Ana Murnar Fara Azumi, Mutane 37 Sun Mutu bayan Gama Sallar Asubah a Filato
- Wasu masu aikin hakar ma'adanai aun gamu da ajalinsu bayan sun kammala sallar Asubahi a yankin karamar hukumar Wase ta jihar Filato
- Rahotanni sun nuna cewa ma'aikatan sun shaki iskar gas da ake zargin tana dauke da guba a ramin da suke aiki a wanyij kauyen Zurak
- Duk da babu wata sanarwa a hukumance, majiyoyi sun ce sojoji sun kewaye gurin domin dakile yaduwar iskar ta gas
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Ana fargabar akalla mutane 37 sun mutu sakamakon shakar iskar gas mai guba a wani raminn haƙar ma’adanai da ke kauyen Zurak, ƙaramar hukumar Wase ta jihar Filato.
Shugaban Matasa na Wase, Shafi Sambo, ya ce ya samu kiran waya da safiyar yau Laraba, inda aka sanar da shi game da iftila’in saboda matsayinsa na jagora a yankin.

Source: Original
Akalla mutane 37 sun mutu a rami a Filato
A rahoton da tashar Channels tv ta dauko, Sambo ya bayyana cewa a labarin da ya samu, mutane 37 ne suka rasa rayukansu nan take, wasu da dama na kwance a asibiti.
“Abin ya faru ne a wurin haƙar ma’adanai a Company Zurak. Mun samu bayani cewa ma’aikatan sun haka rami mai zurfi, sai iskar gas ta mamaye su, ta kashe mutum 37 nan take,” in ji Sambo.
Ya ce an ceto wasu daga cikin ma’aikatan da ransu, inda aka garzaya da su asibitoci mafi kusa domin ba su kulawar gaggawa, amma har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a tantance ainihin adadin waɗanda suka tsira ba.
Sambo ya bayyana cewa matasan na haƙar madanai ne a madadin wani kamfani da ake zargin mallakin ’yan ƙasar China ne, wanda ke aiki a yankin.
Dakarun sojoji sun kai dauki wurin

Kara karanta wannan
'Yan daba sun fasa ofishin APC, sun raunata shugaban jam'iyya, tsohon dan majalisa
Ya kuma ce rundunar sojoji ta isa wurin tare da killace yankin domin hana shiga da kuma dakile yaduwar matsalar, amma har yanzu babu wata sanarwa a hukumance.
Wani dan hakar ma'adanai a yankin, Safiyanu Haruna, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sama da mutum 20 da suka samu raunuka an kai su asibiti a garin Wase domin jinya.
Yadda mutanen suka mutu bayan Asubah
A cewarsa, lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 6:30 na safe, bayan ma’aikatan sun yi sallar asuba sannan suka koma wurin aiki, inda suka faɗa tarkon hayakin gas.
“Iskar carbon monoxide ce ta fito ta kashe su. Da misalin 5:30 na safe duk suna raye domin sun bar wurin aiki sun tafi sallah. Da suka dawo ne aka same su a wannan hali,” in ji shi.

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa wadanda lamarin ya shafa ba su samu wani ceto a kan lokaci ba domin wasu ma’aikatan da ake sa ran su je wurin da safe ba su isa ba a lokacin da lamarin ya faru.
A cewarsa, an tabbatar da mutuwar mutum 37 yayin da sama da 20 ke karɓar magani a asibiti, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Yan bindiga sun farmaki masu hakar ma'adanai
A wani rahoton, kun ji cewa yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan wani wurin hakar ma'adanai a jihar Filato.
'Yan bindigan sun kai harin ne a wani wurin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Capitex, yankin Kuru da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.
Wata babbar majiya daga jami’an sojoji ta ce jami’an tsaro sun gano gawarwaki da harsasai a wurin yayin da suke gudanar da bincike.
Asali: Legit.ng

