Babbar Magana: Izala Ta Dakatar da Tafsiri, Ta Kira Taron Gaggawa a Kaduna
- Kungiyar Izala ta dakatar da tafsiri a wasu yankunan Zariya da ke jihar Kaduna tare da kiran malamai wani taron gaggawa
- Legit Hausa ta tattaunawa da wani daga cikin 'yan kungiyar Izala game da dalilan daukar matakin da ya zo wa jama'a da mamaki
- Jagoran kungiyar ya bayyana cewa wani sabani ya taso game da masallacin da ya ce mallakarsu ne sama da shekara 30 da suka wuce
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Kungiyar Izala ta dakatar da tafsirin Ramadan a Zaria da Sabon Garin Zaria a yau Alhamis 19 ga Fabrairun 2026 saboda rikicin masallaci da aka dade ana yi.
Dan kungiyar ya bayyana cewa zaman da za su yi yau shi zai nuna za a dawo a cigaba da tafsiri ko kuma za a dakatar da shi a dukkan fadin jihar.

Source: Facebook
Legit Hausa ta samu bayanai game da dakatar da tafsirin da Izala ta yi a wani sako da shafin Jibwis Kaduna ya wallafa a Facebook.
Izala ta dakatar da tafsiri
Kungiyar Izala ta sanar da cewa tana gayyatar malamai zuwa wani taron gaggawa saboda wata matsalar masallaci da ta taso a Zariya.
Sanarwar kungiyar ta ce:
"Shugabannin Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa-iqamatis Sunnah (JIBWIS) reshen jihar Kaduna na sanar da dukkan malaman da ke gabatar da tafsiri a Zaria da Sabon Garin Zaria da su rufe Tafsiri da gaggawa na yau.
"Kuma tana bada umarni ga dukkan malamai da mabiya da su hadu a Masallacin Low-cost da karfe 3:30 na rana dai dai."
Daya daga cikin jami'an kungiyar ya ce:
"A yanzu dakatarwan na yau ne, yanda sakamako ya zo zai nuna ko za a cigaba, ko kuma ma za a fadada zuwa duka jihar"
Me ya sa Izala ta dakatar da tafsiri?
A wata tattaunawa da wani jagora a kungiyar Izala da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa an dauki matakin ne saboda rikici game da wani masallaci.
Ya ce:
"Abin da ke faruwa shi ne, wannan masallaci na Low-cost wanda tun da ana karamin masallacin da Izala ta gina, lokacin tsohon gwamna Abba Musa Rimi ya ba da wannan filin, Izala ta gina masallacin.
"Sama da shekara 30 tana gudanar da masallacin, tana tafsiri da sallar Juma'a, sai daga baya wasu suka taso wai masallacin nasu ne."
Bayan shekara biyu, ya ce sai yanzu mutanen suka samo wata takarda da ta ce za su cigaba da gudanar da masallacin kuma lamarin yana kotu.
"Saboda haka ne aka ce a bar duk abin da ake a taho a tare a can."
Jagoran kungiyar ya bayyana cewa masallacin shi ne babban masallacin Izala, a nan suka fara sallar Idi, kuma kowa yana jingina su da masallacin.

Source: Facebook
Za a karya azumi saboda wahala?
A wani rahoton, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi karin haske game da hukuncin karya azumi saboda tsananin wahala.
Malamin ya yi magana ne yayin da aka masa tambaya game da hakan yayin da ya ke tafsirin Ramadan a jihar Gombe a wata shekara da ta gabata.
Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bambance tsakanin tsananin wahala da matsakaiciyar wahala kafin bayar da amsa ga mai tambayar.
Asali: Legit.ng


