An ji Abin da Ya Roka da Tinubu Ya Yi Waya da Shugaban Gwamnatin Kasar Jamus a Tarho
- Shugaba Bola Ahmed Tinubu da shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, sun tattauna kan abubuwa da dama ta wayar tarho
- A hirar da suka yi, Bola Tinubu ya roki gwamnatin Jamus ta taimakawa Najeriya da kwancen jiragen helikwafta da ta riga ta yi amfani da su
- Haka zalika shugabannin biyu sun yi maganar yadda za a inganta wutar lantarki a Najeriya duk da kasashen biyu sun taba kulla wata yarjejeniya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi waya da shugaban gwamnatin kasar Jamus, Friedrich Merz a tarho.
Shugaba Bola Tinubu ya roki a taimakawa Najeriya da kwancen jirage masu saukar angulu, wadanda kasar Jamus ta yi amfani da su.

Source: Twitter
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X.
Abin da Tinubu ya roki gwamnatin Jamus
Ya ce Tinubu ya yi wannan roƙo ne a tattaunawar waya da ya yi da Shugaban Gwamnatin Jamurs, Friedrich Merz, a ranar Laraba da rana, wadda ta ɗauki kusan mintuna 10.
Sanarwar ta ce shugabannin biyu sun amince da inganta alaƙar ƙasashen biyu da ƙarfafa haɗin gwiwa a fannoni kamar tsaro, wutar lantarki da layin dogo.
“Yankin sahara na cikin matsala kuma yana buƙatar tallafi. Ana buƙatar ƙarin bayanan sirri da sa ido,” Tinubu ya fadawa Merz.
Sai dai sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar ba ta bayyana ko Jamus ta amince da buƙatar Shugaba Tinubu ba.
Abubuwan da Tinubu ya tattauna da Merz
Shugabannin biyu sun kuma tattauna kan shirin wutar lantarki na Shugaban Ƙasa, wanda aka ƙirƙira domin inganta samar da wutar lantarki a Najeriya.
Tinubu ya ce Najeriya na buƙatar taimako wajen inganta hanyoyin isar da wutar lantarki.
A cewar sanarwar, Merz ya yi alƙawarin cewa kamfanin Siemens zai taimaka a wannan ɓangare, yayin da Deutsche Bank za ta iya samar da kuɗaɗen tallafin aikin.
Najeriya na da yarjejeniya da Jamus tun 2019
A halin yanzu, akwai yarjejeniyar Dala biliyan 2.3 tsakanin Najeriya da Siemens kan wutar lantarki, wadda ta samu tangarda tun daga 2019.
A watan Disamba 2021, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da ware Dala miliyan 1.9 da Yuro miliyan 62.9 domin fara mataki na farko na aikin, wanda ya haɗa da sabunta, gyara da faɗaɗa layin wutar lantarki na ƙasa.
A watan Nuwamban da ya gabata, Tinubu ya amince cewa an samu ci gaba a aikin Siemens, amma ya ce bai kai matsayin da ake sa rai ba.

Source: Twitter
Haka kuma, shugabannin sun tattauna kan haɗin gwiwa a ɓangaren fasaha da al’adu, inda shugaban gwamnatin Jamus ya yi kira da a kafa Babban Gidan Tarihi na Fasahar Afirka.
Merz ya kuma shaidawa Bola Ahmed Tinubu cewa ƙasarsa na dakon isowar sabon jakadan Najeriya zuwa Jamus.
Bola Tinubu ya rattaba hannu a dokar zabe
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta shekarar 2026 a fadar gwamnati dake Abuja.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da kudirin dokar da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi a ranar Talata, bayan kwashe watanni ana tattaunawa.
Shugaban ya sanya wa dokar hannu ne a fadar gwamnati a gaban manyan jami’an gwamnati, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio.
Asali: Legit.ng


