisa a lokacin.
Shinkafi ya fadi rawar da Arewa ta taka
Shinkafi ya nanata cewa shiyyar Arewa Maso Yamma ta taka rawar gani sosai wajen ganin Tinubu ya zama ɗan takarar APC da kuma nasararsa a babban zaɓe, inda shiyyar ta ba da kuri’u sama da miliyan 2.8.
Ya lissafa manyan mutane daga shiyyar kamar su tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje a matsayin waɗanda suka yi tasiri.

Source: Facebook
Wace shawara ya ba Shugaba Tinubu?
Daga ƙarshe, 'dan siyasar ya shawarci shugaban ƙasa da ya mayar da hankali wajen cika alkawuran da ya ɗauka lokacin yaƙin neman zaɓe, sannan ya kafa wata kungiyar kwararru domin sake tuntuɓar masu kaɗa ƙuri’a gabanin zaɓen 2027.
“Zaɓen 2027 zai kasance ne tsakanin jam’iyyun siyasa da talakawan Najeriya. Idan talakawa ba su gamsu ba, zai yi wuya kowace jam’iyya ta yi nasara."
- Alhaji Sani Shinkafi
Tinubu ya yi magana kan dokar zabe
A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan dokar zabe ta shekarar 2026.
Shugaban Najeriyan ya ce ingancin zaɓe ya dogara ne kacokan kan yadda ake tafiyar da shi da kuma sa idon ɗan adam.
Mai girma Bola Tinubu ya jaddada cewa ko ma wane irin tsarin fasaha aka yi amfani da shi, mutane ne ke gudanar da zaɓe kuma su ne ke kammala shi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

