Arewa Ta Yi Rashi: Watanni bayan Nada Shi Muƙami, Babban Sojan Ruwa Ya Rasu

Arewa Ta Yi Rashi: Watanni bayan Nada Shi Muƙami, Babban Sojan Ruwa Ya Rasu

  • Shugaban kula da sashen Ayyuka na Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya ya yi bankwana da duniya bayan ya yi fama da jinya
  • Marigayin Rear Admiral Musa Katagum, ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, lamarin da ya girgiza rundunar da al'umma
  • Marigayin ya taba rike mukamin Shugaban Leken Asirin Sojin Ruwa, sannan kwanan nan aka nada shi shugaban sashen Ayyuka a Hedikwatar Rundunar

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Rundunar sojojin ruwa a Najeriya ta yi gagarumin rashi bayan sanar da mutuwar wani babban sojanta.

Shugaban sashen Ayyuka na Hedikwatar Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, Rear Admiral Musa Katagum, ya rasu.

Rundunar sojojin ruwa ta yi babban rashi
Shugaban sojojin ruwa, Vice Admiral Idi Abbas da marigayi Rear Admiral Musa Katagum. Hoto: Nigeria Navy.
Source: Facebook

Rahoton Zagazalola Makama ya tabbatar da haka a shafin X inda ya ce marigayin ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya.

Soja ta rasu watanni da ba shi mukami

Kara karanta wannan

An ji abin da ya roka da Tinubu ya yi waya da Shugaban gwamnatin kasar Jamus a tarho

Marigayin wanda ake girmamawa a cikin rundunar, ya taba aiki a Hedikwatar Tsaro ta Kasa, sannan ya rike mukamin Shugaban Leken Asirin Sojin Ruwa.

Watannin bayan ne Shugaban Hafsan Sojin Ruwa ya nada shi a matsayin Shugaban Ayyuka, inda yake kula da muhimman ayyukan tsaro na rundunar, cewar Punch.

A tsawon rayuwarsa ta aiki, Rear Admiral Katagum ya bayar da gagarumar gudummawa wajen karfafa tsaron kasa da inganta dabarun ayyuka.

Nasarorin da marigayin ya taimaka aka samu

Ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara dabarun yaki, bunkasa kwarewar leken asiri, tare da horas da sababbin jami’ai masu kishin kasa.

Kwarewarsa da tsantsar kulawarsa ga ayyuka sun tabbatar da cewa rundunar ta kasance cikin shiri da karfi wajen kare muradun Najeriya a teku.

An yi babban sojan ruwa a Najeriya
Marigayi sojan ruwa, Real Admiral Musa Katagum. Hoto: @ZagazOlaMakama.
Source: Twitter

An bayyana gundunmawar marigayi a gidan soja

Gudummawarsa ta taimaka matuka wajen kare ruwan iyakar Najeriya da kuma kara karfin shirin rundunar wajen tunkarar barazana.

Labarin rasuwarsa ya jefa alhini a cikin dakarun sojoji, inda abokan aikinsa suka bayyana shi a matsayin abin koyi na jarumtaka da ladabi.

Manyan hafsoshin sojin ruwa sun nuna alhininsu kan rasuwar wannan jagora mai hangen nesa, wanda tarihin aikinsa zai ci gaba da zama a zukatan al'umma.

Kara karanta wannan

Babban albishirin Dangote ga 'yan Najeriya kan farashin Naira a 2026

Abubuwan da za a ke tunawa da marigayin

Baya ga nasarorinsa na aiki, za a rika tunawa da shi saboda tawali’unsa, karamcinsa da jajircewarsa wajen kula da walwalar abokan aikinsa.

Yayin da ake alhinin rasuwarsa, ana kuma yabawa rayuwarsa wadda ya sadaukar da ita ga hidimar kasa cikin jarumtaka da gaskiya.

Mutane sun yi addu'ar Allah ya jikansa da rahama, ya kuma bai wa iyalansa da abokan aikinsa hakurin jure wannan babban rashi da aka yi.

Taohon shugaban sojojin ruwa ya mutu

A baya, mun ba ku labarin cewa Hedkwatar rundunar sojojin ruwa ta sanar da mutuwar tsohon Shugaban hafsoshinta, Vice Admiral Patrick Seubo Koshoni mai ritaya.

An tabbatar da cewa babban jami’in ya rasu a ranar 25 ga watan Janairun shekarar 2020 bayan wani dan gajeren rashin lafiya da ya yi fama da shi.

Marigayin ya halarci kwasa-kwasai da dama na sojin ruwa kuma ya jagoranci mukaman sojin ruwa da dama da kuma na nade-naden soji, da kwamitoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.