Gwamna Ya Gama Shiri, Ya Bayyana yadda Zai Sa Tinubu Ya Yi Nasara a Jiharsa
- Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai samu kuri'un jihar Taraba 100 bisa 100 a zaben 2027
- Kefas ya nuna cewa fikirarsa ta tsohon jami'in soja ta taimaka masa wajen tsara taswirar siyasa da za ta tabbatar da nasarar Tinubu
- Game da matsalolin tsaro da yankunan Arewacin Najeriya ke fuskanta, Gwamna Kefas ya fadi halin da ake ciki a Taraba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Taraba - Gwamna Agbu Kefas na Jihar Taraba ya bayyana cewa ba zai fuskanci wata matsala wajen samawa Shugaba Bola Tinubu kuri'un jiharsa a yanzu ba.
Ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Laraba bayan ganawarsa ta farko da Bola Tinubu tun bayan shigarsa APC.

Source: Twitter
Kefas ya bayyana kwarin gwiwar cewa goyon bayan da yake da shi daga talakawan jihar yana nan daram kuma Tinubu ya ci zabe cikin sauki, a cewar rahoton Punch.
Gwamnan Taraba ya tsara nasarar Tinubu
Gwamnan ya jaddada cewa dabarunsa na tsohon jami'in soja sun ba shi damar tsara taswirar da za ta ba shugaba Tinubu gagarumar nasara a Taraba.
Gwamna Kefas ya ce:
"Kun san inda na fito. Kun san asali na, ina da dabarun sirri na soja. Kuma ba ma yin abubuwa haka kawai."
Ya bayyana cewa ba sa yin abubuwa haka kawai domin sun riga sun gama tsara taswirar nasarar APC daki-daki a jihar.
Kefas ya yi watsi da maganganun wasu mabiya PDP a kafafen sada zumunta wadanda suka nuna rashin jin dadin su kan sauya shekar.
Ya bugi kirji da cewa dukkan mambobin majalisar dokoki da shugabannin kananan hukumomi 16 sun biyo shi zuwa jam'iyyar APC, kuma za su taimaka wajen nasarar Tinubu.
'Ban koma APC don kudi ba' - Gwamna
Gwamnan ya bayyana cewa ganawarsa da shugaba Tinubu ta mayar da hankali ne kan batutuwan tsaro da kuma jin dadin al'ummar jihar Taraba.
Kefas ya kuma musanta jita-jitar cewa an ba shi kudi domin ya koma APC, inda ya ce ya yi hakan ne don ci-gaban jama'arsa kawai, kamar yadda muka rahoto.
Ya ce babban burinsa shi ne samar wa matasan jihar ayyukan yi da kuma inganta kayayyakin more rayuwa domin amfanin dukkanin al'umma.

Source: Facebook
Yanayin tsaro da noma a jihar Taraba
Gwamnan Kefas ya kuma ce an samu ci gaba sosai a fannin tsaron jihar, inda mutane ke iya zirga-zirga cikin kwanciyar hankali a yanzu.
Ya ce ko da yake ba za a rasa kalubale ba, amma zaman lafiya ya dawo jihar fiye da yadda aka same ta baya, in ji rahoton The Nation.
Gwamnan ya bayyana cewa jihar Taraba tana da albarkatun kasa da filayen noma masu yawa wadanda za su iya taimaka wa tattalin arzikin kasa.
Ya ce gwamnatinsa ta shigo da taraktoci domin inganta noman zamani kuma nan gaba za su gina masana'antun sarrafa amfanin gona a jihar.
Tinubu ya yabi kokarin Gwamna Kefas
A wani labari, mun ruwaito cewa, Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnonin da ke karkashin inuwar jam’iyyar APC su ne jagororin jam’iyyar a jihohinsu.

Kara karanta wannan
Rashin tsaro: Shugaba Tinubu ya kwantar da hankalin 'yan Najeriya kan 'yan bindiga
Tinubu ya bayyana hakan ne a yayin taron karbar Gwamna Agbu Kefas zuwa cikin jam’iyyar APC wanda aka gudanar a birnin Jalingo.
Shugaban kasar, ta bakin Kashim Shettima ya bayyana aniyarsa ta ba Gwamna Kefas da majalisar zartarwarsa cikakken goyon baya domin kawo cigaba a Taraba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

