Ramadan: Gwamnan Kebbi Ya Ji Tausayin Ma'aikata, Ya Kawo Musu Sauki Saboda Azumi
- Ma'aikata za su samu sauki a jihar Kebbi bayan Gwamna Nasir Idris ya waiwayesu saboda zuwan lokacin watan azumin Ramadan mai albarka
- Gwamna Nasir Idris ya amince da rage lokacin da ma'aikata za su rika a wuraren ayyukansu domin su samu saukin azumi
- A cikin sanarwar da aka fitar, an bayyana cewa za a koma tsarin da ake amfani da shi a baya da zarar an kammala azumi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Gwamnatin jihar Kebbi ta amince da rage sa’o’in aiki ga ma’aikatan gwamnati domin sauƙaƙa musu a lokacin azumin watan Ramadan.
Wannan umarni ya biyo bayan sanarwar fara azumin watan Ramadan da Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci (NSCIA) ta yi.

Source: Facebook
Jaridar The Punch an sanar da rage lokacin ne a cikin wata sanarwa da babbar sakatariya a ma’aikatar samar da aiki, fansho, da horarwa, Hafsat Tune, ta fitar ranar Laraba, 18 ga watan Fabrairun 2026 a Birnin Kebbi.

Kara karanta wannan
Ramadan: Gwamna Zulum ya ware Musulmi da Kiristoci 300,000, ya raba tallafin azumi
Gwamna Nasir ya rage lokacin tashi aiki
Hafsat Tune ta bayyana cewa gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya amince da rage sa’o’i biyu daga jadawalin tashi a wurin aiki.
“Gwamnan jihar Kebbi, Comrade Dr. Nasir Idris, ya amince da rage sa’o’in aiki da sa’o’i biyu a lokacin azumin Ramadan na wannan shekarar."
- Hafsat Tune
Sabon jadawalin lokacin aiki
A cewarta, sabon lokacin aikin zai fara ne daga karfe 8:00 na safe zuwa 2:00 na rana, daga ranar Litinin zuwa Alhamis. A ranar Juma’a kuwa, za a tashi da karfe 12:00 na rana, jaridar Vanguard ta dauko labarin.
“Sakamakon wannan ci gaba, ana bukatar ma’aikata a faɗin jihar su kasance a wuraren ayyukansu har zuwa karfe 2:00 na rana daga Litinin zuwa Alhamis, sannan ƙarfe 12:00 na rana a ranar Juma’a."
- Hafsat Tune
Ta kara da cewa za a koma tsohon lokacin aiki na yau da kullum da zaran an kammala watan azumi.

Kara karanta wannan
Ana jiran sanarwar Sarkin Musulmi, gwamnatin Kano ta ba da shawarwari 4 kan azumin Ramadan

Source: Facebook
Wasu jihohin Arewa na rage lokacin aiki
Wannan mataki ya yi daidai da tsohuwar al’ada a wasu jihohin Arewacin Najeriya inda akasari Musulmi ne, inda gwamnatoci kan rage lokacin aiki a watan Ramadan domin sauƙaƙa wa ma’aikata raɗaɗin azumi.
Ramadan dai ɗaya ne daga cikin rukunai biyar na Musulunci, wanda Musulmi a duk faɗin duniya ke gudanar da azumi da komawa ga Allah.
Gwamnan Bauchi ya rage lokacin aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya saukakawa ma'aikatan jiharsa yayin da aka fara azumin watan Ramadan.
Mai girma Bala Mohammed ya amince da rage lokutan tashi daga aiki ga ma'aikatan gwamnatin jihar a duk tsawon lokacin azumin Ramadan na bana.
Hakazalika, an buƙaci ma'aikata da su yi amfani da lokacin mai tsarki wajen gudanar da addu'o'in neman ci gaba, zaman lafiya, da haɗin kai a jihar Bauchi da kuma Najeriya baki ɗaya.
Asali: Legit.ng