Yanzu Yanzu: Tsohon Shugaban sojin ruwa ya mutu

Yanzu Yanzu: Tsohon Shugaban sojin ruwa ya mutu

- Hedkwatar rundunar sojin ruwa ta sanar da mutuwar tsohon Shugaban hafsoshinta, Vice Admiral Patrick Seubo Koshoni mai ritaya

- Babban jami’in ya rasu a ranar 25 ga watan Janairu 2020 bayan wani dan gajeren rashin lafiya

- Marigayin ya halarci kwasa-kwasai da dama na sojin ruwa kuma ya jagoranci mukaman sojin ruwa da dama da kuma na nade-naden soji, da kwamitoci

Hedkwatar rundunar sojin ruwa ta sanar da mutuwar tsohon Shugaban hafsoshinta, Vice Admiral Patrick Seubo Koshoni mai ritaya.

Legit.ng ta ruwaito cewa an bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 30 ga watan Janairu a wani jawabi dauke da sa hannun Commodore Suleiman Dahun a madadin shugaban hafsan sojin ruwan.

Yanzu Yanzu: Tsohon Shugaban sojin ruwa ya mutu
Yanzu Yanzu: Tsohon Shugaban sojin ruwa ya mutu
Asali: UGC

Marigayin ya halarci kwasa-kwasai da dama na sojin ruwa kuma ya jagoranci mukaman sojin ruwa da dama da kuma na nade-naden soji, da kwamitoci.

Sanarwar ya zo kamar haka: “hedkwatar rundunar sojin ruwa na burin sanar da mutuwar wani tsohon shugaban hafsoshinta, Vice admiral Patrick Seubo Koshoni mai ritaya.

“Babban jami’in ya rasu a ranar 25 ga watan Janairu 2020 bayan wani dan gajeren rashin lafiya. An haife shi a Lagas a ranar 11 ga watan Afrilu 1943, Vice Admiral Koshoni ya shiga aikin sojin ruwan Najeriya a ranar 11 ga watan Yuni 1962 bayan karatun sakandare a makarantar St Finbarr College, Akoko, Lagas.

KU KARANTA KUMA: Gwamnan Adamawa ya sallami ma’aikata 5,000 kan rashin bin ka’idar daukar aiki

“A wannan shekarar ya fara amsar horon sojan ruwa a makarantar National Defence Training Academy da ke Indiya sannan aka kaddamar dashi a matsayin Laftanal a ranar 13 ga watan Yuli 1964.

Admiral Koshoni ya halarci kwasa-kwasan soji da dama.”

A wani labari na daban, mun ji cewa al’ummar Unguwar Dorayi karama sun kama wani mutum mai suna Musa da ya jefar da gawar wani almajiri mai suna Nasir a yankin.

Lamarin ya faru ne da yammacin jiya Laraba, in da wata mata mai suna Amina ta hango shi ta Katanga a yayin da ya jefar da gawar. Ya yi wa matar barazanar cewa zai halakata, kamar yadda ta shaidawa gidan rediyon Dala.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel