Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Mai Martaba Sarki, Sun Harbe Shi har Lahira

Tashin Hankali: Ƴan Bindiga Sun Sace Mai Martaba Sarki, Sun Harbe Shi har Lahira

  • Wasu mahara su shida sun yi garkuwa da Oba Kehinde Jacob Falodun sannan suka kashe shi a kusa da fadarsa da ke a jihar Ondo
  • Majiyoyi sun bayyana cewa 'yan bindigar sun yi amfani da karfin tuwo wajen fitar da sarkin daga fadarsa kafin su harbe shi
  • Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da faruwar lamarin, sannan ta bayyana matakan da aka dauka zuwa wannan lokaci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Ondo - Wasu gungun mahara sun yi garkuwa da Mai martaba sarki, Oba Kehinde Jacob Falodun, na garin Agamo, sannan suka kashe shi a jihar Ondo.

Rundunar ƴan sanda a jihar Ondo sun tabbatar da cewa wasu 'yan bindiga da suka kai su shida ne suka farmaki fadar basaraken a ranar Laraba.

'Yan bindiga sun kashe wani basarake a Ondo bayan sun yi garkuwa da shi.
Taswirar jihar Ondo, inda 'yan bindiga suka yi garkuwa da basarake, suka kashe shi. Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan bindiga sun kashe mai martaba sarki

Kara karanta wannan

'Yan bindiga 200 sun shiga garuruwa 3 da Asubah, sun kashe mutane sama da 30

Wani rahoto na jaridar This Day ya nuna cewa 'yan bindigar sun kutsa gidan Sarki Kehinde Falodun da tsakiyar dare don yin garkuwa da shi.

An ce basaraken ya yi iyakar kokarinsa don nuna turjiya ga maharan, amma aka tafi da shi. Sai dai, an jiyo karar harbin bindiga nesa kadan da fadarsa.

Majiyoyi sun ce, an tsinci gawar Sarki Kehinde ne bayan 'yan ta'addan sun tafi, lamarin da ya jefa al'mmar Agamo cikin tashin hankali.

Rundunar 'yan sandan jihar Ondo ta tabbatar da cewa 'yan bindigar sun farmaki gidan basaraken, kumar har sun kashe shi bayan garkuwa da shi.

'Yan sanda sun tabbatar da kisan sarki

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun yi amfani da ƙarfin tuwo wajen sace sarkin daga harabar gidansa kafin su tsere da shi zuwa daji.

A cikin wata sanarwa da kakakin 'yan sandan jihar, Abayomi Jimoh ya fitar a ranar Alhamis, rundunar ta bayyana cewa:

"Mun samu rahoto a ofishinmu da misalin karfe 7:50 na dare daga wani shugaban yankin, Chief Ajewole Clement na New Town, cewa 'yan bindiga shida sun farmaki gidan sarkin, kuma sun tsere daga wurin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan bindiga sun saki bidiyon mutane 176 da suka sace a Kwara

"An tsinci gawar wanda aka sacen nesa kadan da fadarsa, dauke da harbin bindiga. A nan take ne aka tabbatar da cewa ya mutu."
Rundunar 'yan sanda ta ce ta tura jami'ai don kamo wadanda suka kashe sarki a Ondo.
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun yana aiki a ofishinsa. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Matakin da 'yan sanda suka dauka

Abayomi Jimoh ya bayyana cewa an tura jami'an bincike na musamman zuwa yankin domin samar da tsaro da kuma ƙoƙarin kamo waɗanda suka aikata kisan, in ji rahoton Channels TV.

Jimoh ya ƙara da cewa:

"Jami'anmu tare da haɗin gwiwar Amotekun da mafarauta suna cikin daji domin neman waɗanda suka yi wannan danyen aikin."

Rundunar ƴan sandan ta yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu sannan su bayar da muhimman bayanai domin taimaka wa binciken.

Jami'an tsaro sun tabbatar wa jama'a cewa ba za su huta ba har sai sun kamo waɗanda ke da hannu a wannan kisan gilla yau.

'Yan bindiga sun sace wani sarki a Kwara

A wani labari, mun ruwaito cewa, al’umma sun shiga tsananin firgici bayan wasu da ake zargin masu garkuwa ne sun sace Sarkin Bayagan, jihar Kwara.

An ce, 'yan ta'addan, dauke da miyagun makamai sun sace Mai martaba Ojibara na Bayagan, watau Oba Kamilu Salami, a cikin garin Ifelodun.

Bincike ya nuna cewa babu wata turjiya da ta faru a wurin da aka sace basaraken, sai alamar sawun babura da suka nuna cewa maharan sun nausa cikin daji.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com