Katuwar Bishiya Ta Kifo kan Fasinjoji a Mota, Ta Danne Su Sun Mutu

Katuwar Bishiya Ta Kifo kan Fasinjoji a Mota, Ta Danne Su Sun Mutu

  • Fasinjoji 11 sun mutu yayin da wata babbar bishiya da ta shafe shekara da shekaru ta faɗo kan motoci a da suka tsaya a karkashin ta
  • Jami'an 'yan sanda sun bayyana cewa sun kai dauki ga mutanen da lamarin ya rutsa da su nan take, sai dai duk da haka sun rasu a asibiti
  • Kwamishinan 'yan sanda ya yi kira ga al'umma da su rika taka tsantsan wajen tsayawa a karkashin bishiyoyi domin tsira da rayuwarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Enugu - An tabbatar da mutuwar akalla mutane 11 bayan wata babbar bishiya ta faɗo kan wasu motocin haya guda biyu a dandalin kasuwar kauyen Awhum da ke karamar hukumar Udi a jihar Enugu.

Legit Hausa ta samu rahoton cewa lamarin, wanda ya faru da misalin ƙarfe 8:45 na dare a ranar Talata, ya shafi motar bas kirar Toyota Hiace da kuma ƙaramar mota kirar Sienna.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun yi wa 'yan APC jina jina a wajen taro, wasu sun rasu

Bishiya ta fado kan fasinjoji a Enugu
Wajen da bishiya ta fado kan fasinjoji a Enugu. Hoto: @Enugu_PoliceNg
Source: Twitter

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa a X, jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar, Daniel Ndukwe, ya ce waɗanda abin ya shafa fasinjoji ne da ke kan hanya.

Yadda bishiya ta fado kan mutane

A cewar ’yan sanda, motocin sun tsaya ne a dandalin kasuwar domin sauke wasu fasinjoji lokacin da bishiyar ta kife ta faɗa kansu.

Wani ɓangare na sanarwar ya ce:

“Binciken farko ya nuna cewa motocin sun tsaya domin sauke fasinjoji lokacin da bishiyar, wadda ta karkato sakamakon ruwan sama mai yawa, iska mai ƙarfi da kuma raunin da jikinta ya yi, ta faɗa kansu.
“Bayan samun rahoton, jami’an da ke aiki a sashen 9th Mile Division sun gaggauta zuwa wurin, tare da taimakon al’ummar yankin suka ceto mutane huɗu da suka makale a cikin motocin tare da tsare wurin da abin ya faru.

Kara karanta wannan

Dan bindiga ya harbe Amurkawa har lahira bayan Trump ya turo sojoji Najeriya

'Yan sanda sun kara da cewa:

“An kai sauran mutum 11 asibiti cikin gaggawa amma daga baya likitoci suka tabbatar da mutuwarsu.
"An ajiye gawawwakin a ɗakin ajiye gawa domin kammala sauran matakan da suka dace.”
Taswirar jihar Enugu
Taswirar jihar Enugu a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Gargadin kwamishinan 'yan sanda

Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, CP Mamman Giwa, yayin da yake miƙa ta’aziyya ga iyalan mamatan da al’ummar Awhum, ya bayyana lamarin a matsayin mummunan al’amari mai cike da takaici.

Yayin magana kan matakan da ya kamata a ɗauka, ya ba da shawara ga shugabannin al’umma da mazauna jihar da su kasance masu kula da muhalli.

Punch ta rahoto kakakin 'yan sanda ya ce:

“Kwamishinan ya shawarci shugabannin al’umma da mazauna jihar da su riƙa dubawa da kula da manyan bishiyoyi ko tsofaffin bishiyoyi a kusa da kasuwanni, tashoshin mota, makarantu da wuraren zama,”

A kai hari taron APC a Ondo

A wani labarin, mun kawo muku cewa wasu 'yan daba sun kai hari a wajen taron jam'iyyar APC da aka fara gudanarwa a Ondo.

Kara karanta wannan

Wanda mahaifinsa ya daure tsirara ya zama 'kwarangwal' bayan shekara 17

Shugaban jam'iyyar APC na jihar ya bayyana cewa maharan sun harbi dan uwansa, sun sara shi da wuka suna tunanin shi ne.

Rahotanni sun nuna cewa dattawan APC a jihar sun yi Allah wadai da lamarin suna cewa ba a kafa APC domin ta'addanci ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng