Hukuncin Karya Azumi saboda Tsananin Wahala Tare da Sheikh Daurawa
- An tambayi Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa game da hukuncin mutumin da ya karya azumin Ramadan saboda tsananin wahala
- Kafin ba da amsa a kan tambayar, malamin ya bayyana abin da ake nufi da tsananin wahala a mahangar Shari'ar Musulunci
- Sheikh Daurawa ya amsa tambayar ne a lokacin tafsirin Ramadan da ya gabatar a kofar gidan mai unguwa Doma a jihar Gombe
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi karin haske game da hukuncin karya azumi saboda tsananin wahala.
Sheikh Aminu Daurawa ya yi bayanin ne bayan wata tambaya da aka masa yayin da ya ke gabatar da tafsirin Ramadan a jihar Gombe.

Source: Facebook
Legit Hausa ta tattaro hukunce-hukunce game da amsar da Sheikh Aminu Daurawa ya bayar a wani bidiyo da El-Uthman ya wallafa a shafinsa na X.
Azumi: Menene tsananin wahala?
Kafin bayar da amsa, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana cewa akwai bambancin tsakanin wahala da tsakanin wahala idan ana azumi.
Malam Daurawa ya ce malamai sun yi wa tsananin wahala fassara kala uku:
- Abin da zai haifar da ciwo
- Abin da zai sa ciwo ya kara girma
- Abin da zai sa ciwo ya ki warkewa
Karya azumi saboda tsananin wahala
A amsar da ya bayar, Sheikh Aminu Daurawa ya bayyana cewa za a ajiye azumi duk lokacin da aka samu tsakanin wahala.
Sheikh Daurawa ya fadi haka yana kafa hujja da cewa:
"Domin Allah bai daura muku azumi don ku mutu ba, sai domin samun takawa."
Gargadi karya azumi saboda matsakaiciyar wahala
Bayan amsa tamayar, Sheikh Aminu Daurawa ya yi gargadi da cewa ba a ajiye azumin Ramadan domin shiga wahala matsakaiciya.
Ya ce:
"Domin Allah ya san za a sha wahala matsakaiciya, shi yasa ya ce kai a ci, kar a sha, kar a je wa iyali."
Malamin ya bayyana cewa azumin wata tarbiyya ce da Allah ya ke yi wa mutum domin tabbatar da imaninsa, ya ce duk wanda ya yi azumi, ba munafuki ba ne.
Ya fadi haka yana mai cewa mutum zai iya shiga daki da abinci bai ci ba, saboda karfin imami da rashin munafurci a tattare da shi.
Sheikh Daurawa ya jaddada cewa:
"Wahala kadai ba ta sa a ajiye azumi, sai tsananin wahala."

Source: Facebook
Ga bidiyon da Sheikh Daurawa ya yi bayanin a kasa:
Bayani daga Edita:
Legit Hausa ba ta kiyaye a tafsirin azumin wace shekara ba ne Sheikh Aminu Daurawa ya amsa tambayar da aka yi masa a kan karya azumi saboda tsananin wahala.
Shugaban APC ya ziyarci Aminu Daurawa
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ziyarci Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa.
Farfesa Yilwatda ya bayyana cewa alaƙarsa da Sheikh Daurawa ta samo asali ne tun a lokacin da ya rike Ministan jin kai na Najeriya.
Shugaban APC ya yi alkawarin daukar nauyin dalibai mata daga makarantar Zamzam da Sheikh Daurawa ke lura da ita zuwa matakin jami'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

