'Yan Daba Sun Yi wa 'Yan APC Jina Jina a Wajen Taro, Wasu Sun Rasu
- Taron zaɓen unguwanni na jam’iyyar APC da ke gudana a jihar Ondo ya rikide zuwa tashin hankali, inda mutane biyu suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata
- Lamarin ya faru ne kasa da awa 24 bayan wasu ’yan daba sun kai hari sakatariyar APC da ke Akure, inda suka tarwatsa taron masu ruwa da tsaki da ake tsaka da yi
- Rahotannin da Legit Hausa ta samu nuna nuna cewa a yayin harin, an kai wa shugabanni farmaki da sauran jagororin jam’iyyar a jihar, tare da jikkata wasu mambobi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Ondo - Rahotanni sun nuna cewa ba a iya gudanar da taro a wasu unguwannin karamar hukumar Idanre ba a Ondo bayan wasu 'yan daba sun kai hari ga mambobin jam’iyyar.
An kuma ruwaito cewa an banka wa wasu motoci wuta a lokacin rikicin, sai dai har zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, ba a san musabbabin rikicin ba.

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa daya daga cikin waɗanda abin ya shafa shi ne ɗan’uwan shugaban APC na jihar, Raphael Adetimehin, wanda aka kai wa mummunan hari a unguwarsa da ke Idanre.
An kai farmaki kan 'yan APC a Ondo
Rahotanni sun nuna cewa shugaban jam'iyyar APC na jihar Ondo ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce ’yan daban ne suka kai wa ɗan’uwansa hari.
Ya ce an harbi ɗan’uwansa tare da sara shi da adda, sannan maharan sun ƙone motarsa:
“An kai wa ɗan’uwana hari; waɗanda suka kai harin sun yi zaton ni ne saboda mun yi kama sosai.
“Bayan sun harbe shi kuma sun caka masa wuƙa, sun bar shi bayan sun yi zaton ya mutu.”
Bayanin 'yan sandan jihar Ondo
Sanarwar kakakin ’yan sandan Jihar Ondo, DSP Abayomi Jimoh, ta tabbatar da cewa mutane biyu sun mutu yayin da wasu uku suka jikkata a Idanre.

Kara karanta wannan
'Yan daba sun fasa ofishin APC, sun raunata shugaban jam'iyya, tsohon dan majalisa
Sanarwar ta ce harin ya faru da misalin ƙarfe 11:00 na safe:
“Bayan haka, kwamishinan ’yan sanda tare da kwamandan kukumar NSCDC na jihar, CC Oluyemi Ibiloye, sun jagoranci tawagar jami’an tsaro zuwa wurin da lamarin ya faru.
“Shigarsu cikin gaggawa ya tabbatar da dawo da zaman lafiya da doka a yankin da abin ya shafa,”
Jimoh ya wallafa a X cewa:
“Mutane uku sun samu raunuka daban-daban kuma suna karɓar magani a asibiti, yayin da wasu biyu aka tabbatar da mutuwarsu a asibitin.

Source: Original
Dattawan jam'iyyar APC sun yi Allah-wadai
Dattawan jam’iyyar APC a Jihar Ondo sun yi Allah-wadai da harin da aka kai. A yayin harin Akure, an ruwaito cewa dattawa 15 sun jikkata kuma suna karɓar magani a asibiti.
Sun ce:
“Ba a gina APC da ta’addanci ba,"
Shugaban APC ya ziyarci Aminu Daurawa
A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda ya ziyarci Sheikh Aminu Daurawa a Kano.
Rahotanni sun nuna cewa Nentawe Yilwatda ya gana da Sheikh Daurawa ne a ofishin hukumar Hisbah da Malamin ke jagoranta.
Shugaban jam'iyyar ya yi alkawarin daukar nauyin wani adadi na dalibai mata masu hazaka domin su yi karatu a matakin jami'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

