Ta Faru Ta Kare: Shugaba Tinubu Ya Rattaba Hannu kan Sabuwar Dokar Zabe
- Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe ta shekarar 2026 a fadar gwamnati dake Abuja a yau Laraba
- Tinubu ya bayyana cewa akwai bukatar yin amfani da tsarin hannu wajen tura sakamakon zabe domin kaucewa matsalar yanar gizo
- Shugaban ya sanya wa kudirin hannu ne bayan an kai runa rana a majalisar dattawa, musamman turjiyar 'yan hamayya a majalisa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rattaba hannu kan kudurin dokar zaɓe ta shekarar 2026 (wacce aka sabunta daga dokar ta 2022) domin ta zama doka a hukumance.
Wannan mataki ya biyo bayan amincewa da kudirin dokar da Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta yi a ranar Talata, bayan kwashe watanni ana tattaunawa da muhawara a kai.

Source: Twitter
Tinubu ya amince da dokar zabe ta 2026
Ana kallon sabuwar dokar, wacce ta soke dokar zaɓe ta shekarar 2022, a matsayin wani yunƙuri na ƙara gyara tsarin zaɓen ƙasar gabanin babban zaɓen 2027 mai zuwa, in ji rahoton Channels TV.
Shugaban ya sanya wa dokar hannu ne a fadar gwamnati a gaban manyan jami’an gwamnati, ciki har da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila.
Tinubu ya bayyana cewa ginshiƙin damokaraɗiyya shi ne samun tattaunawa mai ma'ana wadda za ta kai ga ci gaban ƙasa da ƙarfafa amincewar ƴan Najeriya ga tsarin zaɓe.
Dangane da takaddamar da ake yi kan tura sakamakon zaɓe ta na'ura, shugaban ya nuna bukatar yin taka-tsantsan duba da yanayin ƙarfin yanar gizo na ƙasar nan.
Tinubu ya yi tsokaci kan tura sakamakon zabe
Shugaba Bola Tinubu ya ce:
"A gaskiya, idan aka zo tura sakamakon ƙarshe, ba da kwamfuta ya kamata a tura ba; mutane ya kamata a ce sun zama waɗanda za su sanar da sakamakon.
"Dole ne mu guje wa matsalolin na'ura da kutse a wannan zamani da muke ciki. Kamar yadda mutum yake fita da kansa ya jefa ƙuri'a a takarda, haka ma za a kirga su da hannu a sanar kowa ya ji."
A cewar shugaban, babban abin da ake nema shi ne daidaita lissafi a cikin fom ɗin EC8A, kuma tura wannan sakamakon da aka rubuta da hannu shi ne abin da ya fi dacewa, in ji rahton Punch.

Source: Twitter
Dambarwar da aka yi a majalisa
Wannan dokar ta haifar da muhawara mai zafi a makon da ya gabata, tare da jawo rarrabuwar kai tsakanin ƴan majalisa kan hanyar da za a bi wajen tura sakamakon zabe gabanin babban zaɓen 2027.
A ranar Talata, Majalisar Dattawa ta yi zama cikin yanayi na hayaniya lokacin da Sanata Enyinnaya Abaribe ya buƙaci a raba majalisa domin jefa ƙuri'a kan sashe na 60 na dokar.
Sanata Godswill Akpabio ya yi iƙirarin cewa an riga an janye buƙatar Abaribe, amma ƴan hamayya a majalisar suka ƙi amincewa da maganarsa, kamar yadda muka ruwaito.
Duk da waɗannan rigingimu, an amince da dokar wadda yanzu ta zama jagora ga yadda hukumar INEC za ta gudanar da zaɓuka masu zuwa a ƙasar nan.
An gyara dokar zabe saboda azumi
A wani labari, mun ruwaito cewa, Majalisar dattawa ta saurari koken yan Najeriya kan sanya ranakun babban zaben 2027 a watan azumin Ramadan na badi.
A zaman da ta yi yau Talata, Majalisar ta gyara sashen da zai ba hukumar INEC damar canza ranakun da ta sanar idan da bukatar hakan.
Haka zalika yunkurin Sanata Enyinna Abaribe na gyara tanadin dokar tura sakamakon zabe ta intanet bai yi nasara ba bayan kada kuri'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


